Labarai

ASUU ta ƙara tsawaita yajin aikin da take yi

ASUU ta ƙara tsawaita yajin aikin da take yi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Malaman Jami’o'i a Nijeriya, ASUU ta yanke shawarar tsawaita yajin aikin da take gudanarwa da ƙarin watanni 6. Jaridar Punch ta rawaito cewa matakin ya zo ne bayan wata zazzafar tattaunawa da aka yi a ranar Litinin game da yadda za a cimma matsaya tsakanin ƙungiyar da kuma gwamnati. An ɗauki matakin ci gaba da yajin aikin bayan ganawar kwamitin zartarwa a hedikwatar ASUU da ke Jami’ar Abuja, babban birnin Nijeriya. Ƙungiyar ASUU dai ta shafe watanni tana gudanar da yajin aikin da ya tilasta wa ɗaliban jami’o'in gwamnati zama a gida. ASUU…
Read More
Sanata Adamu ya naɗa Bala Ibrahim Daraktan Yaɗa Labarai na APC

Sanata Adamu ya naɗa Bala Ibrahim Daraktan Yaɗa Labarai na APC

Daga BASHIR ISAH Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya naɗa ɗan jarida a matsayin Daraktan Yaɗa Labarai na Jam'iyyar. Naɗin Malam Yusuf Bala Ibrahim a matsayin Daraktan Yaɗa Labarai na APC na ƙunshe ne cikin wasiƙar da babban ofishin APC na ƙasa ya fitar mai ɗauke da kwanan wata 1 ga Satumba, 2022 da kuma sa hannun Babban Mai Bai wa Shugaban APC Shawara kan sabbin kafafen yaɗa labarai, Ambasada Samuel Jimba. Wasiƙar ta nuna naɗin Ibrahim ya soma aiki ne nan take. Yusuf Ibrahim ɗan asalin Jihar Kano ne, wanda ya yi karatu a gida da…
Read More
Gwamnatinmu za ta cigaba da bada agaji ga waɗanda ambaliyar ruwa ya shafa – Buhari

Gwamnatinmu za ta cigaba da bada agaji ga waɗanda ambaliyar ruwa ya shafa – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya miqa saƙon jaje ga mutane sama da 500,000 da ambaliyar ruwa ya shafa a faɗin ƙasar. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban ya alƙawarta cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da bayar da taimakon gaggawa ga waɗanda iftila'in ta shafa. Ya kuma yi kira ga ɗaiɗaikun masu hannu da shuni da ƙungiyoyi da su taimaka wa dubban mutanen da lamarin ya shafa. Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya tare da haɗin gwiwar gwamnatocin jihohi, za su yi…
Read More
Ambaliyar ruwa ya ruguje gadar Katarko a Jihar Yobe

Ambaliyar ruwa ya ruguje gadar Katarko a Jihar Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ranar Litinin ya jawo mummunan ambaliyar ruwan da ya ruguje Gadar-Katarko a Qaramar Hukumar Gujba a Jihar Yobe, wanda ta yanke hanyar Damaturu/Buni Yadi/ Biu; wadda ta haɗa jihar da jihohin Borno da Gombe, mai tazarar kilomita 22 daga Damaturu, babban birnin jihar Yobe. Wanda zabtarewar gadar ya kawo cikas ga Ma’aikatan Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) a ƙoƙarin kai wa jama'ar da ambaliyar ruwan ta shafa a ƙauyen Mutai a yankin, wanda suka gamu da mummunan ambaliyar ruwan da ya shafe garin baki…
Read More
Makarantar Halima Usman Zugarawa ta yaye ɗalibai 32

Makarantar Halima Usman Zugarawa ta yaye ɗalibai 32

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Makarantar Islamiyya da karatun zamani da ake kira Halima Usman Memorial da ke ƙarƙashin shugabancin Marafan Dukajin Gaya Hakimin Wudil, Alhaji Abba wato Alhaji Yusuf Wakilin dukiya ya gina a garin Zugarawa da ke Ƙaramar Hukumar Wudil a Jihar Kano ta yi bikin yaye ɗalibai 32 a karo na farko a walimar bikin da aka yi a harabar makarantar da ke Zugarawa a ranar Lahadi da ta gabata ƙarƙashin jagorancin Dukajin Gaya Hakimin Wudil Alhaji Abba Muhammad. A jawabinsa, Dukajin Gaya Hakimin Wudil Alhaji Abba Muhammad ya bayyana farin cikinsa da wannan rana mai muhinmanci…
Read More
Mawaƙan Annabi ba ‘yan bambaɗancin siyasa ba ne – Sharu Siddi Bolari

Mawaƙan Annabi ba ‘yan bambaɗancin siyasa ba ne – Sharu Siddi Bolari

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Shugaban Ƙungiyar Mawaƙan Annabi na Ƙasa (Ushaƙun Nabiyi Rasulil A'azam Nigeria), Sharu Auwal Siddi Bolari, ya ce mawaƙan bege masu ƙasidun yabon Manzon Allah ba 'yan bambaɗancin siyasa ba ne. Sharu Auwal Siddi Bolari, ya bayyana hakan ne a lokacin zantawarsa da wakilinmu a Gombe, inda ya ce bayan taron ƙungiyar na ƙasa da suka yi a Abuja sun yi irin sa a Kano sannan a makon da ya gabata sun yi wani a Maiduguri fadar Jihar Borno, inda suka ja hankalin matasa mawaqan Manzon Allah da cewa su kiyaye harshe kar kuma su…
Read More
Bunƙasa ilimi: Zulum ya shigar da marayu 7,000 makaranta a Monguno a Jihar Borno

Bunƙasa ilimi: Zulum ya shigar da marayu 7,000 makaranta a Monguno a Jihar Borno

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Maiduguri A ci gaba da ƙoƙarin sake farfaɗo da harkokin ilimi tare da ƙarfafa gwiwar jama'a wajen sake tsugunnar da yan gudun hijira a yankunan da rikicin Boko Haram ya tagayyra tare da samar da zaman lafiya ga al’umma, Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Litinin ya ziyarci Kasuwar Cross-Kauwa wadda a da sansanin ce ga mayaqan Boko Haram a ƙaramar hukumar Kukawa a Arewacin jihar Borno. Garin Cross Kauwa mai tazarar kilomita 200 daga birnin Maiduguri, a arrwacin jihar kuma ya na kan gaɓar Tafkin Chadi. Bugu da ƙari, Gwamna Zulum ya shigar…
Read More
Gwamnatin Nijeriya za ta ciwo bashin Naira tiriliyan 11 domin ayyukan kasafin 2023 – Zainab

Gwamnatin Nijeriya za ta ciwo bashin Naira tiriliyan 11 domin ayyukan kasafin 2023 – Zainab

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministar Harkokin Kuɗaɗe ta Nijeriya, Zainab Ahmed ta bayyana cewa babu tsimi ba dabara, Gwamnatin Tarayya za ta ciwo wani sabon bashi na Naira tiriliyan 11 cur domin antaya kuɗaɗen cikin kasafin kuɗin 2023. Ba a nan lamarin ya tsaya ba, Zainab ta ce kuma Gwamnatin Tarayya za ta sayar da wasu kadarorin gwamnati duk don a samu kuɗaɗen da za a yi ayyukan kasafin 2023 da su. “Idan Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da biyan tallafin fetur daga farko har zuwa ƙarshen 2023, to za a samu giɓin Naira tiriliyan 12.42 a cikin…
Read More
Hukumar NDE ta horas da mata 130 kan sarrafa tsirrai da ‘ya’yan itatuwa a Bauchi

Hukumar NDE ta horas da mata 130 kan sarrafa tsirrai da ‘ya’yan itatuwa a Bauchi

Daga MU'AZU HARDAWA a Bauchi Hukumar Samar da Aikin Yi ta Ƙasa (National Directorate of Employment), ta horas da mata 130 ilimin sarrafa tsirrai da 'ya'yan itatuwa yadda za su yi tasiri wajen inganta rayuwa da lafiyar bil Adama. Malam Aliyu Lawal Yaya, Daraktan hukumar ta NDE a Jihar Bauchi, shine ya bayyana haka lokacin taron yaye ɗaliban wanda ya gudana a harabar ofishin NDE da ke Bauchi. Ya ce an karantar da ɗaliban da suka ƙunshi 'yan mata da matan aure yadda za su gyara tsirrai da 'ya'yan itatuwa kamar namijin goro da ciyayi da su habbatus sauda da…
Read More
Ambaliyar ruwa: Gwamnatin Kano za ta rushe gine-gine da aka yi kan hanyoyin ruwa – Kwamishina

Ambaliyar ruwa: Gwamnatin Kano za ta rushe gine-gine da aka yi kan hanyoyin ruwa – Kwamishina

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin Kano ta ce ta kafa wani kwamiti da zai gaggauta yin nazari da magance yawan ambaliyar ruwa da mamakon ruwan sama ke haifar wa a jihar. Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya fitar a ranar Litinin a Kano. Ya ce gwamnati ta damu da irin ambaliyar ruwan da ke faruwa a jihar, musamman a cikin birni. Ya ce kwamitin zai ɗauki nauyin duba titina, kwatoci da kwalbati da su ka lalace kuma su ke toshe magudnan ruwa domin a gyara, ko kuma a gina…
Read More