Labarai

An samu ƙaruwar satar ɗanyen mai cikin wata biyar a Nijeriya – NNPC

An samu ƙaruwar satar ɗanyen mai cikin wata biyar a Nijeriya – NNPC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Kamfanin Mai na Nijeriya NNPC, Malam Mele Kyari ya bayyana cewa an samu ƙaruwar satar ɗanyen mai a Nijeriya cikin watanni biyar, kamar yadda ya faɗa ranar Talata a Abuja, inda ya ce jami'an tsaron ƙasar sun gano aƙalla wurare 295 da aka fasa bututun don satar man a cikin tafiyar kilomita 200. Ya sanar da hakan ne yayin wani taron manema labarai a Fadar Shugaban ƙasar. A cewar Mele Kyari an kama mutane 122 da hannu a satar man tsakanin watan Afrilun bana da wannan watan na Agusta da ake ciki kaɗai.…
Read More
NIMET ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a jihohin Arewa biyar

NIMET ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a jihohin Arewa biyar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa, NIMET ta yi hasashen fuskantar ƙaƙƙarfan ruwan sama na tsawon kwanaki 4 babu ƙaƙƙautawa a wasu jihohin arewacin ƙasar 5, da kuma birnin Abuja, fadar gwamnatin Nijeriya. Cikin rahoton hasashen yanayin da hukumar ta NIMET ta fitar, ta ce jihohin da za su fuskanci wannan ruwa na tsawon kwanaki 4 ba tare da ƙaƙƙautawa ba sun haɗa da Kaduna, Neja, Bauchi, Filato da kuma Jihar Nasarawa, baya ga birnin tarayyar ƙasar. Rahoton na NIMET ya kuma yi hasashen fuskantar madaidaicin ruwan sama a wasu jihohin Nijeriya daga Kudanci…
Read More
RANAR HAUSA 2022: Kare martabar kyawawan al’adun Hausawa

RANAR HAUSA 2022: Kare martabar kyawawan al’adun Hausawa

Daga ABUBAKAR YAKUBU ABDULLAHI "Al'adun da ku ke ƙyama, yanzu sun zama abin kwalliyar ku, saura ku karɓi addinin mu!" Waɗannan wasu kalamai ne na izgili da wani wanda ba musulmi ba ya rubuta a ƙasan jikin wani hoton wasu ma'aurata sabbin aure, wato ango da amarya, wanda aka ɗauka lokacin wani shagalin bikin aure. Yanayin hoton ya nuna angon cikin shigar ƙananan kaya ya sa kwat da wando da maɗaurin wuya, yayin da ita kuma amaryar ta sanya farar rigar leshi da siffar ɗinkin amaren Turawa, kai ka ce dai bukin na waɗanda ba musulmi ba ne. Ba su…
Read More
Ginin bene ya rufta a Kano

Ginin bene ya rufta a Kano

Wani ginin bene da ke hanyar Beirut daura da hanyar Ibrahim Taiwo a birni Kano, ya rufta. Wani mai amfani da shafin Tiwita, Devdeiz, ya wallafa a shafinsa ranar Talata cewa, ginin da ya rufta ɗin ana kan aikin gina shi ne. Ya zuwa haɗa wannan rahoton babu wani ƙarin bayani a hukumance dangane da iftila'in. Wannan na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya da ruftawar wani gini a yankin Kubwa a Abuja. A 'yan lokutan baya-bayan an fuskanci ruftawar gine-gine a sassan Nijeriya, musamman a Jihar Legas, lamarin da masana ke danganta shi da rashin amfani da kayan gini…
Read More
2023: Adamu ya nemi dafawar Ubangiji kan nasarar Tinubu

2023: Adamu ya nemi dafawar Ubangiji kan nasarar Tinubu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya nemi dafawar Ubangiji don ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyarsu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kai bantensa a babban zaɓe mai zuwa. Adamu ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci shugabancin jam'iyyar (NWC) zuwa ofishin kamfe ɗin Tinubu/Shettima da ke Abuja a farkon wannan makon. Sa'ailin da yake jawabi yayin ziyarar, Shugaban APCn ya yaba da tsare-tsare da shirye-shiryen da Tinubu ke yi don gudanar da yaƙin neman zaɓensa. Adamu ya faɗa wa Tinubu, “Duba da ƙoƙarin da ka yi, hakan wata alama ce mai nuni…
Read More
Barci ya kwashe wasu matuƙan jirgin sama a sararin samaniya

Barci ya kwashe wasu matuƙan jirgin sama a sararin samaniya

Barci ya ɗauke wasu matukan jirgin sama biyu mallakin ƙasar Habasha a yayin da ya ke tsaka da balaguro a sararin samaniya. Jirgin ƙirar Boeing 737 mai ɗauke da fasinjoji 154, ya tashi ne daga birnin Khartoum na Ƙasar Sudan zuwa birnin Addis Ababa na Habasha a farkon makon nan. Masu tuƙinsu na sararin samaniya da nisan kafa 37,000 tsakaninsu da qasa, sai barci ya ɗauke su gabanin isowarsu filin jirgin saman Addis Ababa inda za su sauka. Masu kula da tashi da kuma saukar jiragen sama a filin, sun yi ta ƙoƙarin ankarar da su cewa suna daf da…
Read More
Atiku ya tallafa wa ‘yan Kasuwar Kwari da miliyan N50

Atiku ya tallafa wa ‘yan Kasuwar Kwari da miliyan N50

…yayin da Ibrahim Sekarau ya sauya sheƙa zuwa PDP Daga BABANGIDA S GORA KANO. Ɗantakarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya jajanta wa 'yan kasuwar Kantin Kwari bisa ɓarnar da ruwan sama ya yi musu, tare da ba su tallafin naira milyan hamsin dan rage raɗaɗin asarar da suka yi. Wannan na zuwa ne a lokacin da Wazirin Adamawan yake karɓar tsohon sanatan Kano ta Arewa, Malam Ibrahim shekarau daga Jam'iyyar NNPP ranar Litinin ɗin makon nan a gidansa da ke Mundubawa, Jihar kano. Atiku ya ce, abin a tausaya ne iftila'in da sami 'yan kasuwar na…
Read More
Garkuwa: Bayan mako uku ’yan sandan Zamfara sun ceto wasu mata

Garkuwa: Bayan mako uku ’yan sandan Zamfara sun ceto wasu mata

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta ceto wasu mata biyu da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Bungudu da ke jihar. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan SP Muhammad Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Litinin. “A ranar 20 ga watan Agusta, 2022, jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara yayin da suke sintiri tare da Nya Mango a ƙaramar hukumar Bungudu, sun ɗauki matakin ceto wasu mata biyu da aka yi garkuwa da su ba tare da wani…
Read More
Yadda sabon Daraktan Hukumar Kula da Hanyoyi na Ƙasa ke canja fasalin hukumar – Mista Kalu Emetu

Yadda sabon Daraktan Hukumar Kula da Hanyoyi na Ƙasa ke canja fasalin hukumar – Mista Kalu Emetu

Daga JOHN D. WADA a Lafiya An bayyana sabon Daraktan Hukumar Kula da Hanyoyi na Ƙasa wato Road Traffic Services (DRTS) a turance wato Dokta Abdul-lateef Bello a matsayin ƙwararren shugaba da a cikin watanni ƙalilan da ya yi a matsayin daraktan hukumar ya cimma nasarori da dama dake cigaba da kawo sauyi mai ma’ana da kuma canja fasalin hukumar a yanzu. Shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar, Kulu Emetu ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da wakilin mu a ofishinsa dake babbar sakatariyar hukumar a Abuja ranar Laraba 24 ga watan Agustan shekarar 2022 da…
Read More
Atiku ya taya Sarkin Musulmi murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Atiku ya taya Sarkin Musulmi murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Ɗan takarar Shugabancin Nijeriya na Jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya aike da saƙon taya murna ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar bisa zagayowar ranar haihuwarsa. Mai Alfarma Sarkin na Musulmi wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci a Nijeriya, ya cika shekaru 66 a duniya ranar 24 ga watan Agustan 2022. A saƙon taya Sarkin Musulmin murnar ranar haihuwarsa a shafin sa na Tiwita, Wazirin Adamawa ya ce a madadinsa da iyali, yana taya murna gare shi sannan yana addu'ar Allah Ya ƙara masa lafiya…
Read More