Labarai

Gwamna Ganduje zai samar da ƙarin jami’o’i guda biyu a Kano

Gwamna Ganduje zai samar da ƙarin jami’o’i guda biyu a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin Jiihar Kano ta yi alƙawarin sake samar da jami’o’i guda 2 a Kano domin ƙara bada damar inganta ilimin matasa a jihar. Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi yayin buɗe taron makon matasa, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin duba a kan matsalolin matasa da kuma lalubo hanyoyin da za a magance su. Taron wanda ya gudanar a rufaffen ɗakin taro na filin wasa na Sani Abacha dake Ƙofar Mata a ranar Laraba da ta gabata. A cewar Gwamna Ganduje, tuni an tura sunayen Kwalejin…
Read More
Zamfara: Makarantun sakandare 75 ne a rufe saboda matsalar tsaro

Zamfara: Makarantun sakandare 75 ne a rufe saboda matsalar tsaro

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa har yanzu akwai makarantun sakandare 75 da suke a rufe sakamakon ayyukan 'yan ta'adda. Hakan ya fito ne ta bakin babban sakataren ma’aikatar ilimi ta jiha Alhaji Kabiru Attahiru cikin saƙon fatan alheri a wani taro na kwanaki biyu a matakin jiha na gidauniyar samar da manufofin ƙasa kan jinsi a fannin ilimi NPGE A jihar Zamfara wanda hukumar kula da ilimin bai ɗaya ta ƙasa da haɗin gwiwar hukumar UNICEF suka shirya a cibiyar horas da malamai ta Zamfara Gusau ranar Laraba. A cewarsa, gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin…
Read More
Sakkwatawa na kokawa kan ramukan titina a wasu manyan hanyoyin birnin

Sakkwatawa na kokawa kan ramukan titina a wasu manyan hanyoyin birnin

…Tuni muka soma magance matsalar, cewar Hukumar Tsara Birnin Sakkwato Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Wasu masu amfani da ababen hawa a Jihar Sakkwato sun yi kira ga mahukunta da su duba hanyoyin gyara titina dama shatale-shatalen dake ƙwaryar birnin Sakkwaton, lamarin da suka ce rashin gyaran na iya kai ga rasa rayuka da ma dukiyoyin al’umma. Kiran nasu dai na zuwa ne a daidai lokacin da titinan dake ƙwaryar birnin jihar ke fama da matsalar fashewar, wanda masu amfani da ababen hawan musamman masu sana’ar kabu-kabu ke cewa hakan na iya kawo tsaiko ga tattalin arzikinsu. Titinan dake fama…
Read More
Matashi ya kashe kishiyar babarsa, ya karya babansa a Katsina

Matashi ya kashe kishiyar babarsa, ya karya babansa a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wani matashi mai suna Najib Shehu Umar, ɗalibi a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ta ke Dutsinma (FUDMA) ya kashe kishiyar mahaifiyar shi daga bisani ya kuma karya kafar mahaifinsa a Katsina. Kamar yadda Manhaja ta samu, Najib ya sha furta cewar sai ya kashe Hajiya Hasiya Galadima wadda ita ce kishiyar mahaifiyar ta sa. Yana zargin ita ce tai sanadiyyar raba auren mahaifiyarsa da mahaifinsa. Najib ya shiga ɗakin girki, inda ya ɗauko tavarya ya shigo inda marigayiyar ke zaune tare da 'yarta da kuma wasu mutane daban bai yi wata-wata ba ya kulle ɗakin.…
Read More
Gwamnatin Zamfara za ta kammala dukkan ayyukan da ta soma kafin ƙarshen wa’adinta – Kwamishinan Ayyuka

Gwamnatin Zamfara za ta kammala dukkan ayyukan da ta soma kafin ƙarshen wa’adinta – Kwamishinan Ayyuka

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Kwamishinan ayyuka na Jihar Zamfara Hon. Rabiu Garba ya yi fatan cewa dukkan abubuwa da aka cimma a taron ƙasa na ayyuka da aka gudanar a Kano za a aiwatar da su yadda zai amfani jama'ar ƙasar nan. Ya ce a ɓangaren gudanar da ayyuka Gwamnatin Jihar Zamfara tana gudanar da aikin gina filin jirgin sama da samar da hanyoyi da zai kai ga filin jirgin wanda nan gaba kaɗan za a kammala ya zama jirgi na iya tashi kai tsaye daga Zamfara zuwa ƙo'ina a faɗin duniya. Ya yi nuni da cewa  duk da…
Read More
Za mu gina Nijeriya kamar yadda muka gina Lagos da Borno – Shettima

Za mu gina Nijeriya kamar yadda muka gina Lagos da Borno – Shettima

Daga IBRAHEEM HAMZA MUHAMMAD Sanata Kashim Shettima ya jaddada cewa, Najeriya za ta mori romon mulkin dimukraɗiyya idan aka zavi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin Shugaban Ƙasa a zaven da ke gabatowa. A takardar sanarwa da Kakakin Kwamitin APC mai neman a zaɓi Bola Ahmed Tinubu da Sanata Kashim Shettima a matsayin Shugaba da Mataimaki, Mista Bayo Onanuga, ya fitar, ta ce, sanatan ya furta haka ne a ranar Litinin a Legas yayin da ya wakilci Tinubu a taron shekara-shekara na Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA). Inda ya ce, aikin gani-da-ido da Tinubu da Shettima suka…
Read More
Gwamnatin Bauchi za ta kafa kotuna don ƙwato bashin da aka ba manoman alkama

Gwamnatin Bauchi za ta kafa kotuna don ƙwato bashin da aka ba manoman alkama

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Jihar Bauchi za ta kafa wasu kotuna guda uku na musamman, ɗaya a kowace mazaɓar Sanata waɗanda za su riƙa gudanar da shari’o’i na musamman, a cewar shugaban ƙungiyar masu noman rani na alkama na jiha, Mohammed Juli Adamu. Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewar, kafa waɗannan kotuna na musamman ya biyo bayan tattaunawa ne da ƙungiyar tasu ta yi da babban mai shari’a ta Jihar Bauchi, Mai Shari’a Rabi Talatu Umar, yayin da ‘yan ƙungiyar suka kai mata koke-koke kan ƙememe da manoman alkama suke yi na rashin biyan bashin noman alkama. Adamu, wanda ya…
Read More
Wasan mota: Ya yi silar gutsire ƙafar Fatima a Sakkwato

Wasan mota: Ya yi silar gutsire ƙafar Fatima a Sakkwato

*Tana murnar kammala jarrabawar NECO abin ya faru*Ba zan taɓa yafe wa Aliyu ba – Fatima*Ban aikata abinda ake zargi na ba – Aliyu*Kotu ta tasa ƙeyar matashin zuwa gidan gyara hali*Ba gudu ba ja da baya wajen ƙwato haƙƙin Fatima – Mahaifan Fatima*Sai mun tabbatar doka ta yi aiki kan Aliyu, cewar Hukumar Kiyaye Haɗura ta Sakkwato Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Wata ɗalibar matashiya mai suna Fatima Sulaiman Sabo mai shekaru 16 da haihuwa ta rasa ƙafarta a Sakkwato sakamakon yadda ake zargin wani matashi mai suna Aliyu da zama silar gutsire mata ƙafar a lokacin da ya…
Read More
An kori sojojin da suka kashe Sheikh Goni Aisami a Yobe

An kori sojojin da suka kashe Sheikh Goni Aisami a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Rundunar Sojojin Nijeriya ta bayyana ɗaukar matakin korar wasu sojojinta biyu bisa samun su da laifin kashe malamin addinin Musulunci, Sheikh Goni Aisami Gashuwa, a jihar Yobe. Sojojin da lamarin ya shafa su ne Lance Kofur John Gabriel da Lance Kofur Adamu Gideon. Sanarwar korar ta fito ne daga muƙaddashin kwamandan da ke kula da Bataliya ta 241 dake Nguru a jihar Yobe, Laftanar Kanar Ibrahim Osabo, inda ya shaida wa manema labarai cewa kwamitin binciken haɗin gwiwa da aka kafa tare da haɗin gwiwar 'yan sanda ya same su da laifi. Ya ƙara da…
Read More
Makarantar ST.Lous ta yi walimar ɗalibai 29 da suka yi saukar karatun Alƙur’ani Maigirma

Makarantar ST.Lous ta yi walimar ɗalibai 29 da suka yi saukar karatun Alƙur’ani Maigirma

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Makarantar ST Lous mai tsohon tarihi da ke Unguwar Bamfai a birnin Kano, ta yi bikin walimar taya ɗalibanta 29 murna da suka samu falalar rabauta da sauke karatun Alƙur'ani maigirma, a walimar da hukumar makarantar ta shirya musu wadda aka yi a harabar makarantar a ranar Larabar da ta gabata, kamar yadda Malama Halima Baba Yaro, mataimakiyar shugabar makarantar kuma wacce ta jagoranci bikin walimar ɗaliban 29, ta bayyana a lokacin walimar. Har ila yau, Malama Halima Baba Yaro, ta ce wannan ranar ba ƙaramar rana ba ce ga hukumar makarantar da malamai, da…
Read More