Labarai

Da ɗumi-ɗumi: ƴan Bindiga sun sace mahaifiyar ɗan takarar sanatan Kano ta tsakiya A.A Zaura

Da ɗumi-ɗumi: ƴan Bindiga sun sace mahaifiyar ɗan takarar sanatan Kano ta tsakiya A.A Zaura

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wasu da ake zargin ƴan ta’adda ne sun yi garkuwa da mahaifiyar ɗan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, Abdulkarim Abdulsalam Zaura, wanda aka fi sani da A.A Zaura. Rahotanni sun nuna cewa da sanyin safiyar Litinin din nan ne aka sace mahaifiyar ɗan siyasar, Hajiya Laure Mai Kunu kafin kiran Sallar Asubahi. Shugaban ƙaramar hukumar Ungogo, Injiniya Abdullahi Garba Ramat wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga Solacebase, ya ce jami’an tsaro sun sanar da shi lamarin a hukumance. Ya ce an yi garkuwa da Hajiya Laure ne a gidanta da…
Read More
Zaɓen APC: Sanata Adamu ya ƙaddamar da kwamitocin gudanarwa

Zaɓen APC: Sanata Adamu ya ƙaddamar da kwamitocin gudanarwa

Daga BASHIR ISAH A ranar Lahadin da ta gabata Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ƙaddamar da kwamitocin da za su ja ragamar gudanar da zaɓen fidda gwani na takarar Shugaban Ƙasa na jam'iyyar. Taron ƙaddamarwar ya gudana ne a Sakatariyar APC da ke Wuse 2, Abuja. APC za ta gudanar da zaɓen nata ne daga ranar 6 zuwa 8 ga Yuni, 2022, a dandalin Eagle Square da ke Abuja inda za ta tasayar da ɗan takararta na Shugaban Ƙasa a 2023.
Read More
Gwamnati za ta raya ƙasa murabba’in kilomita 22,000 da inganta rayuwar mutane miliyan 20 nan da 2030 – Minista

Gwamnati za ta raya ƙasa murabba’in kilomita 22,000 da inganta rayuwar mutane miliyan 20 nan da 2030 – Minista

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Gwamnatin Tarayya ta ayyana cewar, za ta farfaɗo da matacciyar ƙasa kimanin murabba’in kilomita 22,000, ta kuma inganta rayuwar ‘yan Nijeriya kimanin miliyan 20 nan da shekarar 2030. Ministan lura da muhalli, Alhaji Mohammed Abdullahi shi ne ya yi furucin haka a makon nan yayin gudanar da wata bitar ƙara wa juna sani kan ƙarfafa kuzarin gudanar da ayyuka da kuma fayyace tsarin manufar shirin nan na yin kadarko ko garkuwa daga kwararowar hamada (GGW) da aka gudanar a birnin tarayya na Abuja. Shirin, wanda aka tsara domin tafiya bai ɗaya da duniya kan bunƙasa…
Read More
‘Yan jarida na da muhimmiyar rawar takawa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa – YZ CITAD

‘Yan jarida na da muhimmiyar rawar takawa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa – YZ CITAD

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Cigaban Al'umma (CITAD), ta horar da 'yan jarida masu binciken ƙwaƙwaf dabarun ɗauko labaran cin hanci da rashawa da yaɗa shi, ga 'yan jaridu 20 da suka fito daga arewacin Nijeriya. Horarwar da ta gudana a cikin kwana 2, an yi ta ne a Pali Suite da ke Unguwar GRA ta jihar Bauchi. A jawabinsa, shugaban CITAD Yunusa Zakari Ya'u ya ce, maƙasudin shirya bitar shi ne sun lura cewa yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya ba ya samun nasarar da ya kamata ya samu. Ya ƙara da…
Read More
Sojojin Nijeriya sun kama baƙon-hauren ɗan ta’adda a Sakkwato

Sojojin Nijeriya sun kama baƙon-hauren ɗan ta’adda a Sakkwato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa, dakarun Operation Hadarin Daji, a ranar 21 ga watan Mayu, sun kama wani mai suna Jabe Buba, wani ɗan ƙasar waje kuma fitaccen ɗan ta’adda, a ƙauyen Garuwa dake Ƙaramar Hukumar Tambuwal a jihar Sakkwato. Darakta mai kula da ayyukan yaɗa labarai na tsaro, Manjo-Janar Bernard Onyeuko, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan sojoji a faɗin Nijeriya, tsakanin 19 ga watan Mayu zuwa 2 ga watan Yuni jiya Alhamis a Abuja. Mista Onyeuko ya ce an gano hotuna da bidiyo na…
Read More
Buhari bai tattauna batun karɓa-karɓa da ‘yan takara ba, cewar hadimin Sanata Adamu

Buhari bai tattauna batun karɓa-karɓa da ‘yan takara ba, cewar hadimin Sanata Adamu

Daga BASHIR ISAH An bayyana cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, bai tattauna batun tsarin karɓa-karɓa ba a tsakaninsa da 'yan takarar Shugaban Ƙasa na APC. Hadimin Shugaban APC na Ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Muhammad Nata'ala Keffi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar. Sanarwar ta ce, labarin da ke karakaina a kafafen sada zumunta na zamani dangane da tsarin mulkin karɓa-karɓa da aka ce Buhari ya zance a kai ba gaskiya ba ne, aikin masharranta ne kawai. Nata'ala ya ce, Shugaba Buhari cewa ya yi, "Ba tare da take cancantar kowa ba, ina kira gare ku…
Read More
‘Yan bindiga sun saki mai yi wa ƙasa hidima bayan biya Naira miliyan biyu

‘Yan bindiga sun saki mai yi wa ƙasa hidima bayan biya Naira miliyan biyu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 'Yan bindiga sun saki 'yar yi wa ƙasa hidima (NYSC) da suka sace a Kaduna, bayan sun cika sharuɗan da suka gindaya masu na biyan kuɗin fansa Naira miliyan biyu da katin waya na Naira dubu 100 da kuma babur. Faith Onoriode, wacce ta kammala Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Otefe, Oghara da ke Jihar Delta, a Tsangayar Nazarin Halittu da Ilimin Kananan Halittu (Biology/Microbiology), an sake ta ne bayan an cimma matsaya tsakanin iyayenta da waɗanda suka sace ta. SaharaReporters ta ba da rahoton cewa, Onoriode, an sace ta ne a kan hanyar…
Read More
Sakamakon shaƙar wani sinadari mutane da dama sun fita hayyacinsu a Kano

Sakamakon shaƙar wani sinadari mutane da dama sun fita hayyacinsu a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Rahotonni daga yankin rukunnin masana’antu na 3 da ke Sharada a jihar Kano na cewa, wasu mazauna unguwar Mundaɗu da dama sun fita daga hayyacinsu sakamakon shaƙar hayaƙin wani sinadari. Da yammacin jiya Juma’a ne dai gidan radiyon Freedom ya fara bada Labarin faruwar lamarin, yana mai cewa iftila’in ya faru ne sakamakon fashewar wata tukunyar sinadari ta masana’antu wadda ke ɗauke da guba. Kazalika Rahotan ya nuna cewa lamarin ya samo asali ne daga wani wurin masu yin sana’ar gwangwan da ke unguwar inda mai unguwar yankin Malam Magaji Abdullahi ya tabbatar da faruwar…
Read More
Ban aminta da ci gaba da bai wa CBN ajiyar kayan zaɓe ba – INEC

Ban aminta da ci gaba da bai wa CBN ajiyar kayan zaɓe ba – INEC

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce, ba za ta ci gaba da kai ajiyar muhimman kayan aikinta a Babban Bankin Nijeriya (CBN) ba. Shugaban INEC na ƙasa, Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan, yana mai cewa daga kan zaɓen gwamna na Jihar Ekiti, INEC ba za ta ƙara kai muhimman kayan aikinta a ajiya a CBN ba. A cewar Yakubu, domin kauce wa samun akasin kayan zaɓe a yayin zaɓuɓɓuka masu zuwa ya sa aka ɗauki wannan mataki. Ana ganin matakin da INEC ɗin ta ɗauka ba ya rasa nasa da bayyana ra'ayin shiga takarar da…
Read More