Labarai

Idon Mikiya: Buhari ya tare wa Shugaban NIA faɗa da gidan rediyon Vision FM

Idon Mikiya: Buhari ya tare wa Shugaban NIA faɗa da gidan rediyon Vision FM

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Gwamnatin Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ta dakatar da shirin ‘Idon Mikiya’, wanda wani shahararren shiri ne a gidan rediyon Vision FM da ke Abuja da wasu jihohin Arewa, saboda tattaunawa kan taƙaddamar tsawaita naɗin da aka yi wa Daraktan Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA), Alhaji Rufa'i Abubakar, da kuma zargin rashin iya aikinsa, lamarin da wasu ke kallo a matsayin tare wa shugaban na NIA faɗa da gidan rediyon na Vision FM. A cikin wata wasiƙa da ta aike wa Manajan Daraktan Gidan Rediyon Vision FM, wacce Blueprint Manhaja ta samu kwafi a…
Read More
Matsalar tsaro ba ta hana mu fita aiki ba – Shugaban Direbobin Tanka

Matsalar tsaro ba ta hana mu fita aiki ba – Shugaban Direbobin Tanka

Daga MUHAMMADU MUJITABA BIN USMAN Shugaban ƙungiyar direbobin dakon man fetur na ƙasa, wato ‘Petroleum Tankers Drivers’ (PTD), shiyyar Kano, Katsina, Jigawa da Yobe, Alhaji Sani Malam Garba ya ce kansancewar wannan sana’a ita suka iya Allah kuma ya sa suka dogara da ita, ya ce suna yi wa Ubangiji godiya duk da matsalilin lalacewar hanya da kuma matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar, ya ce hakan bai hana su gudanar da aikin su ba. Sani ya kuma janyo hankalin gwamnati kan gyara hanyoyin ƙasar nan baki ɗaya da kuma shawara kan dakatar da janye tallafin man fetir da gwamnatin…
Read More
Hisbah ta ƙwace kwalaben giya 1,906 da kama mutum 92 a Jigawa

Hisbah ta ƙwace kwalaben giya 1,906 da kama mutum 92 a Jigawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta ce ta ƙwace kwalaben giya 1,906 a sumamen da ta kai a lokuta daban-daban a faɗin jihar a shekarar da ta gabata, 2021. Kwamandan rundunar, Mallam Ibrahim Dahiru, shi ne ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya, NAN, a Dutse, babban birnin jihar, a ranar Talatar makon jiya. Mallam Ibrahim ya ce sun yi nasarar ƙwace giyar ne a otal-otal da wuraren shan barasa daban-daban a faɗin jihar. Shugaban Hisbar ya kuma ce sun kama mutum 92 da suke zargi da aikata laifuka na baɗala daban-daban, waɗanda suka…
Read More
Hare-haren Boko Haram/ISWAP sun yi ajalin jami’an tsaro 11 a Neja

Hare-haren Boko Haram/ISWAP sun yi ajalin jami’an tsaro 11 a Neja

*Sanata Sani Musa ya roƙi agajin Gwamnatin Tarayya Daga BASHIR ISAH Sanata mai wakiltar Neja ta Gabas a Majalisar Dattawa, Sanata Mohammed Sani Musa na jam'iyyar APC, ya yi tir da mabambantan hare-haren da mayaƙan Boko Haram/ISWAP suka kai a yankunan ƙaramar hukumar Paikoro da Shiroro tsakanin ranakun Juma'a da Asabar da suka gabata. Bayanai sun nuna sabbin hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar jami'an tsaro 11 tare da jikkata manoma da dama haɗa da lalata dukiya mai tarin yawa a yankuna da lamarin ya shafa. Cikin sanarwar da ya fitar ranar Laraba a Abuja, Sanata Sani ya bayyana kashe-kashen da…
Read More
Sojoji sun fatattaki ‘yan ta’adda a Katsina

Sojoji sun fatattaki ‘yan ta’adda a Katsina

Daga WAKILINMU A ci gaba da yaƙi da matsalolin tsaron da suka addabi shiyyar Arewa-maso-yammacin Nijeriya, sojoji sun fatattaki 'yan ta'adda wanda hakan ya yi ajalin wasu manyan 'yan ta'addan a jihar Katsina. Bayanan da MANHAJA ta kalato sun nuna cewa, luguden wutar da jirgin yaƙin sojojin sama (NAF) ya yi a Lahadin da ta gabata a yankin Ilela na jihar Katsina, ya haifar da galaba a kan 'yan ta'addan yankin tare da yi ajalin da damansu a sansanonin Gwaska Dankarami da Alhaji Abdulkarami, wanda duka su biyun gawurtattu ne. An gano cewa, 'yan ta'addan da aka halaka su ke…
Read More
Na kashe mutane sama da 20, cewar matashin ɗan ta’adda Naziru Sani

Na kashe mutane sama da 20, cewar matashin ɗan ta’adda Naziru Sani

*Ana biya na tsakanin N20000 zuwa N30000 bayan kowane hari da muka kai - Sani Daga BASHIR ISAH Matashin nan ɗan shekara 21 da ake zargin ɗan ta'adda ne, wato Naziru Sani, wanda ke aiki a ƙarƙashin gawurtaccen ɗan ta'adda Bello Turji, ya yi iƙirarin cewa ya kashe sama da mutum 20 a hare-hare da dama a faɗin Nijeriya. Matashin ɗan ta'addan ya bayyana hakan ne a lokacin da jami'i mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, SP Gambo Isah, ya gabatar da shi a gaban manema labarai a babbar hedikwatar rundunar a ranar Talata. An cafke Sani…
Read More
Mutane 36,000 sun ƙi amsar rigakafin Korona a Birnin Kudu

Mutane 36,000 sun ƙi amsar rigakafin Korona a Birnin Kudu

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Lissafi ya nuna kimanin mutane  36,000 ne suka ƙi amsar allurar rigakafin cutar Korona a yankin Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu da ke jihar Jigawa.  Jawabin hakan ya biyo bayan wata ziyara da kwamatin kiwon lafiya mai karfin gaske ya kai ziyara ƙaramar hukumar domin ganin an yi gangami wajen nuna wa jama'a muhimmancin rigakafin Korona. Kwamitin a ƙarƙashin jagorancin babban Sakataren Hukumar Lafiya kuma muƙaddashin kwamashinan lafiya na Jihar Jigawa Dr Sambo Ibrahim tare da manyan muƙarrabansa a hukumar lafiya matakin farko sun je ƙaramar hukumar ta Birnin Kudu domin gano kura-kuran dake ƙaramar…
Read More
Ɓatagari sun halaka gyatuma bayan sun yi mata fyaɗe a Ondo

Ɓatagari sun halaka gyatuma bayan sun yi mata fyaɗe a Ondo

Wasu ɓatagari da ake zargin Fulani makiyaye ne, sun yi taron dangi wajen yi wa wata mata mai suna Mrs Roseline Joguntan fyaɗe sannan suka halaka ta bayan haka a ƙauyen Igbokoda da ke cikin yankin ƙaramar hukumar Ilaje, jihar Ondo. Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa, an aikata wa matar wannan ɗanyen aiki ne a gonarta sa'ilin da ta je ɗibar 'yan'yan itatuwa kamar yadda ta saba tare da ɗaya daga cikin 'ya'yanta. Majiyar jaridar ta ce, "Bayan da marigayiyar ta ɗibi kwandon farko na 'ya'yan itatuwan ne sai ta buƙaci 'yarta ta ɗauka ta kai gida, ko da…
Read More

Yadda taron kacici-kacici da raba kyautuka akan harshen Hausa ya gudana a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ƙungiyar Ɗaliban Hausa ta Nijeriya ta gudanar da taron gasar kaci-kaci da a tsakanin makarantun gaba da sakandire na jihar Kano, da kuma raba kyautuka ga zakarun gasar waƙoƙin Hausa da ya gudana a ɗakin taro na Convocation Arena da ke Jami'ar Bayero, Kano. Taron dai ya mayar da hankali ne wajen wayar da kan matasa a kan illolin shaye-shaye a tsakanin matasa, waɗanda suka shiga gasar waƙar Hausar dai aƙalla sun kai guda 73. Taken taron shi ne, "Aiki da hankali', wanda Mataimakin Gwamnan na Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya ɗauki nauyin gudanarwa.…
Read More
Jakadan Bauchi: Kwance rawanina zancen baki ne kawai, inji Dogara

Jakadan Bauchi: Kwance rawanina zancen baki ne kawai, inji Dogara

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Rt. Hon. Yakubu Dogara ya danganta dakatar da sarautar sa ta gargajiya na Jakadan Bauchi da majalisar masarautar Bauchi ta yi a ranar Litinin da ta gabata a matsayin zance ne na baki wanda bai kai ga zuciya ba. Ya ce, “kawo wannan rana ta Talata, ba wata takardar dakatarwa da aka bani, kuma har ila yau babu wanda ya sanar da ni cewar, akwai wani ƙagen laifi da ake tuhuma ta da shi a gaban majalisar masarautar Bauchi.” Da yake numfasawa kan zargin dakatar da sarautar sa ta Jakadan…
Read More