Labarai

Tashar RFI ta yi babban rashi

Tashar RFI ta yi babban rashi

Allah ya yi wa mataimakin Editan sashin Hausa na gidan rediyon Faransa (RFI), Garba Aliyu Zaria rasuwa. Sanarwar rasuwar ta fito ne ta hannun Editan RFI, Bashir Ibrahim Idris, inda ya ce marigayin ya rasu ne bayan fama da gajeruwar jinya. Ko jiya Asabar, an ji Garba Aliyu ya gabatar da shiri inda a yau kuma aka wayi gari da labarin rasuwarsa. Marigayin na ɗaya daga cikin waɗanda suka yi tsayin daka wajen kafuwar sashen Hausa na gidan rediyon Faransa (RFI). Bayanai sun nuna za a yi jana'izar marigayin ne sa yau Lahadi a birnin Legas.
Read More
‘Idon Mikiya’: Matakin NBC ya fallasa take-taken gwamnati na neman daƙile ‘yancin faɗar albarkacin baki – CISLAC

‘Idon Mikiya’: Matakin NBC ya fallasa take-taken gwamnati na neman daƙile ‘yancin faɗar albarkacin baki – CISLAC

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar nan mai fafutukar kare haƙƙin al'umma da aka fi sani da CISLAC a taƙaice, ta yi tir da matakin ƙaƙaba wa gidan rediyon Vision FM takunkumi da Gwamnatin Tarayya ta yi. Gwamnatin Tarayya ta kafa wa tashar Vision takunkumi ne sakamakon tattaunawar da ta yi kan abin da ya shafi sake naɗa shugaban Hukumar Leƙen ta Ƙasa (NIN), Ahmed Rufai Abubakar a cikin wani shirinta mai taken 'Idon Mikiya'. Sai dai da alama wannan mataki da Shugaba Muhammadu Buhari ya ɗauka bai yi wa wasu jami'an tsaron hukumar da masu ruwa da tsaki da daɗi ba.…
Read More
Majalisar dokokin Zamfara tana yunƙurin tsige mataimakin gwamna Mahadi Aliyu

Majalisar dokokin Zamfara tana yunƙurin tsige mataimakin gwamna Mahadi Aliyu

Daga SANUSI MUHAMMAD, Gusau Majalisar Dokokin jihar Zamfara ta fara wani sabon yunƙurin tsige mataimakin gwamnan jihar Barr. Mahadi Aliyu Muhammad Gusau. Rahotanni sun nuna cewar, Mataimakin Gwamnan dai ya shafe kusan watanni shida bai je ofis ba inda ya tare a Abuja daga Gusau babban birnin jihar tun lokacin da Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya fice daga PDP ya koma APC mai mulki a ƙasar. Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa tuni aka miƙa takardar tsige shugaban majalisar dokokin jihar ga Kakakin Majalisar, Hon. Nasiru Muazu Magarya a safiyar jiya Juma'a domin ɗaukar matakan ƙarshe. Majiyar mu daga majalisar dokokin…
Read More
Gwamna Ganduje ya miƙa sandar mulki ga Sarkin Gaya

Gwamna Ganduje ya miƙa sandar mulki ga Sarkin Gaya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Manyan mutane da manyan sarakuna a faɗin ƙasar nan ne suka haɗu a garin Gaya wurin bai wa Sarki Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya (Karmau mai Gabas) sanda, da ya gudana cikin garin Gaya a ranar Asabar da ta gabata. Sabon sarkin ya gaji mahaifinsa ne Marigayi Alhaji Ibrahim Abdulkadir wanda ya rasu a 22 ga Satumbar shekarar da ta gabata yana da shekara 91. Naɗin ya biyo bayan amincewar da masu naɗa sarki a fadar suka yi, inda gwamnati ta aminta a naɗa sabon sarkin. Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya taya sarkin na Gaya…
Read More
Mu cigaba da ɗora mabiyanmu kan turbar zaman lafiya – Sarkin Hausawan Ijede

Mu cigaba da ɗora mabiyanmu kan turbar zaman lafiya – Sarkin Hausawan Ijede

Daga DAUDA USMAN a Legas  Tun bayan shigowar sabuwar shekarar Miladiya ta bana waɗansu daga cikin al'ummar Nijeriya suke ta gudanar da addu'o'i na musamman domin neman izini a wajen Ubangiji Subahanahu wata Ala na ƙarin samun zaman lafiya a ƙasar nan tare da kiraye-kiraye ga sarakunan al'ummar Hausawa mazauna jihohin Kudu da yammacin Nijeriya da sauran shuwagabannin al'ummar qasar nan da su cigaba da ɗora mabiyansu a bisa kan turbar zaman lafiya. Alhaji Muhammadu Rabiu Sale ɗan asalin ƙaramar hukumar Funtuwa ta jihar Katsina mazaunin birnin Legas kuma Sarkin al'ummar Hausawan Unguwar Ijede dake ƙaramar hukumar Ikorodu a Legas,…
Read More
‘Idon Mikiya’: Amnesty International ta yi tir da matakin NBC a kan Vision FM

‘Idon Mikiya’: Amnesty International ta yi tir da matakin NBC a kan Vision FM

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da matakin dakatar da tashar Vision FM 92.1 Abuja, daga gabatar da shirin nan nata mai taken 'Idon Mikiya', da hukumar kula da kafafen yaɗa labarai ta ƙasa, NBC ta ɗauka. Ƙungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta cire wa tashar rediyon takunkumin da ta ƙaƙana mata da kuma sake duba tarar da ta zabga mata. Ƙungiyar ta yi waɗannan bayanan ne cikin wata sanarwa da ta fitar da ta sami sa hannun Daraktan ƙungiyar, Osai Ojigho, tana mai cewa ɗaukar matakin tamkar farmaki ne ga 'yancin bayyana…
Read More
Idon Mikiya: Ba mu muka kar zomon ba – kamfanin Vision ya mayar wa Hukumar NBC martani

Idon Mikiya: Ba mu muka kar zomon ba – kamfanin Vision ya mayar wa Hukumar NBC martani

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Kamfanin Gidan Rediyon Vision FM da Gidan Talabijin na Farin Wata ya mayar da martani kan dakatar da shirinsa na ‘Idon Mikiya’ da Gwamnati Shugaba Buhari ta yi kan tattauna batun tsawaita naɗin da aka yi wa Daraktan Hukumar Leqen Asiri ta Ƙasa (NIA), Rufa'i Abubakar, da kuma zargin rashin iya aikinsa, kamfanin yana mai cewa, shine ya kar zomon ba, rataya aka ba shi. Martanin da ya ke rubuce ne a wata takarda da Shugaban Kamfanin Yaɗa Labarai na Vision Media, Alhaji Umar Faruk Musa, ya aike wa Hukumar NBC, ya nuna cewa,…
Read More
Mutane 1,129 aka kashe a Kaduna shekarar 2021 – Gwamnatin Kaduna

Mutane 1,129 aka kashe a Kaduna shekarar 2021 – Gwamnatin Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufa'i ya bayyana cewa hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa a Arewa maso yammacin Nijeriya ya fi na Boko Haram muni. El-Rufai wanda ke jawabi a wajen taron gabatar da rahoton tsaro na shekarar 2021, ya ce rahoton da aka fitar na bara ya tabbar da cewa akwai aiki gaban mahukunta. Gwamnan ya ce ya kamata gwamnati ta ɗauki tsauraran matakan tsaro kan hare-haren 'yan bindiga a Arewa maso Yamma fiye da yadda ta yi kan 'yan Boko Haram. Gwamnatin jihar Kaduna ta ce an kashe mutane 1,129…
Read More
Akwai rufin asiri a cikin sana’ar fawa – Sarkin Fawa Usaini

Akwai rufin asiri a cikin sana’ar fawa – Sarkin Fawa Usaini

Daga DAUDA USMAN a Legas Sarkin fawar ƙaramar hukumar Amuwo Odofin a Legas, Alhaji Usaini Iliyasu bakin sabuwar kasuwar Bichi mazaunin Legas wanda yake gudanar da harkokin kasuwancin sana'ar fawa akan titin Bila fak tasakwan rebo kusa da Mile 12 titin a cikin birnin Legas, ya bayyana cewar akwai rufin asirin Ubangiji a cikin sana'ar fawa idan aka tsare gaskiya da riƙon amana. Sarkin fawan, Alhaji Usaini Iliyasu bakin sabuwar kasuwar Bichi wanda ya bayyana hakan a ofishin sa dake Bila fak jim kaɗan bayan kammala taron su da waɗansu mahautan kasuwannin cikin garin Legas waɗanda suka zo masa murnar…
Read More
Kotu ta bada umarnin dawo da shaidar farko a shari’ar Sheikh Abdujjabar

Kotu ta bada umarnin dawo da shaidar farko a shari’ar Sheikh Abdujjabar

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A safiyar ranar Alhamis ne aka ci gaba da gabatar da shari’ar Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Abdujabbar Nasir Kabara, wanda aka gurfanar da shi a gaban kotun shari’ar Musulumci da ke zaman ta a Ƙofar Kudu a jihar Kano. A zaman kutun, Barista A. O. Mohammed (SAN) ne ya jagorance lauyoyin da suke kare Malam Abdujabbar, inda Barista Sa’ida Shu’aibu (SAN) ya jagoranci tawagar lauyoyin masu gabatar da ƙara. Lauyoyin malamin sun nemi a dawo musu da shaidar farko, domin sake yi masa tambayoyi, sai dai vangaren da suke gabatar da ƙara sun yi suka…
Read More