Tashar RFI ta yi babban rashi

Allah ya yi wa mataimakin Editan sashin Hausa na gidan rediyon Faransa (RFI), Garba Aliyu Zaria rasuwa.

Sanarwar rasuwar ta fito ne ta hannun Editan RFI, Bashir Ibrahim Idris, inda ya ce marigayin ya rasu ne bayan fama da gajeruwar jinya.

Ko jiya Asabar, an ji Garba Aliyu ya gabatar da shiri inda a yau kuma aka wayi gari da labarin rasuwarsa.

Marigayin na ɗaya daga cikin waɗanda suka yi tsayin daka wajen kafuwar sashen Hausa na gidan rediyon Faransa (RFI).

Bayanai sun nuna za a yi jana’izar marigayin ne sa yau Lahadi a birnin Legas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *