09
Feb
"Matakin da gwamnatin Buhari da NBC suka ɗauka, wata alama ce da ke nuni da take-taken da ake yi na neman yi wa kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu kisan mummuge da hana ɗaiɗaikun mutane 'yancin faɗar albarkacin bakinsu" - SERAP Daga BASHIR ISAH Ƙugiyar SERAP ta ce babu abin da zai hana Hukumar Kula da Gidajen Rediyo ta Ƙasa (NBC) fuskantar matakin shari'a cikin sa'o'i ashirin da huɗu sai dai idan ta janye tarar Naira miliyan 5 ɗin da ta yanka wa gidan rediyon Vision FM da ke Abuja. Idan dai ba a manta ba, Manhaja ta rawaito yadda…
