12
Feb
Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar daƙile wani harin 'yan bindiga da yammacin ranar Juma'a tare da ƙwato dabbobi kimanin 350 daga hannun 'yan ta'adda. Kakakin rundunar SP Gambo Isa ne ya sanar da hakan a yau Asabar cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a birnin Katsina. SP Isa ya bayyana cewar sun samu nasarar fatattakar 'yan bindigar ne sakamakon kiran gaggawa da rundunar ta samu da yammacin ranar Juma'a, inda mazauna ƙauyen Nassarawar Bugaje da ke a ƙaramar hukumar Jibiya ta jihar Katsina suka sanar da rundunar cewar gungun…
