Labarai

Yajin aikin jami’o’i: Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya ta caccaki ASUU da Gwamnatin Tarayya

Yajin aikin jami’o’i: Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya ta caccaki ASUU da Gwamnatin Tarayya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya wato NANS, ta yi Allah wadai da sabon yajin aikin da Ƙungiyar Malaman Jami’a ASUU suka sake tafiya. A ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu 2022 ne shugaban ƙungiyar NANS na ƙasa, Asefon Sunday ya fitar da jawabi ga manema labarai, yana kokawa a kan wannan yajin aikin. Asefon Sunday ya haɗa da Gwamnatin Tarayya da shugabannin ASUU, ya yi masu ta-tas a kan yadda suka gaza shawo kan batun ba tare da rufe jami’o’i ba. “Mun samu labarin matakin da ƙungiyar ASUU ta ɗauka na shiga yajin aikin jan-kunne na…
Read More
’Yan bindiga sun sace sama da mutane 50 a Katsina

’Yan bindiga sun sace sama da mutane 50 a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Ɓarayin daji sun sace sama da mutum 50 a ƙauyen Ruwan Goɗiya da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina. Rahotanni sun tabbar da cewar maharan su fiye da 60 akan babura kimanin 30 sun kutsa kai a garin na Ruwan Goɗiya inda su ka yi ta yin harbi a kan mai uwa da wabi. Wani mazaunin garin da aka sakaya sunansa ya shaida wa jaridar Daily trust cewa ‘yan bindigar sun ci karensu ba bu babbaka tsawon sa’a biyu, ba tare da wasu jami’an tsaro sun kai ɗauki ba, duk da cewa akwai sojoji…
Read More
Imam Suleiman ya shawarci matasa su ƙaurace wa ’yan siyasar sara-suka

Imam Suleiman ya shawarci matasa su ƙaurace wa ’yan siyasar sara-suka

Daga DAUDA USMAN a Legas  Babban limamin masallacin Juma'a na rukunin gidajen unguwar Wantauzan a Victoria Ireland dake cikin birnin Legas, Sheikh Imam Suleman Ibrahim kuma shugaban ƙungiyar Jama'atul Izalatul Bidi'a Wa Iƙamatussunah ta ƙasa reshen  jihar Legas ya ce ganin cewar lokacin siyasa yana ci gaba da ƙara tunkarowa, kuma mafi yawan 'yan siyasa da sauran waɗansu al'ummar Musulmi sun sauka bisa kan sunnar Manzon Allah suna amfani da wannan lokacin suna ɓata yaran mutane a wajen koya masu shaye-shayen kayan maye tare da koya masu aikata miyagun ayyukan kaba'ira  domin biyan buƙatar kansu a wajen gudanar da harkokin…
Read More
Mu na fatan gwamnati ta samar wa masu buƙata ta musamman aiki – Sani Dambatta

Mu na fatan gwamnati ta samar wa masu buƙata ta musamman aiki – Sani Dambatta

Daga BABANGIDA GORA a Kano An yi kira ga gwamnati da ta yi ƙoƙari wajen samar wa masu buƙata ta musamman gurabun aikin gwamnati domin su ma a dama da su. Hakan ya fito ne daga bakin sakataren ƙungiyar masu taimaka wa masu buƙata ta musamman ta Kanawa Malam Sani Lawal Ɗambatta a wata zantawa da ya yi da wakilinmu a satin da ya gabata. Sannan sakataren ya kuma bayyana cewa tun farkon tafiyar wannan gidauniya ta samo asali ne daga Marigayi Malam Abba Sarki da Allah ya yi wa rasuwa shekarun baya sakamakon rashin lafiyar da ta ritsa shi…
Read More
Safarar miyagun ƙwayoyi: Abba kyari da mataimakansa sun shiga hannu

Safarar miyagun ƙwayoyi: Abba kyari da mataimakansa sun shiga hannu

Daga BASHIR ISAH Bayan bada sanarwar neman DCP Abba Kyari da hukumar NDLEA ta yi da wasu 'yan sa'o'i ne 'ya sanda suka bada sanarwar Kyari ya faɗa a komarsu. A jiya Litinin NDLEA ta yi shelar tana neman Abba Kyari ruwa a jallo bisa tuhumarsa da hannu cikin badaƙalar safarar miyagun ƙwayoyi, bayan da ya ƙi amsa mata gayyata don amsa mata tambayoyi. Bayanai daga mai maganaa da yawun NDLEA, Femi Babafemi, sun nuna 'yan sanda sun kama tare da miƙa musu DCP Abba Kyari, tsohon kwamandan rundunar IRT. Jami'in ya ce an miƙa Abba Kyari ne tare da…
Read More
ASUU ta soma yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya

ASUU ta soma yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta soma yajin aiki don neman cimma buƙatunta a wajen Gwamnatin Tarayya. ASUU ta bayyana soma yajin aikin nata ne ga manema labarai a wannan Litinin. Da yake yi wa manema labarai bayani kan matakin da suka ɗauka bayan kammala tattaunawar yini biyu da shugabbanin ƙungiyar suka yi, shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce yajin aikin nasu na tsawon wata guda ne a matsayin gargaɗi ga gwamnatin ƙasa. Ya ce tun a ranar Asabar da ta gabata shugabannin ASUU na ƙasa suka soma zaman tattaunawa a Jami’ar Legas kan batun.…
Read More
Tsohon ɗan Majalisar Tarayya ya zama hadimin Aisha Buhari

Tsohon ɗan Majalisar Tarayya ya zama hadimin Aisha Buhari

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Hon. Sani Zorro a matsayin Babban mai taimaka masa na musamman a kan Dabarun Hulɗa da Jama'a a ofishin Matar Shugaban Ƙasa. Sabon babban mai taimakawa na musamman a Ofishin matar shugaban ƙasa, Muhammad Sani Zorro dai ƙwararren ɗan jarida ne kuma jagora a aikin jarida a Nijeriya, Afirka, da ma duniya. Babban mai taimaka wa Shugaban Ƙasa a kan harkar yaɗa labarai, Garba Shehu ne ya tabbatar da naɗin a wata sanarwar da ya fitar a Asabar da ta gabata a Abuja. Shehu ya ce Zorro zai yi…
Read More
Kwamishinan Zamfara ya ɗauki nauyin auren ’yan mata marayu 20

Kwamishinan Zamfara ya ɗauki nauyin auren ’yan mata marayu 20

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Kwamishinan ma'aikatar raya otal-otal da yawon buɗe ido na jihar Zamfara Hon. Abubakar Abdullahi ya ɗauki nauyin auren yara mata marayu su 20 a ƙaramar hukumarsa Tsafe. Da yake jawabi yayin bikin ɗaurin auren da aka gudanar a fadar mai martaba Sarkin Tsafe ranar Lahadin da ta gabata, mai martaba Sarkin Tsafe Alhaji Muhammad Bawa ya yaba wa kwamishinan bisa jajircewarsa na inganta tarbiyya da rayuwar marasa galihu a yankin. Sarkin ya yi kira ga masu arzikin yankin da su yi koyi da shi wajen inganta rayuwar marasa galihu a masarautarsa. "Ina so in yi…
Read More
An cafke ɗan shekara 14 mai garkuwa da yin fyaɗe a Zamfara

An cafke ɗan shekara 14 mai garkuwa da yin fyaɗe a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jami'an hukumar tsaro na Civil Defence sun yi nasarar cafke wani yaro mai suna Sani Suleiman ɗan kimanin shekara 14 da ake zargi da laifin sata da yin garkuwa da mutane a Jihar Zamfara.  Labarin hakan ya fito ne daga bakin babban kwamandan rundar jami'an tsaron farin kaya ta jihar, A.A Spark a lokacin da yake gabatar da mai laifin ga manema labarai ranar Laraba.  A cewarsa, an cafke Suleiman ne a ƙauyen Kadage da ke yankin Masarautar Moriki a Ƙaramar Hukumar Zurmi  Kamar yadda rahoton ya nuna, ƙaramin yaron ya samu horo ne…
Read More
An yi jana’izar Magajin Garin Sakkwato, Hassan Danbaba

An yi jana’izar Magajin Garin Sakkwato, Hassan Danbaba

Allah Ya yi wa Magajin Garin Sakkwato, Alhaji Hassan Ahmad Danbaba, rasuwa. Wata majiya ta kusa da ahalin marigayin ta ce, marigayin ya rasu ne ran Asabar a Kaduna bayan fama da rashin lafiya. Dangi, 'yan'uwa da abokan arziki na kusa da nesa sun bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ba ga jihar Sakkwato kaɗai ba har ma da ƙasa baki ɗaya. Tuni dai aka gudanar da jana'izar marigayin a Sakkwato daidai da karantarwar addinin Islama.
Read More