30
Jan
Daga WKAILINMU A ranar Talatar da ta gabata ne a Jihar Zamfara aka gurfanar da wasu mutum biyar a gaban kotun majistare mai lamba ɗaya a Gusau, bisa zarginsu da kashewa tare da cin naman wani yaro. Daga cikin waɗanda aka gurfanar ɗin kuma ake zargi, har da wani fitaccen dillalin motoci a Jihar. Ana dai zarginsu ne da kashewa sannan suka ci naman Ahmad Yakubu Aliyu, wani yaro mai kimanin shekara tara a duniya. An dai kawo mutanen da ake zargi ne gaban kotun cikin tsauraran matakan tsaro. Sai dai bayan da alƙalin kotun, Mai Shari’a Sa’adu Gurbin Bore…
