Labarai

‘Yan jarida suna da rawar da za su taka wajen magance ta’addanci a ƙasa – Farfesa Khalid Zaria

‘Yan jarida suna da rawar da za su taka wajen magance ta’addanci a ƙasa – Farfesa Khalid Zaria

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An bayyana 'yan jarida a matsayin wasu mutane da suke da muhimmanci a cikin al'umma, kuma waɗanda ke da rawar da za su iya takawa wajen magance tashe-tashen hankula da ta'addanci a Nijeriya. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shehin malamin nan masanin tarihi da harsunan Afrika, Farfesa Khalid Abdullahi Zaria, a wajen taron gabatar da littafin sa a ranar Lahadi a Agura Otal da ke Abuja, wanda ya rubuta akan rayuwar tsohon gwamnan Jihar Kwara, kuma tsohon shugaban majalisar dattawa ta takwas, Dr. Abubakar Bukola Saraki. Farfesa Abdullahi ya yi nuni da…
Read More
Mawaƙi M. Shareef ya zama Ambasadan gidan talabijin na Qausain TV

Mawaƙi M. Shareef ya zama Ambasadan gidan talabijin na Qausain TV

Daga WAKILINMU Sabon gidan talabijin na Qausain ya naɗa shahararren mawaƙi Umar M. Shareef a matsayin jakadansa na farko a Kaduna. Babban Shugaban Kamfanin Qausain Group, Alhaji Nasir Musa Idris (Albani Agege) ne ya bayyana haka a yayin ƙaddamarwar wanda gidan talabijin ɗin ya shirya a harabar ofishinsa da ke Sultan Road, GRA Kaduna a wannan makon. Shugaban kamfanin ya bayyana jin daɗinsa tare da kuma miƙa godiyarsa ga Allah SWT da kuma ilahirin ma'aikata da waɗanda suka bada gudumuwa har wannan gidan talabijin ya tabbata. Malam Nasir ya bada tabbacin cewa gidan talabijin ɗin zai ta fi daidai da…
Read More
Cire tallafin mai: Ƙungiyar Ƙwadago za ta gudanar da zanga-zanga a faɗin Nijeriya

Cire tallafin mai: Ƙungiyar Ƙwadago za ta gudanar da zanga-zanga a faɗin Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya NLC, ta ce ta shirya tsaf domin tsunduma cikin gagarumar zanga-zanga a faɗin Nijeriya a ranar 1 ga watan Fabrairu, domin nuna rashin goyon bayan shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ke yi na cire tallafin man fetur gaba ɗaya. Ƙungiyar ta yanke shawarar ne a wani jawabin bayan taro da ta fitar a ranar Juma'a, wanda Shugaban ta na ƙasa, Kwamared Ayuba Wabba da kuma Babban Sakataren ta, Emmanuel Ugboaja su ka rattava wa hannu bayan taron majalisar zartarwar. NLC ta ce kafin zanga-zangar ta ƙasa, rassan ta na jihohi za…
Read More
Yadda sojojin Nijeriya suka yi galaba kan rundunar Bello Turji a Sakkwato

Yadda sojojin Nijeriya suka yi galaba kan rundunar Bello Turji a Sakkwato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A daidai lolacin da matsalar tsaro ta ta'azzara a Arewa maso Yammacin Nijeriya, rahotanni sun tabbatar da ƙoƙarin da sojoji ke yi na kakkave 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihohin Katsina, Zamfara da Sakkwato, inda rahotanni ke cewa sojojin sun yi nasarar kakkaɓe rundunar kwamandan dajin nan Bello Turji, wanda ya addabi yankunan Sakkwato da Zamfara. Shaidun gani da ido sun ce babban kwamandan sojin da ke kula da runduna ta 8, Manjo Janar Uwem Bassey ya jagoranci tawagar sojoji tare da manyan jami’an sa a cikin motocin yaƙi sama da…
Read More
NDLEA ta kuɓutar da yara 34 da aka yi safarar su daga Arewa zuwa Kudu

NDLEA ta kuɓutar da yara 34 da aka yi safarar su daga Arewa zuwa Kudu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta kuɓutar da wasu ƙananan yara 34 a kan babbar hanyar Okene zuwa Lokoja a jihar Kogi. Kakakin hukumar, Femi Babafemi shine ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar, sanarwar ta kuma bayyana cewa hukumar ta ƙwace sassan ƙarafunan bindiga a jihar Anambara. A cewar sanarwar, yaran da hakumar ta kuɓutar sun kasance tsakanin shekaru 8 zuwa shekara 14, waɗanda aka yi safararsu ba bisa ƙa’ida ba daga jihar Ogun zuwa birnin tarayya Abuja. Ya ce da fari an yi…
Read More
Zan yi aiki tuƙuru kafin na koma Daura in ci gaba da kula da dabbobina a 2023 – Buhari

Zan yi aiki tuƙuru kafin na koma Daura in ci gaba da kula da dabbobina a 2023 – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce zai mayar da hankali wajen cigaban Nijeriya da al’ummarta kafin ƙarshen wa’adinsa, inda ya ce zai koma mahaifarsa Daura da ke Jihar Katsina domin ci gaba da kulawa da gona da kuma dabbobinsa. Shugaban ya bayyana haka ne tare da hotunan bikin zagayowar haihuwarsa wanda ofishin jakadancin Nijeriya a ƙarƙashin Ministan Kula da Harkokin Ƙasashen Waje, Mista Geoffery Onyeama suka yi masa ba-zata a birnin Istanbul da ke ƙasar Turkiyya. Buhari wanda ya tafi ƙasar Turkiyya domin halartar taro, a ranar Juma'a ya cika shekara 79 da haihuwa.…
Read More
Korona: Hana ‘yan Nijeriya zarya zuwa wasu ƙasashe ya fusata Buhari, ya ce sai ya rama

Korona: Hana ‘yan Nijeriya zarya zuwa wasu ƙasashe ya fusata Buhari, ya ce sai ya rama

Daga BASHIR ISAH A matsayin wani mataki na maida martani kan hana 'yan Nijeriya shiga wasu ƙasashen duniya saboda korona, Gwamnatin Tarayya ta ce daga ranar Talata mai zuwa, 14 ga Disamba, za ta haramta wa jiragen saman da suka fito daga Canada da Birtaniya da kuma Saudiyya shigowa Nijeriya. Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, shi ne ya bada sanarwar ɗaukar wannan mataki a Legas ranar Lahadi, inda ya ce an ɗauki matakin ne don maida martani kan ƙasashen da suka haramta wa jiragen da suka fito daga Nijeriya shiga cikinsu domin ɓarkewar sabon nau'in cutar korona mai suna…
Read More
EFCC na bincikar wani gwamnan Arewa kan fitar da Naira Biliyan 60 a banki

EFCC na bincikar wani gwamnan Arewa kan fitar da Naira Biliyan 60 a banki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa tu'annati (EFCC), ta tuhumi wani Gwamnan Arewa bisa zargin fitar da kuɗi har Naira biliyan 60 daga baitulmalin jihar da kansa. Hukumar EFCC, wacce ta bayyana hakan a yau a cikin sabuwar sanarwarta, ta ce, gwamnan ya fito ne daga yankin Arewa ta Tsakiyar ƙasar nan amma ba ta bayyana sunansa ba. Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, wanda ya yi magana a sanarwar, ya ce, “zan iya gaya muku cewa sabuwar sashen leƙen asirin da muka ƙirƙiro ne yake yin irin waɗannan abubuwan al’ajabi.” Ya…
Read More
ASUU ta samu biliyan N52.5 daga hannun Gwamnatin Tarayya

ASUU ta samu biliyan N52.5 daga hannun Gwamnatin Tarayya

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta biya malaman jami’o’i Naira biliyan 30 na asusun farfaɗo da ilimi da kuma alawus-alawus na ilimi da suka samu Naira biliyan 22.5, tare da jaddada cewa ta samu cigaba sosai wajen aiwatar da yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma da ma’aikatan jami’o’in. Ministan Ƙwadago, Sanata Chris Ngige shi ne ya tabbatar da hakan yayin tattaunawarsu da jaridar THISDAY a wannan ƙarshen makon a lokacin da yake ƙarin haske kan halin da ake ciki tsakanin gwamnati da ƙungiyar ASUU. Ministan ya ce ya samu sanarwa daga Ma'aikatar Kuɗi ta Tarayya kan cewa…
Read More
Yadda ɗa ya yi wa matar mahaifinsa ciki a Nasarawa

Yadda ɗa ya yi wa matar mahaifinsa ciki a Nasarawa

Daga WAKILINMU Wata matar aure a jihar Nasarawa ta bayyana cewa, ɗan mijinta ne ya ɗirka ma ta ciki. Matar ta ɗora laifin kan mijin nata da ta ce, ya gabatar ma ta da ɗan nasa ne a matsayin ɗan uwansa ba ɗan cikinsa ba. Ta ƙara da cewa, “auren saurayi da budurwa muka yi ni da mijina, wanda yanzu ya rasu. Mun fara samun matsala ne bayan na shafe shekara biyar ba tare da na yi ko ɓatan wata ba. Hakan ne ya sa surukata ta dinga tsangwama ta har shi ma ya goyi bayanta saboda rashin samun ciki…
Read More