12
Dec
Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Cibiyar Karrama Shahararrun Mutane na Afrika da ke Landan 'African Achievers Award' ta karrama Dr. Dauda Lawal Dare a shekaran jiya Juma'a, 10 ga watan Disamba a Fadar Kensisngton dake Birnin Landan. Kambun karramawa na 'African Achievers Award' shi ne mafi girma da tasiri a duniya wanda ya ke zaƙulowa tare da karrama mutane masu muhimmanci da suke taka rawa wurin bunƙasar nahiyar Afirka. Taken taron bana shi ne: 'Samar da hanya ga mazauna ƙasashen ƙetare su zuba jari don bunƙasar tattalin arzikin Afirka'. Mujallar Forbes ta ruwaito cewa, wannan bikin karramawa na 'African…
