11
Dec
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Alhamis da ta gabata Ƙungiyar Malaman Jami'a ta Nijeriya ASUU ta koka kan yadda Gwamnatin Tarayya ta kasa cika mata alƙawarin da aka daɗe ana kai ruwa rana tsakanin ƙungiyar da gwamnati. Lamarin da ya sa ƙungiyar ASUU ta fara rara-gefe da barazanar komawa yajin aiki. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa Ƙungiyar Malaman Jami'a ASUU tana cewa har zuwa yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta ce komai ba game da buƙatun da suke nema daga gareta bayan shafe sati uku da suka gindaya. Kwadinetan ƙungiyar ta ASUU, Dr. Salahu…
