Labarai

Noman rani: Gwamna Sule ya ƙaddamar da shirin saida takin zamani

Noman rani: Gwamna Sule ya ƙaddamar da shirin saida takin zamani

Daga BASHIR ISAH A matsayin wani mataki na bunƙasa noman rani a 2022 a jaihar Nasarawa, Gwamnan Jihar, Engr. Abdullahi A. Sule, ya ƙaddamar da shirin sayar da takin zamani don tallafa wa manoman rani a jihar. Ƙaddamarwar ta shafi har da sauran kayayyakin aikin gona, inda gwamnan ya bayyana farashin takin kan N7000 ga kowane buhu. Sa'ilin da yake jawabi, A.A Sule ya yi kira ga manoman da za su ci gajiyar shirin da su yi amfani da wannan dama wajen ci gaba da wadata jihar da kewaye da abinci. Taron ƙaddamarwar ya gudana ne a harabar hedikwatar cibiyar…
Read More
Yadda mota ta yi ajalin ɗaliban firamare 17 a Legas

Yadda mota ta yi ajalin ɗaliban firamare 17 a Legas

Daga BASHIR ISAH A Talatar da ta gabata aka samu aukuwar wani mummunan haɗari wanda ya laƙume rayukan ɗaliban makarantar Omole Primary School da ke yankin Ojodu a jihar Legas, su 17 ciki har da yara uku 'yan gida ɗaya. Faruwar wannan ibtila'in ya tada hankalin mazauna yankin gaya, lamarin da ya fusata ɗaliban sakandaren da ke kusa inda suka fito suka tare hanya sannan suka fafari babbar motar da ta aikata wannan ɗanyen aikin har zuwa yankin Ogba tare da banka mata wuta sannan aka kama direban. An ga ɗaliban sakandaren cikin fushi sun mamaye duka hanyoyin da ke…
Read More
‘Yan fashi sun babbake gomman matafiya a Sakkwato

‘Yan fashi sun babbake gomman matafiya a Sakkwato

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga jihar Sakkwato sun tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga da ake yi zargin 'yan fashin daji ne sun ƙona wasu matafiya a kan hanyarsu bayan da suka taso daga yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni. MANHAJA ta kalato cewa, mummunan al'amrin ya auku ne da misalin ƙarfe tara na safiyar jiya Talata a kusa da ƙauyen Gidan Bawa, wurin da aka ce 'yan fashin sun saba tare matafiya tare da ƙona abubuwan hawa. Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa kimanin mutum 17 suka…
Read More
Ɗan shekara 78 ya kashe ɗan shekara 95 kan abin duniya

Ɗan shekara 78 ya kashe ɗan shekara 95 kan abin duniya

Daga WAKILINMU Wani tsoho ɗan shekara 78 mai suna Moshood Habibu, ya shiga komar ’yan sanda bisa laifin halaka ɗan uwansa Salisu Surakatu mai shekaru 95 kan rikicin fili a jihar Ogun. Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ta bayyana hakan a jawabin da ta saki ranar cikin makon nan. Ta bayyana cewa, Moshood ya sara wa yayansa adda har lahira ranar Laraba a Mowe, ƙaramar hukumar Obafemi Owode. Ta ce, “an damƙe shi ne bisa ƙarar da wani Aminu Tajudeen ya shigar ofishin ’yan sandan Mowe cewa, Salisu Surukatu, wanda aka kashe mahaifinsa kuma wanda ya kashe ya…
Read More
Mawallafin jaridun Manhaja da Blueprint, Mohammed Idris Malagi, ya yi alhinin rasuwar Janar Wushishi

Mawallafin jaridun Manhaja da Blueprint, Mohammed Idris Malagi, ya yi alhinin rasuwar Janar Wushishi

Daga WAKILINMU Shugaban kamfanin buga jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya miƙa saƙon ta'aziyya ga ɗaukacin 'yan Nijeriya dangane da rasuwar tsohon Hafsan Hafsoshin Soja, Janar Mohammed Inuwa Wushishi. Alhaji Mohammed, wanda shi ne Kakakin Nupe, ya miƙa saƙon ta'aziyyar tasa musamman ga Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani-Bello, da ɗaukacin al'ummar Wushishi, Masarautar Kwantagora, jama'ar jihar, da Rundunar Sojojin Nijeriya a kan rasuwar ta Janar Wushishi, wanda ya riƙe muƙamin Hafsan Hafsoshin Sojan Nijeriya a tsakanin Oktoba 1981 zuwa Oktoba 1983. A saƙon ta'aziyyar da ya aika a ranar Lahadi, Alhaji Mohammed Malagi ya bayyana mamacin a matsayin…
Read More
Yadda yara 8 suka mutu cikin tsohuwar mota a Legas

Yadda yara 8 suka mutu cikin tsohuwar mota a Legas

Daga BASHIR ISAH A Lahadin da ta gabata rundunar 'yan sandan jihar Legas ta tabbatar da mutuwar wasu yara su takwas waɗanda cikin kuskure suka kulle kansu cikin wata tsohuwar mota da ke ajiye a gefe a lokacin da suke wasa a kan hanyar Adelayo, Agunlayo, Jah Michael, kusa da yankin Magbon a Badagry. Sanarwar da mai magana da yawun 'yan sandan jihar Legas, Adekunle Ajisebutu ya fitar, ta nuna ibtila'in ya auku ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata. Ajisebutu ya bayyana cewa, bayan da aka gano gawarwakin yaran an kwashe su zuwa ɗakin adana gawarwaki na Babban…
Read More
Buhari ya nuna alhininsa kan rasuwar Janar Wushishi

Buhari ya nuna alhininsa kan rasuwar Janar Wushishi

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya shiga cikin jerin 'yan ƙasa da ke ci gaba da nuna alhininsu dangane da rasuwar tsohon Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya, Janar Mohammed Inuwa Wushishi, tare da bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya. Buhari ya ce gudunmawar da marigayin ya bayar ga cigaban ƙasa a halin rayuwarsu abu ne mara misaltuwa. Sanarwar da ta fito ta hannu mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu a jiya Lahadi, ta nuna Buhari ya ce, “Janar Wushishi ya yi aiki mai tsafta a matsyinsa na soja kuma muna alfahari da…
Read More
Amarya a Zamfara ta nemi saki mako guda da tarewarta saboda girman mazakutar mijinta

Amarya a Zamfara ta nemi saki mako guda da tarewarta saboda girman mazakutar mijinta

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wata mata mai suna Aisha Dannupuwa da ta yi aure mako ɗaya da ya gabata a Jihar Zamfara, ta roƙi kotun shari’ar Musulunci da ta raba aurenta. Matar da ke zaune a yankin Samaru cikin ƙaramar hukumar Gusau ta jihar ta ce, dalilin da ya sa ta buƙaci a raba auren na ta shi ne saboda girman mazakutar mijinta. Da ta ke ba da labarin abin da ya faru, ta bayyana cewa, jima'i da mijinta a daren aurensu na farko ya yi matuƙar tada ma ta da hankali. Aisha Dannupuwa, ta ce, “lokacin da ya…
Read More
Nijeriya za ta ƙaddamar da shirin zaman kotu na zamani ‘Virtual’ – Malami

Nijeriya za ta ƙaddamar da shirin zaman kotu na zamani ‘Virtual’ – Malami

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya bayyana cewa, an shirya tsaf don ƙaddamar da shirin shari’o’in kotun ƙoli na zamani ‘Virtual’ a cibiyoyin gyaran hali na Nijeriya. Malami ya bayyana haka ne a wata sanarwa da Dakta Umar Gwandu, mataimakinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ya fitar ranar Juma’a a Abuja.Ya ce, shirin zai fara aiki ne daga cibiyar gyaran hali na Kuje da ke Abuja a ranar 6 ga watan Disamba. “Waɗanda ake sa ran a wajen taron sun haɗa da Ministan Harkokin Cikin Gida,…
Read More
Harin ISWAP a Maiduguri ya yi sanadiyar jin raunin yarinya ‘yar watanni

Harin ISWAP a Maiduguri ya yi sanadiyar jin raunin yarinya ‘yar watanni

Daga AISHA ASAS Rundunar 'yan sanda ta Jihar Barno ta tabbatar da jin raunin yarinya 'yar watanni shida da haihuwa a sanadiyar harin da ƙungiyar 'yan ta'adda ta ISWAP ta kai a Maiduguri ta hanyar jefo bama-bamai har biyar. Kwamishinan 'yan sanda Abdul Umar, ya sheda wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN cewar, maharan sun harbo bama-bamai ne daga wajen filin jirgin sama na Ngomari, wanda ke bayan jami'ar Barno. Ya ƙara da cewa, harin na su ya sauka a wurare ma-banbanta, hakan ne ya sa ba a samu hasarar rayuka ko kuma manyan raunuka ba. Kwamishinan ya ce,…
Read More