Labarai

Sanata Yahaya ya raba kaya a makarantun sakandare a mazaɓarsa

Sanata Yahaya ya raba kaya a makarantun sakandare a mazaɓarsa

Daga JAMIL GULMA a Kebbi A cikin shirinsa na tallafa wa ɓangaren ilmi, Sanata mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa kuma shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi Mallamawan Kabi ya raba kaya a makarantun sakandare huɗu da ke mazabarsa da suka haɗa da makarantar maza ta Kanta Unity College Argungu da makarantun mata na Augie, Argungu da kuma Ɗakingari. Kayan dai sun haɗa da katifu 396, zannuwan gado 396 da filallu 396, inda kowace makaranta ta samu 99 daga cikin kayan, sauran sun haɗa da manyan tukwanen girki 60 cokula farantin cin abinci dozin ashirin-ashirin,…
Read More
FOMWAN ta buƙaci reshenta na Bauchi ya kafa manyan makarantu

FOMWAN ta buƙaci reshenta na Bauchi ya kafa manyan makarantu

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Ƙungiyar Mata Musulmi Ta Nijeriya (FOMWAN) ta buƙaci reshen ta na jihar Bauchi ya kakkafa manyan makarantun koyar da ilimi a cikin jiha domin bunƙasa cigaban ilimin mata da matasa. Kamar yadda Amirar ƙungiyar ta ƙasa, Rafi’at Idowu Sanni ta ce, ire-iren waɗannan manyan makarantu kamar Jami’ar Koyon Haɗa Magunguna ko Kwalejin FOMWAN kan likitancin ungozomanci (HealthTechnology) da Cibiyar fasahar Sadarwa (ICT), da makamantansu. Amira ta qasa ta ƙungiyar FOMWAN tana jawabi ne a yayin buɗe gangami akan ilimi na kwanaki biyu da reshen qungiyar na jihar Bauchi ta shirya mai taken “Cimma Muradun…
Read More
Kwastam sun kama tabar wiwi ta kimanin Naira miliyan 18 a Katsina

Kwastam sun kama tabar wiwi ta kimanin Naira miliyan 18 a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Hukumar Kwastam reshen jihar Katsina ta kama tabar wiwi wadda kuɗinta ya kai Naira miliyan sha takwas da dubu ɗari ɗaya a watan da ya gabata na Nuwamba. Muƙaddashin Shugaban hukumar reshen jihar Katsina, Ɗalhatu Wada Chedi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da hukumar ta kira don sanar da jama'a nasarar da ta samu a yaqi da hana shigowa da haramtattun kayayyaki a Nijeriya. Wada Chedi ya bayyana cewar an kama wasu mutane biyu ne ɗauke da tabar ta wiwi ƙunshi 230 a lokacin da suke ƙoƙarin shigowa da ita cikin…
Read More
Najeriya za ta fuskanci matsalar ƙarancin ruwan sha – Bincike

Najeriya za ta fuskanci matsalar ƙarancin ruwan sha – Bincike

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Najeriya na fuskantar ƙarancin ruwan sha, wanda hakan ya biyo bayan bincike da masana a harkar ruwa suka gabatar. Kamar yadda binciken ya nuna matuqar gwamnatocin ba su ɗauki mataki kan matsalar ba jama'a za su fuskantar ƙalubale mai tarin yawa ta fuskar samun ruwan sha. Waɗannan bayanai sun fito ne a wani taron kwanaki uku da hukumar samar da ruwan sha ta ƙasa ta shirya a jahar Jigawa da nufin samar da bakin zaren. Wani masani akan harkar ruwan sha, Ambasada Rabiu Dagari wadda shine Babban Darakta a Hukumar hulɗa da ƙasashen waje,…
Read More
Korona nau’in Omicron: Birtaniya ta hana ‘yan Nijeriya shiga ƙasarta

Korona nau’in Omicron: Birtaniya ta hana ‘yan Nijeriya shiga ƙasarta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ci gaba da ɗaukar matakan kariya da take yi, gwamnatin ƙasar Birtaniya ta sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ta ware domin ɗaukar ƙarin matakai a kan 'yan ƙasashensu wajen shiga Birtaniyar, saboda mutane 21 da aka samu ɗauke da sabon nau'in cutar Korona omicron a Ingila, waɗanda suka je can daga Nijeriyar. Matakin ya ƙunshi hana 'yan Nijeriyar da ma sauran mutane daga ƙasar waɗanda ba su da fasfo na Birtaniya ko izinin zama a can zuwa. Wata sanarwa da hukumomin Birtaniyar suka fitar ta ce daga ƙarfe huɗu na asuba agogon…
Read More
Hakimin da ya shekara 68 yana mulki ya rasu a Kano

Hakimin da ya shekara 68 yana mulki ya rasu a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Allah ya yi wa Sarkin Ban Kano Alh. Dr. Mukhtar Adnan rasuwa a daren jiya juma'a, Marigayin ya rasu yana da shekara 95 a duniya, Babban ɗansa Baba Ado ya shaida wa manema labarai cewa mahaifin nasa ya rasu ne dab da asubahin ranar Juma'a a sibitin UMC Zahir da ke unguwar Jan Bulo inda ya yi jinya. An yi jana'izarsa bayan Sallar Juma'a a babban masallacin garin Ɗanbatta, da ke jihar Kano. Marigayi Alhaji Mukhtar Adnan yana daga cikin masu zaɓen Sarkin Kano, wanda kuma shi kaɗai ne ya kafa tarihi, inda ya zaɓi…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: Ɗaya daga cikin malaman da suka yi muƙabala da Sheikh Abduljabbar Kabara ya rasu

Da ɗumi-ɗumi: Ɗaya daga cikin malaman da suka yi muƙabala da Sheikh Abduljabbar Kabara ya rasu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Guda daga cikin malaman da suka yi muƙabala da Malam Abduljabbar Kabara, Malam Mas’ud Mas’ud Hotoro ya rasu. Rahotanni da MANHAJA ta samu sun nuna cewa Malam Mas’ud ya rasu ne a daren ranar Larabar da ta gabata sakamakon haɗarin mota da ya auku a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya Idan za a iya tunawa dai malamin na ɗaya daga cikin mutum huɗun da suka yi muƙabala da Sheikh Abduljabbar Kabara a kwanakin baya. Kazalika, Malamin shi ne wanda ya wakilci ɓangaren Ƙadiriyya yayin zaman muƙabalar. Rahotannin sun bayyana cewa an yi wa Malamin jana’aiza…
Read More
Gwamnatin Legas ta yi watsi da rahoton kashe masu zanga-zangar EndSARS tara a Lekki

Gwamnatin Legas ta yi watsi da rahoton kashe masu zanga-zangar EndSARS tara a Lekki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin jihar Legas ta fitar da farar takardarta kan rahoton da kwamitin bincike kan zanga-zangar EndSARS ya gabatar ma ta wanda ya binciki lamarin da ya faru a ƙofar Lekki a ranar 20 ga Oktoba, 2020. Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, a safiyar ranar Talata yayin ganawa da manema labarai, ya yi alƙawarin cewa za a fitar da farar takarda a ranar Talata. Sai dai gwamnan ya yi watsi da rahoton kwamitin na cewa mutum tara kawai aka kashe a ƙofar karɓar haraji lokacin da sojoji da ‘yan sanda suka harbe masu zanga-zangar lumana. Sanwo-Olu ya bayyana…
Read More
Jami’an tsaro sun hana ma’aikatan da ba a yi musu allurar rigakafi ba shiga sakatariyar Gwamnatin Tarayya a Abuja

Jami’an tsaro sun hana ma’aikatan da ba a yi musu allurar rigakafi ba shiga sakatariyar Gwamnatin Tarayya a Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A halin yanzu an hana ma'aikatan gwamnati da sauran jama'ar da ba su da shaidar allurar rigakafin Korona na PCR daga shiga rukunin ginin gwamnati a Abuja. Sai dai ƙungiyar manyan ma’aikatan Nijeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta tsawaita wa’adin dokar hana ma’aikatan da ba su yi wa allurar rigakafi ba zuwa watan Maris na shekara mai zuwa, daga wa’adin yau na yin allurar dole ga ma’aikatan, matakin da Boss Mustapha ya jagoranta a fadar shugaban ƙasa wanda kwamitin gudanarwa ya bayyana a matsayin abin da ba zai yiwu ba. Nijeriya a ranar Laraba kuma…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: ‘Yan sandan Kano sun garƙame ofishin lauyan Shekarau bayan kayar da Ganduje a kotu

Da ɗumi-ɗumi: ‘Yan sandan Kano sun garƙame ofishin lauyan Shekarau bayan kayar da Ganduje a kotu

Daga WAKILINMU Rahotanni daga jihar Kano sun nuna cewa, jami'an Ma'aikatar Filaye ta Jihar tare da haɗin gwiwar 'yan sanda sun garƙame ofishin lauyan Sanata Shekarau, Nureini Jimoh, SAN, da ke lamba 16c kan titin Murtala Mohammed. A Talatar da ta gabata lauya Jimoh ya wakilici ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau na APC inda suka samu nasara a kan ɓangaren Gwamna Abdullahi Ganduje. Lauyan Shakarau ya tabbatar wa jaridar Daily Nigerian da batun garƙame ofishin nasa, yana mai cewa shi da ma'aikatansa da sauran jama'ar da ke ginin lamarin ya shafa. "Maganar da nake yi, yanzu haka ina cikin ginin ne…
Read More