Labarai

Hatsarin kwale-kwale ya yi sanadin mutuwar mutum 40 a Kano

Hatsarin kwale-kwale ya yi sanadin mutuwar mutum 40 a Kano

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Aƙalla mutane 40 wanda akasari mata da yara ne aka ruwaito sun rasa rayukansu a qauyen Badau da ke qaramar hukumar Bagwai a jihar Kano sakamakon wani hatsarin kwale-kwale. Wani wanda abun ya faru a gaban idonsa wanda kuma ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce, hatsarin ya faru ne a ranar Talata da misalin ƙarfe 6 na yamma. Ya bayyana cewa, kwale-kwalen ya kife ne a tsakiyar kogin yayin da yake jigilar fasinjoji zuwa garin Bagwai daga ƙauyen Badau. Waɗanda lamarin ya rutsa da su sun mutu ne a cikin kogin saboda ba za su…
Read More
Kotu ga Gwamna Ganduje: Sai ka biya Sanusi Naira miliyan 10 bisa fatattakar sa daga Kano

Kotu ga Gwamna Ganduje: Sai ka biya Sanusi Naira miliyan 10 bisa fatattakar sa daga Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata da ta gabata, ta bayyana cewa korar Sarkin Kano na 14, Malam Muhammadu Sanusi II, ko zuwa Jihar Nassarawa bayan an tsige shi daga sarautar Kano ya saɓa wa dokar ƙasa. Alƙalin kotun, Anwuli Chikere, a hukuncin da ya yi , ya bayyana cewa dokar kafa Masarautar Kano ta 2019 da gwamnatin jiha ta kafa ta kuma yi amfani da ita wajen korar Sarki Sanusi bayan ta tsige shi ta saɓa wa kundin tsarin mulki na 1999. Ya ce kundin tsarin mulkin ƙasar…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: Sojoji sun daƙile yinƙurin hare-haren ISWAP

Da ɗumi-ɗumi: Sojoji sun daƙile yinƙurin hare-haren ISWAP

Sojojin Nijeriya na ƙasa da sama sun yi nasarar daƙile yinƙurin kai harin mayaƙan ISWAP da suka mamaye yankin Buni Yadi a jihar Yobe Duk da nasarar da sojojin suka samu a kan mayaƙan na ISWAP, tun farko sai da mayaƙan suka banka wa wani ofishin 'yan sanda wuta kafin daga bisani sojoji suka katse musu hanzari. Bayanan sojojin sun nuna mayaƙan sun tsere don neman mafaka sakamakon luguden wutar da suka sha a wajen sojojon. An ce an ga jiragen yaƙin sojojin sama ƙirar Super Tucano na shawagi a yankin tabkin Chadi tare da yin luguden wuta a kan…
Read More
Zargin ɓata suna: Ɗan jarida ya maka jaridar Daily Trust, Gwamnatin Nasarawa da Yakubu Lamai a kotu

Zargin ɓata suna: Ɗan jarida ya maka jaridar Daily Trust, Gwamnatin Nasarawa da Yakubu Lamai a kotu

Daga WAKILINMU Tsohon ma'aikacin jaridar Daily Trust ya maka Daraktan Yaɗa Labarai ga Gwamnan Jihar Nasarawa, Mr. Yakubu Lamai, da jaridar Daily Trust da kuma Gwamnatin Jihar Nasarawa a gaban kuliya bisa zargin ɓata masa suna. Ibraheem Hamza Muhammad wanda tsohon wakilin jaridar Daily Trust ne a jihar Nasarawa, ya maka waɗanda yake zargin da ɓata masa suna a kotu ne ta hannun lauyansa, Barrister M. A. Danmama. Yayin zaman farko na sauraron shari'ar a Babbar Kotun Jihar Nasarawa mai zamanta a New Karu a ranar Talata, mai ƙarar ya yi iƙirarin cewa ya haɗa wani labari bayan kammala bincikensa…
Read More
Yadda ƙungiyoyin manoma suka tafka asarar kayan amfanin gona

Yadda ƙungiyoyin manoma suka tafka asarar kayan amfanin gona

Daga MUHAMMADU MUJITABA Ƙungiyoyin Manoman shekafa, dawa, masara da sauransu sun tafka sarar kayan amfanin gona mai ɗumbin yawa na billiyon naira da ba a tantance yawansa ba a wannan shekara sakamakon ƙarancin ruwa da aka samu a wasu wuraren na jihohin arewacin Nijiriya, wanda suka bayyana wa duniya domin dai sanar da hukumomin da sauran masu ruwa da tsaki domin ɗaukar mataki kamar yadda ya dace. Alhaji Samaila Abdullahi Wali shi ne shugaban masu sayar da kayan amfanin gona na zamani kuma ɗaya daga cikin ’yan ƙungiyar manoma da safarar kayan gona, ya ce, babu shakka a bana manoma…
Read More
Matafiya sun fusata sakamakon tsadar tikitin jirgin ƙasar Kaduna zuwa Abuja

Matafiya sun fusata sakamakon tsadar tikitin jirgin ƙasar Kaduna zuwa Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A safiyar yau talata ne aka ga fasinjoji a tashar jiragen ƙasa na Kaduna da ke Rigasa sun harziƙa kan yadda wasu mutane da ake zargin ba ma’aikatan Hukumar Jirgin Ƙasar ba ne na saran tikiti tare da sayarwa da tsada har sama da naira dubu goma. Wannan lamarin dai ya tilasta wa fasinjoji suka riqa sayen tikitin a kan farashin dubu goma wanda ya yi tsada ga talakawa a hannun ’yan kasuwar bayan-fage da ba a iya tantance ko su wane ne ba, kamar yadda wakilin Manhaja ya shaida. Tun a watan Janairu ne hukumar…
Read More
Yadda fursunoni 252 suka tsere daga kurkukun Jos bayan kai hari

Yadda fursunoni 252 suka tsere daga kurkukun Jos bayan kai hari

Daga HABU ƊAN SARKI Biyo bayan wani mummunan hari da wasu mahara da har yanzu ba a tantance ko su wanene ba, suka kai babban gidan yarin Jos, dake ƙarƙashin Hukumar Kula da Gidajen Gyara Halinka ta Nijeriya, a ranar Lahadi da ta gabata 27 ga watan Nuwamba, an tabbatar da tserewar fursunoni 252, ciki har da waɗanda ake zaton an kai harin ne domin su. Babban Kwantirola mai kula da Cibiyar Gyara Halinka ta Jos, Samuel Aguda ya tabbatar da ɗan bindiga ɗaya ne daga cikin maharan da suka kai farmakin da muggan makamai aka kashe a cikin kurkukun…
Read More
‘Yan sanda sun bindige gawurtaccen ɗan bindiga, Yellow Magaji a otel

‘Yan sanda sun bindige gawurtaccen ɗan bindiga, Yellow Magaji a otel

Daga BASHIR ISAH Bayanan 'yan sandan jihar Kaduna sun nuna 'yan sandan jihar sun samu nasarar sheƙe gawurtaccen ɗan bindigar nan Yellow Magaji da ya addabi babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna. Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, ya faɗa a ranar Asabar cewa, an kashe Yellow Magaji ne a ranar 24 ga Nuwamban 2021. A cewarsa, sakamakon bayanan sirri da suka samu ne ya sanya 'yan sandan Kaduna tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro na musamman na tarayya bisa unarnin Kwamishinan 'Yan sanda CP Mudassiru Abdullahi suka yi dirar mikiya a masaukin baƙi…
Read More
An rutsa mahara a cikin kurkukun Jos

An rutsa mahara a cikin kurkukun Jos

Daga BASHIR ISAH A yammacin jiya Lahadi 'yan bindiga suka kai hari gidan yarin garin Jos a Jihar Filato inda aka ce 'yan bindigar sun maƙale a cikin gidan yarin sun rasa mafita sakamakon ƙawanyar da jami'an tsaro suka yi musu. Mai magana da yawun hukumar kula da gidajen yari na ƙasa, CC Francis Enobore, shi ne ya bayyana haka a Abuja ran Lahadi da daddare. Sanarwar da ta fito ta hannunsa ta ce, "Gungun 'yan bindiga sun kai wa gidan gyaran hali na Jos, jihar Filato hari ɗauke da muggan makamai. "An ce maharan sun dira gidan yarin ne…
Read More
Rasuwar Sani Buhari Daura babban rashi ne ga Nijeriya – Shugaba Buhari

Rasuwar Sani Buhari Daura babban rashi ne ga Nijeriya – Shugaba Buhari

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana rasuwar hamshaƙin ɗan kasuwar nan mazaunin Kano, Alhaji Sani Buhari Daura, a matsayin babban rashi ba ga jihar Katsina da Kano kaɗai ba, amma ga ƙasa bakiɗaya musamman ma idan aka yi la'akari da irin tasirin da yake da shi ga tattalin arzikin ƙasa. Buhari ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta sami sa hannun mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu a ranar Lahadi. Yana mai bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin daɗaɗɗun jiga-jigan 'yan kasuwa a Nijeriya waɗanda suka bada gudunmawarsu gaya wajen cigaban tattalin arzikim…
Read More