Labarai

Iyalan Marigayi Baba A.T sun roƙi gwamnatin Kebbi ta biya bashin kwangilar da ake bin sa

Iyalan Marigayi Baba A.T sun roƙi gwamnatin Kebbi ta biya bashin kwangilar da ake bin sa

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Iyalan Marigayi Malam Aliyu S. Abubakar Tunga (Baba A.T.) sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kebbi da ta biya kuɗaɗen kwangilar da ake bin marigayin domin su samu damar biyan bashin da ya bari. Da yake zantawa da wakilin Blueprint Manhaja a ranar Litinin, Malam Aminu Aliyu Abubakar Tunga, wanda ya yi magana a madadin iyalan marigayin, ya bayyana cewa shekaru shida kenan da rasuwar mahaifinsu, amma har yanzu ba su samu damar biyan bashin da ya bari ba saboda gwamnatin jihar ba ta biya kuɗaɗen kwangilar da ake binsa ba. A cewarsa, marigayin na…
Read More
Yadda lauyan bogi ya karɓi N7.5m daga hannun kwastoma a Legas – EFCC 

Yadda lauyan bogi ya karɓi N7.5m daga hannun kwastoma a Legas – EFCC 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar kotun Jihar Legas da ke zamanta a Ikeja ta samu wani mutum mai shekara 55, John Nwawuto Anoruo, da laifin yin ƙaryar cewa shi lauya ne da kuma amfani da hatimin bogi na ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA), inda ta yanke masa hukuncin tara. Mai shari’a A.M. Lawal ya yanke hukuncin ne bayan Anoruo ya amsa laifuka biyu da suka haɗa da amfani da hatimin NBA na bogi da kuma yin ƙarya cewa shi ƙwararren lauya ne. Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kama Anoruo a ranar 20 ga Afrilu, 2026.…
Read More
Malamin da ke takara ya fi wanda ke yi wa ‘yan siyasa addu’a – Gumi

Malamin da ke takara ya fi wanda ke yi wa ‘yan siyasa addu’a – Gumi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya ce malamai da ke shiga siyasa domin kawo gyara sun fi waɗanda ke takaita kansu ga yi wa ‘yan siyasa addu’a ba tare da shiga cikin tsarin mulki ba. Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan rawar da ya kamata malaman addini su taka a siyasa, musamman bayan yadda wasu fitattun malaman Musulunci suka shiga harkokin gwamnati da siyasa. A cewarsa, idan malami yana da niyyar tabbatar da adalci da kyakkyawan shugabanci, shiga siyasa ba laifi ba ne.…
Read More
Mataimakin Gwamna ya buɗe ofishin ‘yan sanda da ƙaramar hukumar Katsina ta gina

Mataimakin Gwamna ya buɗe ofishin ‘yan sanda da ƙaramar hukumar Katsina ta gina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Hon. Faruk Lawal Joɓe, ya ƙaddamar da buɗe ofishin ’yan sanda (Outpost) na wucin gadi da shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude , ya gina a Unguwar Kofar Sauri, cikin mazaɓar Wakilin Gabas I da ke ƙaramar hukumar Katsina, wanda ƙaramar hukumar Katsina ta gina domin ƙara inganta harkokin tsaro a faɗin ƙaramar hukumar. A jawabinsa, Mataimakin Gwamnan Jihar, ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad, bisa wannan aiki da ya gudanar, wanda ya ƙara tabbatar wa al’umma cewa Gwamnatin Jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin Gwamna…
Read More
Nijeriya ta samu tiriliyan N24.02 daga ɗanyen mai a wata shida

Nijeriya ta samu tiriliyan N24.02 daga ɗanyen mai a wata shida

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Nijeriya ta samu kimanin Naira tiriliyan 24.02 daga fitar da ɗanyen mai zuwa ƙasashen waje a watanni shida na farkon shekarar 2026, bayan da ta fitar da ganga miliyan 182.2 na ɗanyen mai.  Hakan ya samu ne sakamakon tashin farashin mai a kasuwannin duniya, duk da ci gaba da nuna damuwa kan wadatar ɗanyen mai ga matatun cikin gida. Binciken alƙaluman samar da ɗanyen mai da fitar da shi tsakanin watan Janairu zuwa Yuni ya nuna cewa darajar gangunan man da aka fitar ta kai kusan dala biliyan 17.6, bisa canjin kuɗi na Naira 1,365 kan…
Read More
Tinubu ya bai wa masana’antu fifiko wajen sauya tattalin arzikin Nijeriya – Idris

Tinubu ya bai wa masana’antu fifiko wajen sauya tattalin arzikin Nijeriya – Idris

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama'a na Nijeriya, Alhaji Mohammed Idris, ya ce, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta mayar da bunƙasa masana'antu, fasaha da bai wa matasa dama a matsayin ginshiƙan sauya tattalin arzikin Nijeriya ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda. Ministan ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin ƙaddamar da rangadin tawagar yaɗa labarai ta Fadar Shugaban ƙasa zuwa hedikwatar Hukumar Kula da Kimiyya da Injiniyan Kere-kere ta ƙasa (NASENI) da ke Abuja. Idris ya ce manufofin gwamnatin Tinubu na samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari, bunƙasa kasuwanci…
Read More
Nijeriya ta tura sojoji 86 aikin wanzar da zaman lafiya a Guinea-Bissau

Nijeriya ta tura sojoji 86 aikin wanzar da zaman lafiya a Guinea-Bissau

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar Sojin Nijeriya ta tura jami'ai 86 zuwa ƙasar Guinea-Bissau domin shiga aikin wanzar da zaman lafiya na ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS). A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce matakin ya nuna ci gaba da jajircewar Nijeriya wajen tallafa wa zaman lafiya da tsaro a yankin Afirka ta Yamma, inji sanarwar. Sanarwar ta ce jami'an sun tashi daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, kuma sun isa Guinea-Bissau lafiya domin fara aikinsu ƙarƙashin umarnin ECOWAS, inji sanarwar. Rundunar ta bayyana cewa Nijeriya na ci gaba…
Read More
Majalisar Dokokin Kano ta amince da hana makarantu ƙara kuɗin makaranta barkatai

Majalisar Dokokin Kano ta amince da hana makarantu ƙara kuɗin makaranta barkatai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da wani ƙudiri da zai hana makarantu masu zaman kansu ƙara kuɗin makaranta ba tare da samun amincewar hukuma ba, domin kare iyaye da masu kula da yara daga ƙarin kuɗaɗe barkatai. ƙudirin gyaran Dokar Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai ta shekarar 2026 ya tanadi cewa duk makarantar da ke son ƙara kuɗin makaranta dole ne ta fara neman sahalewar hukumar da abin ya shafa. Rahotanni sun nuna cewa duk wani ƙarin kuɗin makaranta da ya haura kashi 10 cikin 100 zai buƙaci…
Read More
Tinubu ya jinjina wa tawagar Nijeriya bayan lashe lambobin yabo 24 a gasar Commonwealth

Tinubu ya jinjina wa tawagar Nijeriya bayan lashe lambobin yabo 24 a gasar Commonwealth

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya tawagar Nijeriya murnar bajintar da ta nuna a Gasar Commonwealth da aka gudanar a birnin Glasgow na ƙasar Scotland, bayan da ta lashe jimillar lambobin yabo 24. Tawagar Nijeriya ta samu lambobin zinariya 10, azurfa bakwai da tagulla bakwai, lamarin da ya sanya ƙasar cikin waɗanda suka yi fice a gasar. A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, shugaban ya yaba wa ’yan wasan saboda jajircewa, ƙwazo da kuma nuna ruhin kishin ƙasa…
Read More
An kama mutum 48 kan zargin ta’addanci a Zamfara

An kama mutum 48 kan zargin ta’addanci a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta sanar da kama mutum 48 da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci bayan wani samame na haɗin gwiwa da jami’an tsaro suka gudanar a sassa daban-daban na birnin Gusau. Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce samamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka nuna wuraren da ake zargin maɓoyar ’yan ta’adda ne. Ya ce cikin waɗanda aka kama har da mata, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano irin rawar da kowannensu ya taka, inji shi. Ya ƙara da cewa jami’an tsaro…
Read More