08
Aug
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce gwamnatin birnin ta kammala shirye-shiryen sake fasalin ayyukan babura da adaidaita sahu (Keke Napep) a Abuja, domin magance matsalolin tsaro da kuma inganta doka da oda. Wike ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin ganawarsa ta wata-wata da manema labarai a Abuja. Ya ce ayyukan babura da adaidaita sahu sun zama barazana ga tsaro a babban birnin tarayya, saboda haka ya zama dole a taƙaita zirga-zirgarsu zuwa wuraren da gwamnati za ta ware musu. Ministan ya bayyana ayyukansu a matsayin abin da ke kawo cikas…
