Labarai

Zaɓen Osun: Davido da tsohon hadimin Buhari sun yi musayar yawu a kafar sadarwa ta zamani

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fitaccen mawakin Nijeriya, David Adeleke da aka fisani da Davido da tsohon hadimin marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan lamuran kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad, sun tayar da hazo a Soshiyal Mediya inda suka yi musayar kalamai masu zafi a shafin X. Wannan al'amari ya janyo hankalin jama’a musamman ganin yadda ba a saba ganin irin haka ba tsakanin mawaƙi ɗan kudu da ɗan siyasa daga arewacin Nijeriya. Al'amarin ya samo asali ne a lokacin da aka ruwaito Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, ta sanya wa asusun gwamnatin Jihar…
Read More

Zamfara: Gwamna Lawal ya je Bunguɗu ta’aziyyar harin ‘yan bindiga cikin aniyarsa ta yaƙi da ta’addanci

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake nanata cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa shiga tattaunawa ko yin sulhu da 'yan bindiga da sauran masu aikata laifuka ba, yana mai jaddada cewa za ta ci gaba da ɗaukar duk matakan da suka dace domin murƙushe matsalar rashin tsaro a jihar. A ranar Alhamis, gwamnan ya kai ziyarar jaje Ƙaramar Hukumar Bungudu, domin ta'aziyya ga iyalan waɗanda harin 'yan bindiga ya shafa, da Masarautar Bungudu, da kuma al'ummar yankin baki ɗaya. Wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce, ziyarar ta fara…
Read More

‘Yan bindiga sun tsere sun bar dabbobi 452 da suka sace bayan musayar wuta da sojoji a Sakkwato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaro a Jihar Sakkwato sun yi nasarar daƙile wasu hare-hare biyu a ƙananan hukumomin Shagari da Rabah, lamarin da ya tilasta wa maharan sakin wasu dabbobi guda 452 da suka sace bayan musayar wuta da haɗakar tawagar jami'an tsaro. An gudanar da atisayen ne a daren Talata wayewar Laraba, wanda ya yi sanadiyyar ƙwato ɗaruruwan dabbobi da aka sace bayan 'yan bindigar sun tsere zuwa bayan gari. Jami'in Hulɗa da Jama’ar rundunar 'yan sandan jihar, DSP Ahmad Rufa'i ne ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis. A…
Read More
Kwamishinan Gombe ya ƙaddamar da sabon tsarin sa ido kan ƙananan hukumomi

Kwamishinan Gombe ya ƙaddamar da sabon tsarin sa ido kan ƙananan hukumomi

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Kwamishinan ma'aikatar ƙananan hukumomi da raya al’umma ta Jihar Gombe, Barrista Sani Ahmed Haruna, ya ƙaddamar da wani sabon tsari na sa ido kan ayyukan ƙananan hukumomi, inda ya umarci sashen bincike, saka Ido da tantance ayyuka na ma’aikatar da ya riƙa gabatar da rahotannin bincike a duk wata. Ya bayyana cewa matakin na da nufin ƙarfafa sa ido kan yadda ƙananan hukumomi ke gudanar da ayyukansu, bunƙasa gaskiya da riƙon amana, tare da inganta isar da ayyukan gwamnati ga al’umma. Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin taronsa na farko da ma’aikatan sashen, inda ya…
Read More

Tiriliyan N1.16 tallafin fetur ya lanƙwame a 2021 – Hukumar RMAFC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Alhamis Shugaban Hukumar kula da Lamuran Tattara Kuɗaɗen shiga, Rabawa da Kasafi (RMAFC), Dakta Mohammed Bello Shehu ya ce Nijeriya ta kashe jimillar Naira tiriliyan 1.16 a tallafin fetur a shekarar 2021, kamar yadda aka zaftare tiriliyan N1.20 daga kuɗaɗen da aka samu sakamakon siyar da ɗanyen mai. Bello Shehu ya bayyana haka ne a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Al'umma (SPAC), wanda aka ɗora wa alhakin bincike kan rahotannin kuɗaɗen masana'antar mai da gas da Shirin Masana'antun Fitarwa Na Nijeriya (NEITI) ya gudanar. Ya ce, baya ga tallafin fetur, an…
Read More
Yadda Salah ya samu gagarumar tarba a Trabzonspor

Yadda Salah ya samu gagarumar tarba a Trabzonspor

ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Trabzonspor ta Turkiyya za ta tabbatar da sayen Mohamed Salah yayin da magoya bayanta suka yi masa tarba ta karamci a lokacin da ya isa Turkiyya. ɗaruruwan magoya baya sun taru a wajen filin jirgin saman Ataturk da ke Istanbul ranar Laraba yayin da Salah ya fito sanye da kaya masu launukan Trabzonspor. ɗan wasan gaban mai shekarA 34 ya bar Liverpool a ƙarshen kakar wasa da ta gabata bayan shekara tara a Merseyside, inda ya zura ƙwallaye 257. Ba a tabbatar da albashin da Salah zai samu a Trabzonspor ba, amma tunda shi ɗan wasa…
Read More
 ‘Yan bindiga sun sake kai sabon hari a Sakkwato, ana fargabar an kashe mutane da dama

 ‘Yan bindiga sun sake kai sabon hari a Sakkwato, ana fargabar an kashe mutane da dama

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ana fargabar mutuwar mutane da dama tare da sace wasu 37 a sabbin hare-haren da 'yan bindiga suka kai a ƙananan hukumomin Kebbe, Sabon Birni da Shagari na Jihar Sakkwato, yayin da wani Mataimakin Sufeton 'Yan Sanda (ASP), Bala Wakili, ya rasa ransa a fafatawa da maharan. Rahotanni sun nuna cewa marigayi ASP Bala Wakili, wanda ke aiki da Rundunar 'Yan Sandan Kebbe, ya mutu ne ranar Litinin bayan wata arangama mai zafi tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindiga a yankin Kebbe. Majiyoyi sun ce maharan sun kai farmaki ƙauyukan Girkau da Zugu da…
Read More
Gwamnatin Kaduna ta bai wa mijin matar da aka ƙone da ranta gida, kuɗi da guraben karatun  yaransa

Gwamnatin Kaduna ta bai wa mijin matar da aka ƙone da ranta gida, kuɗi da guraben karatun  yaransa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kaduna ta bai wa Aliyu, mijin matar da ta mutu bayan wasu fusatattun mutane sun ƙone ta da ranta a Marabar Jos, kyautar gida, tallafin kuɗi da kuma guraben karatu kyauta ga iyalansa. Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ne ya miƙa mukullin gidan ga Aliyu a ranar Talata a Fadar Gwamnatin jihar, inda ya bayyana cewa gwamnati na da alhakin tallafa wa iyalan da suka faɗa cikin irin waɗannan munanan hare-hare. Tallafin ya biyo bayan mummunan lamarin da ya faru a Marabar Jos, inda wasu fusatattun mutane suka kashe matar Aliyu…
Read More
Sojoji sun ayyana shugaban ISWAP da mataimakinsa a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo

Sojoji sun ayyana shugaban ISWAP da mataimakinsa a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar Sojojin Nijeriya ta ayyana shugaban ƙungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP), Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa (Wali), da mataimakinsa, Amirul Jaish Muhammad Jidda, a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo, bayan bayanan sirri da aka samo daga na'urorin fasaha da aka ƙwato a hare-haren da aka kai kan ƙungiyar a yankin Tafkin Chadi. Muƙaddashin Jami'in Yaɗa Labarai na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai (OPHK), Kyaftin Muhammed Goni, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba. Ya ce an gano shugabannin ne bayan…
Read More
AIG Garba Ahmed ya yi wa Jami’ar KHAIRUN alƙawarin cikakken goyon bayan ‘yan sanda

AIG Garba Ahmed ya yi wa Jami’ar KHAIRUN alƙawarin cikakken goyon bayan ‘yan sanda

Daga RABIU SANUSI a Kano Mataimakin Sufeto Janar na 'Yan Sanda (AIG) mai kula da Shiyya ta Daya da ke Kano, Garba Ahmed, ya tabbatar wa Jami'ar Khalifa Isyaku Rabiu (KHAIRUN) da ci gaba da ba ta cikakken goyon baya domin tabbatar da ingantaccen tsaro da samar da yanayi mai kyau na koyarwa, koyo da ci gaban al'umma. AIG Ahmed ya bayyana hakan ne yayin da Mataimakin Shugaban Jami'ar, Farfesa Abdulrashid Garba, ya jagoranci tawagar jami'ar zuwa hedikwatar Shiyya ta Daya da ke Kano domin ziyarar girmamawa. A jawabinsa, Farfesa Abdulrashid Garba ya ce jami'ar na da kyakkyawar alaƙa da…
Read More