Babban Labari

Bikin sallah: ’Yan ta’adda na shirin tada bomabomai – DSS

Bikin sallah: ’Yan ta’adda na shirin tada bomabomai – DSS

•Za su kai hari a masallatai da wuraren shaƙatawa Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A daidai lokacin da ya rage kwana kaɗan al'ummar Musulmi su gudanar da shagulgulan bikin Ƙaramar Sallah a Nijeriya, Hukumar 'Yan Sandan Farin Kaya (DSS) ta ankarar da 'yan Nijeriya kan wani makirci da suka gano da wasu ɓatagari ke shirin aikatawa a lokacin bukukuwan sallah da bayan sallah. Hukumar DSS ɗin da kanta ta ce ta gano cewa, wasu miyagu suna haɗin gwiwa domin saka bama-bamai a wuraren ibada, wuraren shaƙatawa da wasu gine-gine masu muhimmanci yayin bikin sallah. Don haka hukumar ta buƙaci…
Read More
An sace wa hedikwatar APC Naira miliyan 43 na kuɗin fom ta taga

An sace wa hedikwatar APC Naira miliyan 43 na kuɗin fom ta taga

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Hedikwatar jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta faɗa cikin ruɗani a ranar Larabar da ta gabata yayin da wasu maƙudan kuɗaɗe har Naira miliyan 43 suka ɓace a harabar ofishin. Kuɗaɗen da ke cikin dala sun kai dalar Amurka 75,000 kuma ana tsammanin suna cikin kuɗaɗen da jam’iyyar ta tara a cigaba da sayar da fom ɗin zaɓen 2023. Rahotanni sun bayyana cewa, kwatsam aka tayar da rumfar da ake sayar da fom ɗin ba tare da wani bayani ba bayan an gano kuɗin sun vata. An tattaro cewa, kuɗaɗen da suka kai…
Read More
Aisha Buhari ta roƙi ’yan takarar Shugaban Ƙasa na APC su zaɓi mace a matsayin mataimakiya

Aisha Buhari ta roƙi ’yan takarar Shugaban Ƙasa na APC su zaɓi mace a matsayin mataimakiya

Daga AMINA YUSUF ALI A ƙarshen makon da ya gabata ne dai mai ɗakin Shugaban Ƙasar Nijeriya A'isha Buhari ta yi wani taron ganawa da masu zawarcin kujerar shugabancin ƙasar a zaɓen 2023.  A yayin taron ne A'isha ta isar da roƙon ta ga 'yan takarar shugabancin ƙasar nan gabaɗaya da su zaɓi mata a matsayin abokan takarar tasu. 'Ya takarar Su ne, Bola Ahmad Tinubu, sai mataimakin shugaban ƙasa mai ci a yanzu, Farfesa Yemi Osinbajo, sai Dakta Chris Ngige da sauransu.  Chris Ngige ya yi kira ga takwarorinsa 'yan takara da su yi biyayya ga abinda A'isha Buhari…
Read More
2023: Fitattun ’yan takarar da ke zawarcin Nijeriya

2023: Fitattun ’yan takarar da ke zawarcin Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Alamu sun nuna gangar siyasar 2023 ta fara zaƙi, inda masu sha'awar ganin sun gaji kujerar Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya a zaɓen mai ƙaratowa na 2023 sai ƙara wasa wuƙarsu irin ta siyasa suke yi ta fuskar kwarzanta kai da kuma tuntuɓar masu ruwa da tsaki a sha'anin siyasa. Blueprint Manhaja ta yi nazarin wasu fitattun 'yan takarar neman kujerar Shugaban Ƙasar Nijeriya da suka fito daga jam'iyyu daban-daban, kamar haka: Yan takarar APC: Yemi OsinbajoOsinbajo, wanda daga Kwamishinan Shari'a na Jihar Legas ya zama Mataimakin Shugaban Ƙasa, ya ce, ya tsaya takara…
Read More
Na gama haddace halayen Buhari don zama Shugaban Ƙasa – Osinbajo

Na gama haddace halayen Buhari don zama Shugaban Ƙasa – Osinbajo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbanjo ya ce ya naƙalci duk wasu halaye na Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ce hakan zai taimaka masa wajen zama Shugaban Ƙasa. Osinbanjo ya furta hakan ne ranar Juma'a yayin wata ganawa da ya yi da wakilan Jam'iyyar APC a Jihar Oyo. Da yake bayyana nagartar sa a gaban wakilan, mataimakin shugaban ƙasar ya ce ya share shekaru dama yana samun horo da kuma shirye-shirye. Osinbanjo ya yi amannar cewa yana da ƙwarewar da zai tafiyar da ƙasar nan matuƙar ya gaji kujerar Shugaba Buhari a zaɓen 2023…
Read More
Kano 2023: Zan yi takara ba gudu ba ja da baya – Sheikh Ibrahim Khalil

Kano 2023: Zan yi takara ba gudu ba ja da baya – Sheikh Ibrahim Khalil

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Shugaban Majalisar Malamai na Kano da Arewacin Nijeriya, Sheikh Ibrahim Khalil, ya ce, babu gudu babu ja da baya kan batun tsaya wa takararsa wajen neman gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin tutar jam'iyyar ADC a zaɓen 2023 mai zuwa. Sheik Khalil ya bayyana haka ne lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a gidan tunawa da Malam Aminu Kano, wato Gidan Mumbayya, dake Unguwar Gwammaja a ƙaramar Hukumar Dala a Birnin Kano. Kakakin Majalisar Bauchi ya yi wa APC sakin da babu komeYari da Marafa sun sauya sheƙa zuwa PDP Shehin malamin ya bayyana…
Read More
Tinubu da Osinbajo: Wa zai kai wani ƙasa a APC?

Tinubu da Osinbajo: Wa zai kai wani ƙasa a APC?

*Siyasar ‘uba’ da ‘ɗa’ ta kunno kai a cikin jam’iyyar*Tinubu ya ‘sheganta’ Osinbajo*Yaro ya yi wa maigidansa ƙirmisisi Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A daidai lokacin da manyan zaɓukan 2023 ke ƙara tunkarowa, masu sha'awar taka takarar kujerar shugabancin Nijeriya a ƙarƙashin tutar jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar sai ƙara bayyana kansu suke yi ga al'umma tare da tuntuvar masu ruwa da tsaki, don neman shawarwari da goyon bayansu. Tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma jagoran Jam'iyyar APC na Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Mataimakin Shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbanjo, su ma kamar sauran manema, sun fito sun nuna kwaɗayinsu…
Read More
Lambar NIN: Waɗanda aka rufe layukansu su yi tururuwa ofisoshin kamfanonin sadarwa

Lambar NIN: Waɗanda aka rufe layukansu su yi tururuwa ofisoshin kamfanonin sadarwa

Daga AMINA YUSUF ALI Wasu masu amfani da layukan sadarwa sun shiga tsaka mai wuya a ranar Larabar da ta gabata bayan da suka wayi gari kamfanonin sadarwa suka rufe musu layukan waya. Wato aka hana su kiran waya gabaɗaya. Hakan ya biyo bayan umarnin gwamnatin Tarayya na a rufe layin dukkan wanda bai yi rajistar  shaidar ɗan ƙasa (NIN) a layin nasa ba. A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Gwamnatin Tarayya ta ba da umarni ga dukkan kamfanonin sadarwa da su tilasta wa 'yan Nijeriya yin katin shaidar ɗan ƙasa da kuma yin rajistar wayarsu da…
Read More
Azumin bana: Ga talauci ga tsadar kayan masarufi

Azumin bana: Ga talauci ga tsadar kayan masarufi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Watan Ramadan dai shi ne wata na tara a lissafin watannin Musulunci kuma yana daga cikin watanni masu alfarma. Hasali ma a cikinsa ne aka saukar da Alƙur'ani mai girma, wanda ya ƙunshi dukkan hukunce-hukuncen addinin Islama. Shi dai azumi shi ne kamewa daga cin abinci ko sha da kuma jima'i, haka kuma ana son mai azumi ya ƙara kamewa daga barin duk wani zance na alfasha ko kuma aikata zunubi. A na daina cin abinci ko sha ne tun daga fitowar alfijir har faɗuwar rana. Wannan ya sanya yawaitar buƙatuwa da abin kai wa…
Read More
Yadda APC za ta cigaba da mulki a 2023 – Sanata Adamu

Yadda APC za ta cigaba da mulki a 2023 – Sanata Adamu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce, kwamitin ayyuka na ƙasa (NWC) da ke ƙarƙashinsa zai yi aiki dare da rana domin jam’iyyar ta cigaba da riƙe madafun iko a shekarar 2023. Adamu, wanda ya yi magana a sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa da ke Abuja, a ranar Laraba, yayin da ya ke karvar takardar miqa mulki daga gwamnan Jihar Yobe kuma shugaban kwamitin tsare-tsare na riqon ƙwarya mai barin gado, Mai Mala Buni, ya ce, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba zai amince da gazawa ba. Sanata Adamu, tsohon gwamnan…
Read More