30
Apr
Daga AMINA YUSUF ALI A ƙarshen makon da ya gabata ne dai mai ɗakin Shugaban Ƙasar Nijeriya A'isha Buhari ta yi wani taron ganawa da masu zawarcin kujerar shugabancin ƙasar a zaɓen 2023. A yayin taron ne A'isha ta isar da roƙon ta ga 'yan takarar shugabancin ƙasar nan gabaɗaya da su zaɓi mata a matsayin abokan takarar tasu. 'Ya takarar Su ne, Bola Ahmad Tinubu, sai mataimakin shugaban ƙasa mai ci a yanzu, Farfesa Yemi Osinbajo, sai Dakta Chris Ngige da sauransu. Chris Ngige ya yi kira ga takwarorinsa 'yan takara da su yi biyayya ga abinda A'isha Buhari…
