02
Apr
Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Alhamis ne gidauniyar Bintaliya, wata gidauniya da ta yi fice wajen tallafa wa al'umma masu ƙaramin ƙarfi, ta raba wa dubun-dubatar al'umma kayan abincin azumin watan Ramadan a Jihar Kaduna. An gudanar da taron ne a ɗakin taro na Arewa House da ke Kaduna. Gidauniya ta bayar da irin nata tallafin ga al’umma ne musamman Waɗanda ke buƙatar taimako a garin Kaduna, inda ta ba wa dubun-dubatar al'umma tallafin kayan abinci da suka haɗa da shinkafa, taliya, maggi, Makaroni, gishiri, wanda al'umma da dama su ka amfana. Wakilinmu da ya shaidi rabon waɗannan kaya,…
