Babban Labari

Juyin wainar siyasar Zamfara: Dattijon ƙasa, Hassan Nasiha, ya koma na’ibin Matawalle

Juyin wainar siyasar Zamfara: Dattijon ƙasa, Hassan Nasiha, ya koma na’ibin Matawalle

*Shin gaba Sanata Nasiha ya ci ko kuwa baya? Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Daga dukkan alamu siyasar Jihar Zamfara na cigaba da zama wahainiyar da ke rikiɗa tana yin juyin wainar da ba a saba gani ba a tarihin siyasar Nijeriya bakiɗaya. Idan za a iya tunawa, a shekara ta 2019 kwana ɗaya kafin rantsar da sabuwar gwamnati ne bakiɗayan waɗanda aka zaɓa a tutar ƙarƙashin Jam’iyyar APC a jihar, Kotun Ƙolin Nijeriya ta kore su a yayin da ta yanke hukuncin da ya ɗora ilahirin ’yan takarar Jam’iyyar PDP, waɗanda bakiɗayansu sun faɗi zaɓe a lokacin da aka…
Read More
Babban Limamin Ƙaramar Hukumar Jema’a ya rasu

Babban Limamin Ƙaramar Hukumar Jema’a ya rasu

Daga ABUBAKAR LABARAN KAFANCAN Babban Limamin Ƙaramar Hukumar Jema'a da ke Jihar Kaduna, Alhaji Sheik Adam Tahir ya rasu yana da shekaru 130 a duniya. Jaridar Manhaja ta samu bayanin cewa Sheikh Tahir ya rasu ne ranar Laraba a garin Kaduna bayan fama da gajeruwar rashin lafiya. Da yake yi wa manema labarai bayani bayan rufe limamin a maƙabartar musulmai da ke Kafanchan, Mataimakin Limami na masarautar Kafanchan, Alhaji Muhammad D. Kassim ya ce babban limamin ya shafe fiye da shakara 35 yana gabatar da sallah a babban masallacin Kafanchan, ya bayyana cewa shi mutum ne na kowa, wanda kowa…
Read More
An halaka ɗan binidgar da ya kashe DPO

An halaka ɗan binidgar da ya kashe DPO

*Jiragen sojoji ya sheƙa Dogo Umaru da ’yan ta’adda 41 barzahu Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta samu gagarumar nasarar sheƙa wasu gungun ƙasurguman ’yan bindiga zuwa barzahu, waɗanda suka kitsa kashe Babban Jami’in ’Yan Sanda na Yanki (DPO) a Jihar Katsina. Hare-haren da jiragen NAF ya kai a jiya Alhamis ya samu nasarar halaka Dogo Umaru, wanda ƙusa ne a tafiyar babban ɗan bindigar nan, Bello Turji, wanda ake zargi da addabar yankin Arewa maso Yamma da ayyukan garkuwa da mutane da kuma kisan kiyashi. A tare da Umaru akwai ’yan bindiga…
Read More
Ƙarancin fetur ya jagwalgwala rayuwar ’yan Nijeriya

Ƙarancin fetur ya jagwalgwala rayuwar ’yan Nijeriya

*Za a warware matsalar ba jimawa – Gwamnati Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja ’Yan Nijeriya na cigaba da fuskantar azabar ƙarancin man fetur a ƙasar yayin da hukumomi suka ce su na yin aiki a wani yunƙuri na magance matsalar ƙarancin man da ya janyo raguwar kuɗaɗen shiga a kowane fanni. Birnin Abuja da manyan jihohin Nijeriya sun afka cikin matsanacin ƙarancin man fetur duk da alƙawarin da mahukunta suka yi na samar da shi. Wannan ya kawo cikas a harkokin yau da kullum, saboda ana sayar da shi da tsada, sannan kuma ga wuyar samu. A lokuta da…
Read More
NNPC ya bayyana gidajen man da suka shigo da gurɓataccen mai daga Belgium

NNPC ya bayyana gidajen man da suka shigo da gurɓataccen mai daga Belgium

*Lamarin ya rutsa da Oando, MRS, AY Maikifi da Duke Oil Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Babban Manajin Darakta Kamfanin Man Fetur (NNPC), Malam Mele Kyari, ya bayyana yadda aka shigo da gurɓataccen man fetur mai sinadarin ‘Methanol’ fiye da kima daga Ƙasar Belgium ba tare da an gano shi ba da kuma kamfanonin man da suka shigo da shi. Wannan na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya nuna cewa, gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin gudanar da wani gagarumin bincike domin bankaɗo al’amuran da suka shafi shigo da kayayyaki da kuma…
Read More
’Yan sanda sun mamaye sakatariyar APC yayin rantsar da shugabannin jihohi

’Yan sanda sun mamaye sakatariyar APC yayin rantsar da shugabannin jihohi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Jami’an Rundunar ’Yan Sanda ta Nijeriya sun mamaye sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa a Birnin Abuja. Wannan dai na zuwa ne gabanin ƙaddamar da shugabannin jam'iyyar na jihohi da aka yi a jiya Alhamis. An tattaro daga majiya mai tushe cewa shugabannin jam’iyyar na ƙasa sun tura ’yan sanda domin daƙile taɓarɓarewar doka da oda. Sassan jam’iyyar APC da dama sun shiga cikin rikici biyo bayan sakamakon zaɓen da aka gudanar na jihohi a bara. Jam’iyyar ta tsayar da ranar babban taronta na ƙasa:Za a gudanar da babban taron jam'iyyar APC na ƙasa a…
Read More
Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa ya sauya sheƙa zuwa APC

Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa ya sauya sheƙa zuwa APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sanata mai wakiltar Taraba ta Kudu kuma mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Emmanuel Bwacha, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar Peoples Democratic Party zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).  Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tarbi Bwacha zuwa APC a hukumance a Fadar Shugaban Ƙasa jiya Alhamis, inda ya miƙa masa tutar jam'iyyar mai mulki. Shugaban Kwamitin Riƙon Ƙwarya na APC kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya gabatarwa Buhari da Bwacha a fadar Villa da ke Abuja.  Mai ba shugaban ƙasa shawara a kan kafofin sadarwa ta zamani, Buhari Sallau ne…
Read More
Zan miƙa lafiyayyiyar ƙasa ga magajina – Buhari

Zan miƙa lafiyayyiyar ƙasa ga magajina – Buhari

*Za mu taya ka da addu’a, cewar Sarkin Musulmi Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ci alwashin cewa, zai miƙa lafiyayyiyar ƙasa mai cike da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da yalwar arziki ga magajinsa a shekara ta 2023, inda Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ci alwashin taimaka wa Shugaban Ƙasar da addu’o’i tare da kuma dukkan goyon bayan da suka kamata. Kalaman na Shugaba Buhari su na zuwa ne a yayin ziyarar aiki ta kwana ɗaya da ya kai a Sakkwato jiya; ziyarar da ke da manufar ƙaddamar da kamfanin…
Read More
Cire tallafin mai: Dalilin Buhari na bar wa magajinsa damar hukunci

Cire tallafin mai: Dalilin Buhari na bar wa magajinsa damar hukunci

*NNPC na buƙatar Naira tiriliyan uku a 2022 Daga MAHDI M. MUHAMMAD da SANI AHMAD GIWA a Abuja A ƙarshe dai Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ta yi watsi da cece-kucen da ake yi na buƙatar ko akasin haka wajen cire tallafin man fetur, inda ta ce, ta bar zaɓin aiwatar da hakan ga wanda zai gaji ofishin Shugaban Ƙasa a 2023, saboda yanayin halin da tattalin arzikin Nijeriya da ma na ’yan Nijeriya ke ciki a halin yanzu. Kana kuma, idan shawarar ta wuce gaban Majalisar Dokoki ta ƙasa da ake sa ran za ta ba ta wasu…
Read More
Buhari bai taɓa ba da umarnin cire tallafin fetur ba – Shugaban Majalisar Dattawa

Buhari bai taɓa ba da umarnin cire tallafin fetur ba – Shugaban Majalisar Dattawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa, ba za a cire tallafin man fetur ba a yanzu haka ba, saɓanin yadda wasu kafafen sada zumunta da na zamani suka ruwaito. Sanata Lawan ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan wata ganawar sirri da suka yi da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ranar Talata a Abuja. A cewarsa, Buhari bai taɓa bai wa kowa izinin a cire tallafin man fetur ba kamar yadda ake ta cece-kuce a wasu sassan…
Read More