Babban Labari

NAFDAC ta gamsu da ingancin rigakafin AstraZeneca

NAFDAC ta gamsu da ingancin rigakafin AstraZeneca

Daga FATUHU MUSTAPHA Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta ce, ta amince da ingancin maganin rigakafin korona na AstraZeneca don amfanin ƙasa. Shugabar hukumar, Mojisola Adeyeye ce ta sanar da hakan a wannan Alhamis. Da wannan, Nijeriya ta samu shiga jerin ƙasashen duniya da ke da dama wajen yaƙi da annobar korona. Yayin da take yi wa taron manema labarai bayani a Abuja, Adeyeye ta ce bayan da hukumar NAFDAC ta karɓi maganin, ba tare da ɓata lokaci ba ta sukunya bincike don tabbatar da ingancinsa. A cewar Adeyeye, baya ga rigakafin AstraZeneca da ta…
Read More
Nijeriya: An samu ƙaruwar matsalolin tsaro a ‘yan makonnin da suka gabata – Abdulsalami

Nijeriya: An samu ƙaruwar matsalolin tsaro a ‘yan makonnin da suka gabata – Abdulsalami

Daga FATUHU MUSTAPHA Tsohon Shugaban Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Zaman Lafiyar Ƙasa (NPC), General Abdulsalami Abubakar, ya ce a tsakanin makonni biyun da suka gabata matsalar rashin tsaro da rashin haɗin kai sun ƙaru a sassan Nijeriya. Don haka ya yi kira ga gwamnoni da su gyara ɗarama sannan su maganace waɗannan matsaloli da ke faruwa a jihohinsu. Abdulsalam ya yi kira ga 'yan ƙasa da a kasance masu haƙuri da juriyar mawuyacin halin da aka shiga, sannan a zamo masu sadaukarwa wajen daidaita lamurran ƙasa. Tsohon Shugaban Ƙasar ya yi wannan gargaɗi ne yayin ganawar da ya yi da…
Read More
Bawa ya kama hanyar kafa tarihi a hukumar EFCC

Bawa ya kama hanyar kafa tarihi a hukumar EFCC

Daga FATUHU MUSTAPHA A halin da ake ciki, Abdulrasheed Bawa, ɗan shekara 40, ya kama hanyar kafa tarihi na zama mai mafi ƙarancin shekaru da zai shugabanci Hukumar Yaƙi da Zambar Kuɗaɗe da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa (EFCC). A ranar Talata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa sunan matashin don neman amincewarta kan naɗa shi sabon shugaban EFCC. Bayanai sun nuna Bawa ƙwararre ne a fannin bincike dangane da batutuwan da suka shafi maguɗin kuɗi da sauran laifuka da suka danganci tattalin arziki. Tun bayan dakatar da shugaban riƙo na EFCC Ibrahim Magu, a ranar…
Read More
Kwamiti ya yi zaman farko don magance rashin zuwan yara makaranta

Kwamiti ya yi zaman farko don magance rashin zuwan yara makaranta

Daga FATUHU MUSTAPHA Kwamitin Gudanarwa kan Shirin Sabuwar Hanyar Bada Karatu (National Steering Committee on Alternate School Programme) ya yi taron sa na farko a ranar Litinin a Gidan Ma'aji (Treasury House) da ke Abuja. Taron ya fara aiwatar da tsare-tsare kan hanyoyin da za a bi a magance matsalolin da ke sanya yara su daina zuwa makaranta a Nijeriya tare da gaggauta rage yawan irin waɗannan yaran ta hanyar sama masu ilimin farko mai inganci da ilimin sana'o'in a wasu yanayi na musamman waɗanda ba a magance su a tsarin da ake da shi a yanzu ba. A jawabin…
Read More
‘Yan fashin daji na shirin mallakar makamai masu linzami, inji Sheikh Gumi

‘Yan fashin daji na shirin mallakar makamai masu linzami, inji Sheikh Gumi

Daga WAKILIN MU An bayyana cewa 'yan fashin daji da ke dazuzzakan jihohin Arewa suna shirin mallakar makaman kakkaɓo jirgin yaƙi domin daƙile hare-haren sojoji. Sheikh Abubakar Gumi ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da jaridar PUNCH ta yi da shi. A kwanankin baya ne Gumi ya ziyarci 'yan ta'addar a dajin Zamfara ya gana da su inda suka nuna suna satar mutane suna karɓar fansa ne domin tara kuɗaɗen sayen makamai. Bayan dawowarsa, Gumi ya yi kira ga gwamnati da ta duba ta yi wa ɓarayin afuwa domin ba su damar ajiye makamansu. Yayin ziyarar tasa Gumi ya…
Read More
Shugaban jaridun Manhaja da Blueprint ya sabunta rajistarsa a APC

Shugaban jaridun Manhaja da Blueprint ya sabunta rajistarsa a APC

Daga FATUHU MUSTAPHA A Juma'ar da ta gabata Shugaban Jaridun Manhaja da Blueprint, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya sabunta rajistarsa ta zama ɗan jam'iyyar APC a rumfar zaɓensa da ke Malagi, a ƙaramar hukumar Gbako da ke jihar Neja. Bayan kammala rajistarsa, Alhaji Idris ya yaba da yadda aikin yin rajistar ke guna cikin lumana a rumfar zaɓensu, tare da kira ga 'yan jam'iyyarsu ta APC a faɗin jihar kan kowa ya tabbatar da ya yi rajista ko sabunta rajistarsa. Yana mai cewa, "Na yi matuƙar farin ciki da yadda aikin yin rajistar ke gudana. Wannan wata alama ce mai…
Read More
Nijeriya za ta ƙirƙro rigakafin korona ba da daɗewa ba, cewar Minista Onu

Nijeriya za ta ƙirƙro rigakafin korona ba da daɗewa ba, cewar Minista Onu

Daga BASHIR ISAH Ministan Kimiyya da Fasaha Ogbonnaya Onu, ya ce nan ba da daɗewa ba Nijeriya za ta ƙirƙiro maganin rigakafin cutar korona don amfanin 'yan ƙasa. Ministan ya ce hakan zai samu ne ta dalilin tawagar ƙwararrun kimiyya da aka kafa ƙarkashin jagorancin Dr Oladipo kolawole na Jami'ar Adeleke, inda tawagar ke kan gudanar da bincikenta kan maganin cutar korona. Onu ya bayyana haka ne a Abuja a lokacin da ya karɓi baƙuncin wani kwamitin masana kimiyya a Abuja. Ministan ya yaba wa tawagar masu binciken daga Jami'ar Adeleke bisa sanya sunan Nijeriya a jerin ƙasashen duniya masu…
Read More
Galibin makiyayan da ke halaka mana mutane ba ‘yan Nijeriya ba ne, inji Ortom

Galibin makiyayan da ke halaka mana mutane ba ‘yan Nijeriya ba ne, inji Ortom

Daga BASHIR ISAH An bayyana cewa galibin makiyayan da ke halaka mutane a ƙasar nan ba 'yan asalin Nijeriya ba ne. Bayanin haka ya fito ne ta bakin Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata. Ortom ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya buƙaci a sake waiwayar dokokin ECOWAS don yin gyarar fuska dangane da sha'anin zirga-zirgar mutane da kayayyaki a nahiyar Afirka. Ya ce makiyaya daga wajen Nijeriya na amfani da damar zirga-zirga wajen ruruta matsalolin tsaro. Ta bakinsa, "Ƙasashe maƙwabta irin…
Read More
Buhari ya nuna alhininsa kan rasuwar Jakande

Buhari ya nuna alhininsa kan rasuwar Jakande

Daga FATUHU MUSTAPHA Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa dangane da mutuwar tsohon gwamnan jihar Legas, Chief Lateef Jakande, wanda Allah Ya yi wa cikawa a Alhamis da ta gabata. Sanarwar da ta fito ta hannun mai bai wa shugaban shawara kan sha'anin labarai da hulɗa da jama'a, Femi Adesina, Buhari ya ce marigayin ya yi rayuwa irin wadda al'umma ta amfana da ita. Sanarwar ta bayyana Jakande a matsayin mutum wanda ƙasa da al'umma suka amfana da rayuwarsa, wanda za a daɗe ana tunawa da kyawawan ayyukan da ya gudanar. Buhari ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin gami…
Read More
Gwamnati ta amince da shirin kula da dattawa, inji Minista Sadiya

Gwamnati ta amince da shirin kula da dattawa, inji Minista Sadiya

Daga WAKILIN MU Majalisar Gudanarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da sabon Shirin Kula Da Masu Manyan Shekaru ta Ƙasa, a turance 'National Policy on Aging', a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na tabbatar da tsaron lafiya da tattalin arzikin mutanen da yawan shekaru ya cim masu. Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ita ce ta bayyana haka ga manema labarai a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Laraba, jim kaɗan bayan taron hukumar, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta. A cewar ta, manufar shirin ita ce domin…
Read More