’Yan bindiga ko ’yan ta’adda: Canja matsayinsu zai kawo ƙarshen matsalar tsaro?

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Wata Babbar Kotun Tarayya da ta ke zamanta a Abuja a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Taiwo Taiwo ta ce, ayyukan ’yan bindiga da sauran ƙungiyoyi makamantansu a kowane yanki na Nijeriya ya zama na ta’addanci. Don haka ta ayyana su a matsayin ’yan ta’adda ƙarara.

Wannan hukunci na ayyana ’yan bindigar ‘yan ta’adda ya biyo bayan buƙatar da Daraktan Shigar da Ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, Mohammed Abubakar, ya shigar ne a madadin Gwamnatin Tarayya dangane da ayyukan ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda ne da sauran ƙungiyoyin masu aikata manyan laifuka a yankin ƙasar ya ke.

A cikin takardar da ta gabatar, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta roƙi kotun ne da ta haramta ƙungiyoyin ’yan bindiga da ’yan ta’adda tare da ayyuakansu da kuma sauran ƙungiyoyin ta’addanci a faɗin ƙasar.

Buƙatar, a cewar Gwamnatin Tarayya a wata takardar kariya, ta ce, ta duba ayyukan ƙungiyoyin da gwamnatin ta ce su ne ke da alhakin kashe-kashe, sace-sacen mutane, fyaɗe, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka a yankin Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya da sauran sassan ƙasar.

Gwamnatin Tarayya ta kuma zargi ƙungiyoyin da laifin sace-sacen mutane ba-zata don neman kuɗin fansa, sace-sacen yara ’yan makaranta da sauran ’yan ƙasa, satar shanu, bautar da bayi, ɗauri mai tsanani, tauye ’yancin kai, azabtarwa, fyaɗe, bautar jima’i, tilasta yin karuwanci, ciki dole, da sauran nau’in cin zarafin ɗan’adam, hare-hare da kashe-kashe a cikin al’umma da matafiya, da lalata rayuka da dukiyoyi.

Ta ci gaba da cewa, ƙungiyoyin ’yan bindiga da ’yan ta’adda da dai sauran ƙungiyoyi makamantan su ne ke da alhakin kashe sojoji da jami’an ’yan sanda da sauran jami’an tsaro a faɗin ƙasar.

“Ayyukan kasuwanci, ilimi, da noma a yankin Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya sun lalace sakamakon ayyukan ƙungiyoyin,” inji gwamnatin tarayya.

“Ayyukan ’yan Bindiga da ’yan ta’adda da sauran ƙungiyoyi makamantansu, sun zama ayyukan ta’addanci da ka iya haifar da taɓarɓarewar zaman lafiya da tsaro, tare da yin barazana ga tsaron ƙasa da kamfanoni na Nijeriya,” inji gwamnati a cikin takardar.

DPP ta ce, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da matakin da ya ɗauka, wanda manufarsa ita ce haramta ƙungiyoyin ’yan bindiga da ’yan ta’adda da sauran ƙungiyoyin ’yan ta’adda.

Hukuncin:
Musamman kotun ta ayyana ayyukan ƙungiyar ’yan bindiga da ƙungiyar ’yan ta’adda da sauran ƙungiyoyi makamantan su a kowane ɓangare na ƙasar nan, musamman a shiyyar Arewa maso Yamma da Arewa ta tsakiya, don zama ayyukan ta’addanci da rashin bin doka.

Alƙalin ya yanke hukuncin cewa, irin waɗannan ƙungiyoyi, ko dai a ƙungiyance ko kuma a matsayinsu na kowane irin suna, a kowane yanki na Nijeriya, musamman a shiyyar Arewa maso Yamma da Arewa ta tsakiya, ’yan ta’adda ne kuma an haramta su. Mai shari’a Taiwo ya ce, bisa la’akari da munanan ayyukan ’yan bindiga da illolinsu ga jama’a da tattalin arzikin ƙasa, ya tabbata cewa ana buƙatar irin waɗannan umarni.

Ya kuma miƙa dokar haramtawa duk wasu ƙungiyoyi a ƙasar nan, ba tare da la’akari da sunayensu ba, waɗanda ayyukansu da manufofinsu ya yi kama da na ƙungiyoyin ’yan bindiga.

A cewar hukuncin, ayyukan ta’addanci sun haɗa da, fashi da makami, garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, garkuwa da mutane don aure, sace yara ’yan makaranta da sauran jama’a, satar shanu, fashin kurkuku, tauye ’yanci mai tsanani, azabtarwa, fyaɗe, tilasta karuwanci, wasu nau’ikan cin zarafin jima’i, hare-hare da kashe-kashe a cikin al’umma da matafiya da lalata rayuka da dukiyoyi a Nijeriya.

Alƙalin ya ci gaba da cewa, dole ne gwamnatin tarayya ta buga wannan umarni na gurfanar da su a cikin Gazette na hukuma da kuma jaridu na ƙasa guda biyu a ƙasar.

Rahoton da aka ƙayyade na Gwamnatin Tarayya:
Hakazalika, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, ya ce, bayyana ƙungiyoyin ’yan bindiga a matsayin ƙungiyoyin ’yan ta’adda da wata babbar kotun tarayya ta yi ya nuna cewa gwamnatin Nijeriya ta ƙuduri aniyar murƙushe ’