Taron APC: Yadda takarar Sanata Abdullahi Adamu ke samun tagomashi

Daga BASHIR ISAH da MAHDI M. MUHAMMAD

Yayin da ake dab da gudanar da Babban Taron Jam’iyyar APC na Ƙasa daga dukkan alamu takarar neman kujerar Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa da tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ke yi ya samu tagomashi mai tarin yawa bisa la’akari da yadda ya ke samun goyon bayan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.

Gwamnonin jami’yyar sun yi mubaya’a ga ɗan takarar da Shugaba Buhari ke ra’ayin ya zama shugaban APC na ƙasa, wato Sanata Adamu (Turakin Keffi).

Da ya ke magana da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taronsu da Shugaba Buhari ƙarƙashin ƙungiyarsu ta Progressive Governors’ Forum a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, Gwamna jihar Kebbi, Alhaji Bagudu Atiku, ya ce sun cimma daidaiton bambance-bambancen da ke tsakaninsu game da babban taron jam’iyyar da ke gabansu wanda zai gudana gobe Asabar.

Atiku ya tabbatar cewa lallai da farko akwai ‘yan saɓani a tsakaninsu amma bayan zaman da suka yi da Buhari an samu maslaha.

Ya ƙara da cewa Shugaba Buhari ya ji daɗin wannan al’amari yadda gwamnonin suka haɗu tare da cimma matsaya guda inda za su samar da shugabannin da za su ci gaba da jan ragamar jam’iyyarsu nan gaba.

Bayanai dai sun nuna a Laraba ɗin da ta gabata ne takarar shugaban jam’iyya, Sanata Abdullahi Adamu da sauransu masu neman muƙamai a NWC sun haɗu da ‘yan takarar muƙamai na shiyyoyi a masaukin baƙi na gwamnan Katsina da ke Asokoro, Abuja don a tantance su.

An ga Sanata Abdullahi Adamu ya isa wajen tantancewar da rana inda ya tafi ya cimma kwamitin don a tantance shi.

Daga cikin waɗanda aka samu tantancewa ranar Talata da daddare har da tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Osun, Sanata Iyiola Omisore da Sanata Sani Musa da Tanko Al-Makura da George Akume da kuma Saliu Mustapha.

A wani labarin kuma, masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC sun jaddada goyon bayansu ga ɗan takarar shugabancin jam’iyyar kuma tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu.

Ƙungiyar wacce ta ƙunshi dattawan jam’iyyar na yanzu da kuma tsoffin ’yan majalisar APC da na yanzu, da na tsohuwar jam’iyyar da kuma matasan jam’iyyar a faɗin jihohi 36 na tarayya, sun ce ya zama wajibi a bayyana matsayinsu da ranar da za a yi zaɓe, gabanin kusantowar taron.

Da ya ke zantawa da wasu zaɓaɓɓun manema labarai, shugaban ƙungiyar kuma tsohon ɗan majalisa a jihar Adamawa, Injiniya Adamu Auta Fufure ya ce, abin da jam’iyyar APC ke buƙata a yanzu shi ne mutum irin Sanata Abdullahi, wanda ya fahimci jam’iyyar kuma ’ya’yan jam’iyyar suna mutunta shi sosai.

“Shi ɗan takarar siyasa ne kuma babban jagora, kuma abin da jam’iyyar ke buƙata ke nan a yanzu.” 

Fufure ya ƙara da cewa, Sanata Adamu shi ne shugaban da zai kawo jituwa, haɗin kai da cigaba ga jam’iyyar musamman a lokacin da muke tunkarar zaɓen 2023.

Shi ma Sani Baba Kano, ya ce, farin jini da karvuwar da Sanata Adamu ya samu ya nuna cewa shi ɗan jam’iyya ne na gaskiya, wanda ya yi ƙoƙarin kawo zaman lafiya da cigaban jam’iyyar APC da kuma kowace jam’iyyar da ya ke a cikin shekaru arba’in da suka gabata.

“Mutane ƙalilan ne suka ba da gudunmawar cigaban ƙasar nan da cigaban jam’iyyar kamar yadda Sanata Abdullahi Adamu ya yi. Ni kaina, ina jin waɗanda ke adawa da burinsa na zama shugaban ƙasa, mutane ne da ba su da wata maslaha ga jam’iyya a zuci”.

A nata ɓangaren, Evelyn Johnson daga jihar Akwa Ibom kuma tsohuwar shugabar mata ta bayyana cewa mai neman tsayawa takarar yana mutunta duk wani mutum da kuma bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya da aka sani kuma shi jagora ne na gaskiya.

Wani Shugaban Matasan Jam’iyyar APC daga Jihar Oyo, Bamidele Lekan Martins ya ce, “ban tava haɗuwa da Sanata Abdullahi Adamu ba, kuma ban tava yi masa magana ko na kusa da shi ba game da burinsa na zama Shugaban ƙasa amma ga duk mai ƙaunar APC, mun san cewa Sanata Abdullahi Adamu shi ne mutumin da ya fi dacewa da wannan aiki.”