Ra’ayi

Yayin da watan Azumi ya ƙarato

Yayin da watan Azumi ya ƙarato

A makon da za mu ne ake sa ran ɗaukar azumin watan Ramadan, wata mai alfarma ga dukkan Musulmin duniya. A ranakun wannan wata, waxanda suke kamawa guda 29 ko 30 a kowacce shekara, Musulmi sukan kaxaita daga aikata wasu muhimman abubuwa a rayuwar ɗan adam da rana, kamar ci, sha da jima’i. Lokacin haramcin hakan yana kamawa ne daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana a kulliyaumin. To, a zahirin gaskiya ba waɗannan abubuwa ne kaɗai abubuwan da ake sa ran Musulmi ya guje su ba, illa dai kawai za a iya cewa, waɗannan abubuwa guda uku, wato ci, sha…
Read More
Yadda APC za ta iya ci gaba da mulki har shekara 32

Yadda APC za ta iya ci gaba da mulki har shekara 32

Daga IBRAHIM SHEME A ranar Talata, shugaban riƙo na jam’iyyar APC na ƙasa, Mai Mala Buni, ya faɗi wata magana wadda ta bar baya da ƙura. A cewar sa, jam’iyyar za ta ci gaba da mulkin Nijeriya har zuwa shekaru 32 masu zuwa; wato dai, har zuwa shekara ta 2053. Idan ka haɗa da shekaru shida da ta yi daga 2015 zuwa yau, za ka samu shekara 38 kenan. Na so a ce Mai Mala Buni ya faɗa mana kuma yadda mulkin jam’iyyar zai ƙare a cikin 2053 tunda dai a nan ya yi mata iyaka. Shin a lokacin ne…
Read More
Ƙara taɓarɓarewar harkar ilimi a Arewa

Ƙara taɓarɓarewar harkar ilimi a Arewa

Wani rahoton musamman da jaridar Blueprint ta buga a ranar Talata ta makon jiya ya nuna cewa a cikin watanni uku kacal ’yan bindiga sun ci gaba da kai hare-hare a makarantu aƙalla guda biyar a yankunan Arewa-maso-yamma da Arewa-maso-gabas. Hakan ya haifar da damuwa a kan batun samar da ilimi ba kawai a waɗannan yankunan kaɗai ba har ma da lardin Arewa baki ɗayan sa. Rahoton ya ambaci jihohin Katsina, Zamfara da Kaduna a Arewa-maso-yamma da kuma Neja a Arewa-ta-tsakiya a matsayin inda ayyukan ta’addancin ’yan bindigar ya fi ta’azzara. Hari na baya-bayan nan da aka kai, an kai…
Read More
Ƙin samar da rigakafin cutar zazzaɓin cizon sauro

Ƙin samar da rigakafin cutar zazzaɓin cizon sauro

Daga NAJEEB MAIGATARI Kwanakin baya tattaunawa ta haɗa ni da wani aboki na, sai yake ce mun ai ana sane aka ƙi samar da rigakafin cutar zazzaɓin cizon sauro (Malaria) duk da irin yanda kuwa cutar ta addabi musamman ƙananun yara da yanda ta ke kashe su. Har ya jefo mun wata tambaya; me yasa ba a damu da samar da rigakafin ‘Malaria’ ba, amma aka damu mutane da yi mu su rigakafin cutar shan inna (Poliomyelitis) duk da cewar yanzu ba a fama da ita? Maganar gaskiya shi ne a wancan lokacin ba ni da amsar tambayar shi, saboda…
Read More
Muzguna wa Mahdi Shehu barazana ne ga yaƙin da Buhari ke yi na daƙile cin hanci

Muzguna wa Mahdi Shehu barazana ne ga yaƙin da Buhari ke yi na daƙile cin hanci

Daga ALIYU ADAMU TSIGA Cutar da Gwamnatin Jihar Katsina ke yi wa wani mai fallasa bayanan sirri, Mahdi Shehu, na yin barazanar yaƙi da cin hanci da rashawa na Shugaba Muhammadu Buhari, a cewar wata ƙungiyar farar hula. Ƙungiyar 'Movement for Good Governance and Greater Nigeria' (MGGGN), gamayyar ƙungiyoyin fararen hula da ke ƙoƙarin ganin bayan cin hanci da rashawa da samar da shugabanci na gari a ƙasar, a cikin sanarwar bayan taron da ta fitar a majalisar zartarwa na kasa da ta gudanar a Abuja a karshen mako, ta yi tambaya kan yakin da gwamnati ke yi da cin…
Read More
Kwara: Fahimtar juna game da hijabi

Kwara: Fahimtar juna game da hijabi

Daga IBRAHIM SHEME Sau da yawa, na kan yi mamakin yadda wasu ’yan Nijeriya ba su so a zauna lafiya; kullum ƙoƙari su ke yi su tsokano wata magana da za a dinga tada jijiyar wuya a kan ta. Dubi dai tataɓurzar da ake yi kan batun saka hijabi na ’yan makaranta mata Musulmi a Jihar Kwara. Wasu Kiristoci sun tashi haiqan a kan cewa ba su yarda mata ɗalibai su sanya hijabi su je makaranta ba. Abin da ya fi ba ni mamaki shi ne masu wannan kamfen ɗin ba wai wasu zauna-gari-banza kaxai ba ne, waɗanda za a…
Read More
Tashin gwauron zabo da farashi ke yi

Tashin gwauron zabo da farashi ke yi

Rahoton da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayar kwanan nan kan alƙaluman farashin kayan masarufi (CPI) abin damuwa ne matuƙa. Rahoton ya ce jadawalin tashin farashi a Nijeriya ya ƙaru da kashi 12.82 cikin ɗari a watan Yuli da ya gabata, kuma ba a taɓa ganin irin wannan tashin ba a cikin watanni 27 tun daga watan Maris na 2018 lokacin da farashi ya yi bala’in tashi da kashi 13.34 cikin ɗari. Wannan yanayin zai ƙara tavarɓarar da fatara da yunwa da ake ciki, wanda hakan kuma bazarana ce ga Shirye-shiryen Agajin Jama’a (SIPs) waɗanda Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa,…
Read More
’Yan bindiga: A yafe ko a bindige?

’Yan bindiga: A yafe ko a bindige?

Daga IBRAHIM SHEME Kwanan nan Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i, ya jawo wata muhawara a kan batun a yafe wa ‘yan bindiga ko a kashe su idan an gan su. Matsayar sa ita ce kada a yi wani zaman tattaunawa da su don a samu hanyar da za a warware ibtila’in kashe-kashe da ke faruwa a yankin Arewa-maso-yamma na ƙasar nan. Gara a nuna masu ƙarfin soja, a murƙushe su, babu sassautawa ko jinƙai. A wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon BBC, El-Rufa’i ya bayyana cewa duk wata hanyar lalama da za a bi…
Read More
Mawuyacin halin da Fulani makiyaya su ke ciki laifin gwamnonin Arewa ne?

Mawuyacin halin da Fulani makiyaya su ke ciki laifin gwamnonin Arewa ne?

Daga TIJJANI SARKI  A 'yan makonnin nan an sami tashin tashina a wanin ɓangare na jihohin kudancin ƙasar nan, har inda wani gwamna ya ke ba da sanarwar korar ƙabilar Fulani makiyaya daga faɗin jihar sa, abin har ya kai da ƙona musu gidaje da masallaci  duk dai bisa dogaro da su ba 'yan jihar ba ne. Kuma suna kawo yamutsi a jihar, kodayake mun jiyo Gwamnan Jihar Ogun na cewa suna zaman lafiya da Fulani sama da shekaru ɗari a jiharsa. Zai yi kyau mu ɗan yi waiwaye akan ƙabilar Fulani makiyaya wanda suke da ɗumbin yawa musamman a…
Read More
Toshe hanyar abinci a matsayin makami

Toshe hanyar abinci a matsayin makami

Daga IBRAHIM SHEME Toshe wa mutane hanyar da abinci zai isa gare su wani makami ne da ake amfani da shi a lokacin yaƙi. An yi amfani da shi a lokacin Yaƙin Basasar Nijeriya, wato Yaƙin Biyafra. Manufar wannan matakin ita ce a karya lagon abokan gaba, a rage masu ƙarfi, kuma a tilasta masu su aje makaman su. To amma Majalisar Ɗinkin Duniya ta haramta ɗaukar irin wannan matakin a kan farar hula. Duk wanda aka kama ya yi hakan, ya aikata babban laifi; ana iya gurfanar da shi a Kotun Miyagun Ayyuka ta Duniya (ICC). Sashe na  8(2)(b)(xxv)…
Read More