Mata A Yau

Dandalin shawara: Na kama matata da abokina, amma na kasa sakin ta (ƙarshe)

Dandalin shawara: Na kama matata da abokina, amma na kasa sakin ta (ƙarshe)

Tare Da AISHA ASAS TAMBAYA: Assalamu alaikum. Sunana……….daga……….. Na samu number daga hannun……..Dalilina na neman ki dai shi ne, abokina ne shi, na sanar da shi matsalar da nake tare da ita, sai ya ba ni number ki ya ce, na ma ki magana, wai kwanaki ma ke kin ka kashe matsalarsa da mai dakinsa. Wato mata nake da ita, kuma har ga Allah Ina masifar san ta, wannan ya sa nake kishinta ƙwarai da gaske. Ban rage ta da komai ba, duk abinda na mallaka zata iya iko da shi. Kuma ta ɓangaren kwanciyar aure daidai gwargwado ina duba…
Read More
Kafar sadarwa na taimakon mata matuƙa ta fuskar kasuwanci – Maryam Ango

Kafar sadarwa na taimakon mata matuƙa ta fuskar kasuwanci – Maryam Ango

"Da wuya kaga an wulaqanta macen da ke da ilimi da aiki da shi" Daga AISHA ASAS A yau shafin Gimbiya na jaridarku mai farin jini, Manhaja, ya zaƙulo maku ɗaya daga cikin mata matasan da suka canza kallon da ake yi wa mata ta ɓangaren sana'a, yayin da suka yi zurfin tunani wurin amfani da zamani wurin neman na kai. Sanannen abu ne kafafen sada zumunta sun zama wata taba ga matasa ta yadda za ka samu kaso mai yawa daga cikinsu da ba za su iya wuni ba tare da sun leƙa ba. Da yawa sanadiyyar soyayyarsu da…
Read More
Darasin da za mu koya daga shirin Mata A Yau na tashar Arewa 24

Darasin da za mu koya daga shirin Mata A Yau na tashar Arewa 24

'Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU'Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Shafukan sada zumunta, musamman manhajar Facebook da WhatsApp sun cika da muhawara da rubuce-rubuce game da wasu kalamai da ake danganta su da shirin nan na Mata A Yau da tashar talabijin ta Arewa 24 ke gabatarwa, wanda ke tattauna matsalolin da suka shafi rayuwar mata da ta iyali. Jama'a da dama sun yi ta bayyana ra'ayoyi mabambanta game da zargin da suke yi na cewa, manufofin shirin suna karo da koyarwar addinin Musulunci, da al'adar al'ummar Arewa. Haka kuma yadda masu gabatar da shirin suke zaƙewa wajen bayyana rashin dacewar wasu abubuwa…
Read More
Har yanzu ana kulle a aure?

Har yanzu ana kulle a aure?

Tare Da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a filin Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A wannan mako kuma, mun kawo muku bayani a kan yadda wasu mazan aure musamman ma mazajen Hausawa waɗanda suke yi wa iyalansu kulle. Menene kulle? Kulle shi ne a hana mace ta fita ko ta yi mu'amala da waɗanda take so. Yawancin mazan Hausawa suna da kulle amma sai dai yayin da wasu mazan suke da sauƙi wajen mu'amala da tafiyar da iyali, wasu mazan kuma suna da zafin kishi da tsaurarawa. A yau za mu yi magana a kan…
Read More
Fuska mai maiƙo

Fuska mai maiƙo

Daga AISHA ASAS Maiƙo a fuska ba ɓoyayen abu ba ne musamman ga mata. A lokacin da ki ka fahimci fuskarki na ƙyali fiye da adadin yanda ki ka shafa ma ta mai, za ki tabbatar da fuskarki na cikin layin fuskokin da ake cewa ‘oily face’ inji bature. A wannan sati da yardar Allah shafin kwalliya na jaridar Manhaja zai kawo wa masu bibiyar mu ababen da ke janyo maiƙon fuska da hanyar magance su. Idan kin gyara mu shiga cikin darasin kai tsaye: Ana samun fata mai maiƙo ta sanadiyyar yawan fitar ‘sebun’wanda ke ƙarƙashin ikon sabashiyos gilans…
Read More
Dandalin shawara: Na kama matata da abokina, amma na kasa sakin ta (2)

Dandalin shawara: Na kama matata da abokina, amma na kasa sakin ta (2)

Ci gaba daga makon jiya Tare Da AISHA ASAS Abu na farko kamar yadda ka faɗa kana son matarka, kuma na lura sosai, zai iya yiwa tsananin son da ka ke yi mata ya wuce tunanin ka, takan yiwu kana son rabuwa da ita saboda kana cikin matsanancin fushi da ita kan cin amanar da ta yi ma ka, amma wannan fushin naka bai shafi ɓangaren da ka mallaka mata a zuciyarka ba, don haka duk fushin da ka ke yi da ita, zuciyarka ba za ta iya lamunce wa rabuwa da ita ba. Idan kuwa hakan ne zancen, kana…
Read More
Tasirin yin nema kafin a kai ga aure

Tasirin yin nema kafin a kai ga aure

Tare Da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a shafinmu mai albarka na zamantakewa mai zuwa daga jaridarku mai farin jini, Blueprint Manhaja. A wannan mako muna tafe da dalilan ko na ce tasirin da ya sa ya kamata a fara nema kafin a kai ga aure. Nema dai a aure shi ne zaman da saurayi da budurwa ko bazawara suke yi na soyayya kafin a kai ga aure. Inda saurayi/magidanci zai ta ziyartar budurwa/bazawar (zance), da yi mata waya a kai-a kai har su fahimci juna, sun amince da juna, sannan daga bisani ya turo…
Read More
Dandalin shawara: Na kama matata da abokina, amma na kasa sakin ta

Dandalin shawara: Na kama matata da abokina, amma na kasa sakin ta

Tare Da AISHA ASAS TAMBAYA: Assalamu alaikum. Sunana……….daga……….. Na samu number daga hannun……..Dalilina na neman ki dai shi ne, abokina ne shi, na sanar da shi matsalar da nake tare da ita, sai ya ba ni number ki ya ce, na ma ki magana, wai kwanaki ma ke kin ka kashe matsalarsa da mai ɗakinsa. Wato mata nake da ita, kuma har ga Allah Ina masifar san ta, wannan ya sa nake kishinta ƙwarai da gaske. Ban rage ta da komai ba, duk abinda na mallaka zata iya iko da shi. Kuma ta vangaren kwanciyar aure daidai gwargwado ina duba…
Read More
Shawara game da samun maslaha tsakanin surukai

Shawara game da samun maslaha tsakanin surukai

Tare Da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Manhaja. Za mu ci gaba daga inda muka tsaya a kan dalilan da suke kawo lalacewar alaƙa tsakanin surukai. Ta yadda surukuta a ƙasar Hausa ta zama kamar gaba a tsakaninsu. Kowa kishi da hassada yake wa ɗanuwansa. Ga rainin wayo, abin ba a magana. A wani lokaci a baya mun kawo wasu daga cikin dalilan da suka sa hakan take faruwa domin masu karatu su yi alƙalanci su gano wai shin ma laifin wanene? To a yanzu za mu ci gaba da kwararo muku bayani…
Read More
Alaƙar jinin al’ada da zamantakewar aure

Alaƙar jinin al’ada da zamantakewar aure

Daga AISHA ASAS Allah S.W.A ya faɗa a cikin littafi mai tsarki “suna tambayar ka game da haila (al’ada) ka ce masu ƙazanta ne, su nisance mata har sai sun yi tsarki.” A wannan ayar mata suke fakewa suka haramta ko sumbatar mazajensu. A cewar su ko hannu ya haramta miji ya riƙe na matar sa har sai ta yi tsarki. Uwar gida ki sani a lokacin da ki ke al’ada saduwa kawai aka haramta maku. Da yawa mazaje masu mata ɗaya sukan shiga mawuyacin hali a lokacin da matansu ke al’ada wanda kaɗan ne daga cikinsu ke iya riƙe…
Read More