04
Jul
Daga AISHA ASAS Na san da yawa za su yi mamakin wannan darasi na mu, musamman ma maza da za su ga abin kamar cin fuska, kasancewar saki ɗaya daga cikin ababen da suke tinƙahon su kaɗai ke da iko kan sa. Kasancewar darasin na mu na yau tambaya, za mu fara da amsa ta, domin kawar da kwankwanton da mai karatu yake ciki. Amsar kuwa ita ce, mace na da damar sakin mijinta, sai dai ba irin damar da mijinta ke da kan ta ba. Na san za ku ce Asas ta zo da wani sabon al'amari, sai dai…
