08
Aug
Daga BASIRA SABO NADABO Matar bahaushe manyan duniya, ba a ɗaukar wankan kece raini sai za a yi tafiya gidan biki, mijinki ya iske ki da ɗaurin ƙirji. Matar bahaushe mai abin mamaki, a baki kuɗin cefane masu yawa ki yi girki da rabi ki kai rabi gidan mai adashi. Matar bahaushe ɗakinki kamar wajen siyar da dila, banɗaki kamar na kuturwa, mawankinki kamar kantin siyar da kwanonin abincin masu datti, ba kya sharar ɗaki sai an ji ƙawaye za su kawo ziyara saboda kar su raina ki. Matar bahaushe sai kin gama shirin zuwa wajen biki za ki tambayi…
