14
Sep
"Mata na fuskantar matsaloli yayin aiki tare da maza" Daga AISHA ASAS Yawaitar ƙalubale ga mata a yayin da suke aiki tare ko a ƙarƙashin maza ya jima yana kasancewa cikin al'ummar Hausa, wanda ya cancanci ya zama wutar da za ta cinye ilahirin burin mata na ɓangaren aiki. Da yawa daga cikin mata ƙalubalen na yin tasiri sosai a mafarkin zuciyarsu ta fuskar aiki, inda suke ajiye makaman yaƙi, su haƙura da burinsu. Duk da haka, akan samu jajirtattu daga cikin mata da suke iya jure wannan ƙalubale da ma wasu don tabbatar da ba su hana su isa…
