Mata A Yau

Na fuskanci ƙalubale a neman ilimin boko – Hon. Hafsat Abdullahi

Na fuskanci ƙalubale a neman ilimin boko – Hon. Hafsat Abdullahi

"Da kaina na yi fafutukar samun ilimin boko" Daga JOHN D. WADA a Lafiya Honorabul Hafsat Abdullahi cikakkiyar ‘yar siyasa ce da ta riqe muƙaman siyasa daban daban a Jihar Nasarawa. A yanzu ita ce mataimakiyar shugaban Ƙaramar Hukumar Lafiya kuma hedikwatar gwamnatin jihar. A tattaunawarta da wakilinmu, ta bayyana tarihin rayuwarta da ƙalubale da ta fuskanta a rayuwa da sauransu, inda ta kuma shawarci ‘yan uwanta mata su yi dukka mai yuwa wajen neman ilimin zamani da na addini da sauransu. Ga yadda hirar ta kasance: MANHAJA: Mu fara da jin tarihin rayuwarki.HONORABUL HAFSAT: Sunana Honorabul Hafsat Abdullahi. An…
Read More
Alamomin da ke nuna fata ba ta karɓi kayan kwalliyar da ake amfani da su ba (1)

Alamomin da ke nuna fata ba ta karɓi kayan kwalliyar da ake amfani da su ba (1)

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake saduwa a shafin kwalliya na jaridar al'umma Manhaja. Sannunku da jimirin bibiyar mu. A yau shafin kwalliya zai yi magana ne kan tafiya neman gira da ake yi a ɓangaren kwalliya sai kuma a rasa ido kan hanyar, ma'ana amfani da kayan gyaran fata ba tare da sanin zaɓin fatar ba, wanda lokuta da dama garin neman ƙibar sai kuma a tono rama, maimakon fatar ta yi kyau sai ta kamu da wata cutar. Sanin abin da fata ke buƙata a kwalliya yana da matuƙar muhimmanci a lokacin da kika ɗaura aniyar…
Read More
Saka murmushi a fuskar mabuƙata ke ba ni ƙwarin gwiwa – Maryam Yaro

Saka murmushi a fuskar mabuƙata ke ba ni ƙwarin gwiwa – Maryam Yaro

“Babban burina shine inganta rayuwar al’ummar Zamfara da sana'o'i" Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna A kullum iyaye mata ba su bari a bar su a baya, musamman a wannan zamanin su ne sahun gaba wurin taimakon al’umma a kowane yanki. Hajiya Maryam Shehu Yaro (Zarar Maru) ’yar asalin Ƙaramar Hukumar Maru a Jihar Zamfara ita ce mace ta farko da aka ba wa sarautar Zarar Maru a masarautar Maru da ke Ƙaramar Hukumar Muru, Jihar Zamfara. Allah Ya albakarkaci Hajiya Maryam da ‘ya’ya biyu mata, Hauwa da Amira. Hajiya Maryam gogaggiyar ‘yar boko ce, kuma ta na da ilimin addini,…
Read More
Wani sirri da ya kamata mata su sani game da kwalliya

Wani sirri da ya kamata mata su sani game da kwalliya

Daga QURRATUL-AYN SALIS  Mata da dama na son sanin sirrin da ke sanya kowacce kyau. A gaskiya zamani ya kaimu lokacin da babu mace mummuna sai dai in ta ga damar zama mummuna. Akwai sirrin kwalliya da dama, ta yadda duk munin mace idan har tana kulawa da su, zai yi wuya a ga muninta. Shi ya sa wasu mazan ke bai wa junansu shawarar gane kyakyawar mace, domin ka da a zo a yi zaɓen tumun dare. Idan mace ta zama mummuna ita ta so. Akwai ababe da dama da ake gyarawa daga yanayin shafa hoda da jan-baki da…
Read More
Haihuwar yuyuyu babbar fitina ce a cikin al’umma – Sameerah Shinko

Haihuwar yuyuyu babbar fitina ce a cikin al’umma – Sameerah Shinko

“Yawaitar ilimin mata zai kawo sauƙi ga matsalolin da suka addabi al'umma" Daga ABUBAKAR M. TAHEER Sameerah Bello Shinko haifaffiyar garin Sokoto da ke Arewacin Nijeriya ce.Ta yi 'primary' da Sakandire duk a cikin garin Sokoto. Sannan ta wuce Sokoto state polytechnic inda ta yi diploma a kan 'Sciences laboratory technology'. Sannan ta sake koma wa Waziri Umaru polytechnic Birnin Kebbi inda tayi HND a kan Microbilogy/biochemistry. yanzu kuma tana karatun Post graduate diploma a kan 'Environmental and public' a Bayero university Kano. Sameerah fitacciyar marubuciya ce sannan 'yar rajin kare haƙƙin bil adama musamman ma mata. Sunanta ya yi…
Read More
Mace ’yar kwalliya ce

Mace ’yar kwalliya ce

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake saduwa a cikin shafin kwalliya na jaridar al'umma Manhaja. Allah ya karɓi ibadunmu Ya sa mu cikin bayinSa da zai 'yanta a wannan wata na Ramdana.  A halittar 'ya mace a duk inda ta tunkaro, ana fara kallon abin da ta sa, yanayin shigar ta kafin kallon halittar jikinta. Wannan na nufin shigar mace ko kwalliyar ta ce annurinta. Duk kyawon ki, zai samu nakasu inhar ba kya gyara ko ince kwalliya. Kwalliyar da na ke magana kai a nan ba wai ta shafe-shafen kayan ƙyalƙyali ko ƙarin haske ko canza wani…
Read More
Mulkin mata zai fi tasiri fiye da na maza – Khadija Iya Abdullahi

Mulkin mata zai fi tasiri fiye da na maza – Khadija Iya Abdullahi

"Mata za su iya kawar da matsalolin ƙasar nan idan suka samu dama" Daga AISHA ASAS  An daɗe ana kiran sunan mata da babbar murya kan neman na kai da gujewa zaman kashe wando, daɗaɗen jan kunne ne da ya fi gemu tsufa, sai dai har yau wasu matan masu kunnen ƙashi sun sanya ƙafa sun shure wannan shawara ta gyara kayanka, duk da taurin kai na waɗannan mata, bai hana wasu jajirtattun mata ƙara tuna masu ba, kasancewar an ce hannunka ba ya ruɓewa ka yanke ka yar. Hajiya Khadija Iya Abdullahi na ɗaya daga cikin mata masu kishin…
Read More
Jarrabawar rayuwa ce ta sa na zama uwar marayu – Maryam Nabage

Jarrabawar rayuwa ce ta sa na zama uwar marayu – Maryam Nabage

"Aikin jin ƙai ko tallafa wa mabuƙata ba ruwansa da addini" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Sunan Hajiya Maryam Shehu Nabage da ake yi wa laƙabi da Uwar Marayu, ba ɓoyayye ba ne a cikin garin Jos da ma Jihar Filato bakiɗaya, saboda yadda ta yi fice wajen tallafa wa marayu, gajiyayyu, zawarawa da almajirai ƙarƙashin gidauniyarta ta Haske Support Foundation. Wakilin Manhaja Abba Abubakar Yakubu, ya ziyarci gidan ta dake Tudun Osi a unguwar Nasarawa Gwong, inda ya tarar da ita cikin tsakiyar aikin rabon kayan azumi da na ɗinkin sallah ga yara marayu. Ga yadda hirar su ta kasance:…
Read More
Kisan mijina ne ya sa na cire tsoron komai – Naja’atu Bala Muhammad

Kisan mijina ne ya sa na cire tsoron komai – Naja’atu Bala Muhammad

"Mace ba ta da ƙima a idon mafi yawan 'yan Arewa" Daga AYSHA ASAS Masu iya magana dai na cewa, idan ka ji wane ba banza ba, ko ba a sha dare ba an sha rana. A yau shafin Gimbiya ya ɗauko ma ku ɗaya daga cikin jajurtattun mata da suka yi fice ɓangaren gwagwarmaya da kuma ita kanta siyasar. Aysha Asas ce tare da Naja'atu Bala Muhammad. Masu karatu idan kun shirya: MANHAJA: Hajiya masu karatu za su so ki gabatar musu da kan ki.HAJIYA NAJA'ATU: Sunana Naja'atu Bala Muhammad, an haife ni a shekarar 1956 a cikin birnin…
Read More
Matan da ba su samu mijin aure ba (2)

Matan da ba su samu mijin aure ba (2)

Daga AISHA ASAS Barkanmu da sake saduwa a shafin iyali na jaridar al'umma, Manhaja. Idan ba mu manta ba, mun fara shimfiɗa kan darasin mu na yau tun a satin da ya gabata, don haka za mu ɗora daga inda bayanin mu na wancan sati ya tsaya: Idan kuwa mun amince hakan na faruwa, to ina yake laifi don mace ta rasa mijin aure, ko ta yi jinkiri. A tsangwame ta, a hana ta rawar gaban hantsi, duk don abin da ba ta da iko akan sa. Ba wai ina ƙoƙarin kare duk wata mace da ba ta yi aure…
Read More