06
Apr
Daga AISHA ASAS Barkanmu da sake saduwa a shafin iyali na jaridar al'umma, Manhaja. Idan ba mu manta ba, mun fara shimfiɗa kan darasin mu na yau tun a satin da ya gabata, don haka za mu ɗora daga inda bayanin mu na wancan sati ya tsaya: Idan kuwa mun amince hakan na faruwa, to ina yake laifi don mace ta rasa mijin aure, ko ta yi jinkiri. A tsangwame ta, a hana ta rawar gaban hantsi, duk don abin da ba ta da iko akan sa. Ba wai ina ƙoƙarin kare duk wata mace da ba ta yi aure…
