Mata A Yau

Duk macen da ta dogara da miji, za ta kwashi haushi – Fatima Kaita

Duk macen da ta dogara da miji, za ta kwashi haushi – Fatima Kaita

*Yawancin abinda ke jawo wa 'ya'ya mata shiga harkar lalacewa na da alaƙa da rashin sana'a - Fatima Daga AISHA ASAS Fatima Kaita cikakkiyar 'yar boko kuma 'yar kasuwa sannan 'yar gwagwarmayar siyasa, a hirar ta da jaridar Manhaja ta taɓo abubuwa da dama da su ka shafi muhimmancin sana'a ga 'ya mace ta yadda ba sai ta rage murya a wajen maigida ko 'yan'uwa ba. An dai ce waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi, don haka ga yadda hirar ta kasance: Ko za ki faxa wa masu karatu sunan ki da kuma ɗan taƙaitaccen tarihin ki?Assalamu alaikum,…
Read More
Duk namijin ƙwarai ba zai zauna da macen da za ta iya kisa ba – Khadija S. Mohammed

Duk namijin ƙwarai ba zai zauna da macen da za ta iya kisa ba – Khadija S. Mohammed

DAGA AISHA ASAS Wannan makon mun yi wa ma su karatun jaridarmu babban kamu a wannan shafin, domin mun samu damar tattaunawa da matar nan da ke bai wa ma'aurata da masu shirin yin aure shawarwari domin inganta zaman aurensu, har ta kai su kasance takalmin kaza. Da yake irin wannan cibiya ta Khadija Sa'ad Mohammed tamkar baƙon abu ne ga mutanen Arewacin Nijeriya, amma idan masu karatu suka biyo mu za su ji yadda baƙuwar tamu suke samun koke da jin matsalolin zamantakewar aure da kuma yadda suke bada shawara kuma a samu mafita da daidaito. Ga dai yadda…
Read More
‘Ya’yan mu da shaye-shayen kayan maye (2)

‘Ya’yan mu da shaye-shayen kayan maye (2)

Daga AISHA ASAS Idan ka sama wa ‘ya’yan ka uwa tagari to ka ba su kaso sittin bisa ɗari na tarbiyya. Uwa mai ilimi ce ta san fara tarbiyyar ‘ya’ya tun daga ɗaukar cikin su ne ba bayan haihuwa ba. Manzon (S.A.W) ya sanar da mu addu’a da ya ce ‘duk ma’aurata da su ka zo kwanciyar aure su ka karanta ta, idan an ƙadaro shigar ciki a wannan kwanciyar Allah zai nisanta ɗan da shaiɗan. “Allahumma janibnan shaiɗan ana, wa janibnan shaiɗan ala ma razaƙana” wannan kuwa mai ilimi ce kawai ta ke yin ta, ta ke tunawa mijin…
Read More
Yadda za a kula da tsaftar haƙora

Yadda za a kula da tsaftar haƙora

Daga AISHA ASAS Haƙora na ɗaya daga cikin ɓangarorin jiki da su ke bayyanar da tsafta ko ƙazantar mai su. Da yawa mu na ƙorafin bakin mu na wari ba dalili, alhali rashin kulawa da haƙori ya janyo hakan. Duk da cewa akwai matsalolin da ka iya haifar da warin baki ko da kuwa ana matuƙar kula da shi, kamar ciwon olsa da sauran su. Duk da haka kula da baki yadda ya kamata makami ne babba na yaƙar warin baki. Uwargida ki sani, saka makilin a magogi (burushi) ki goge baki da safe ba shi kaɗai bakin ki ke…
Read More

Ilimin ‘ya mace ya fi na namiji muhimmanci – Saratu Garba

Saratu Garba Hajiya Saratu G. Abdul ƙwararriyar malamar jinya ce kuma babbar ɗaliba wadda ta zage damtse a ɓangaren karatun aikin jinya tun a nan gida Nijeriya har zuwa ƙasashen ƙetare. A yanzu haka ta na ƙasar Amurka ta na ci gaba da karatun digiri na uku a ɓangaren aikin jinya. Saratu Garba Abdullahi dai ta na sahun farko kuma gaba-gaba a rukunin matan da su ka samu ilimi mai zurfi a arewacin Nijeriya, musamman ma a ɓangaren aikin jinya da ta ke cigaba da neman ilimi da ƙwarewa a kai. An dai ce waƙa a bakin mai ita ta…
Read More
Babban buri na shi ne in gina gidan marayu – Fauziyya D. Sulaiman

Babban buri na shi ne in gina gidan marayu – Fauziyya D. Sulaiman

Daga AISHA ASAS Sunan ki sananne ne, sai dai jin tarihin ki ne abin buƙatar masu karatu.Suna na Fauziyya D. Sulaiman. An haife ni a unguwar Fagge ta garin Kano a shekarar 1988. Na yi karatun Islamiyya a makarantar Maikwaru da ke Fagge da firamare ta ‘Festival Special Primary School’. Daga nan na tafi makarantar kwana ta ‘Yargaya inda na yi shekara uku, sannan na dawo makarantar ‘yan mata ta GGC Dala inda a nan na kammala karatu na. Daga nan na yi aure a 1999. A shekarar 2002 na koma karatu na yi difloma a ‘College of Hygiene’ a…
Read More
Idan da goyon baya mata kaɗai na iya ciyar da ƙasa – SWOFON

Idan da goyon baya mata kaɗai na iya ciyar da ƙasa – SWOFON

Daga BASHIR ISAH Kodinetar Ƙungiyar Ƙananan Manoma Mata (SWOFON) ta jihar Bauchi, Hajiya Marka Abbas, ta ƙarfafa cewa mata kaɗai na iya ciyar da ƙasa muddin suka samu goyon bayan da suke buƙata. Marka ta bayyana haka ne a wajen wani taron musayar ra'ayi game da harkokin noma, shiryawar ƙungiyar ‘Fahimta Women and Youth Development Initiative’ (FAWOYDI) tare da haɗin gwiwar ActionAid Nigeria, wanda ya gudana ran Litinin, a Bauchi. A cewarta mata sun fi maza iya tattali ta yadda za su iya amfani da kayan aiki kaɗan wajen samar da amfani mai yawa. Don haka ta yi kira ga gwamnati…
Read More
Duk wadda ta zauna za ta ga zaunau – Fatima Yusuf Muhammad

Duk wadda ta zauna za ta ga zaunau – Fatima Yusuf Muhammad

Fatima Yusuf Muhammad ta kasance mace mara kasala wajen fafutikar neman ilimi, sana’ar dogaro da kai da kuma faɗakar da al’umma da nishaɗantar da su ta hanyar rubuce-rubucen littattafan hikaya. A wannan makon Manhaja ta yi wa masu karatu kiciɓis da ita don jin yadda ta ke jifar tsuntsaye uku da dutse ɗaya, ma’ana ga neman ilimi da ta sa gaba, sana’a da kuma rubutu, ga kuma ɗawainiyar iyali. Kai, wani aiki dai sai mai shi. Ga yadda tattaunar ta kasance:  Masu karatu zasu so jin tarihin ki.Ni dai suna na Fatima Yusuf Muhammad. An haife ni a garin Kaugama…
Read More
Ya kamata gwamnati ta dinga sa mata wakilci domin samun hanyar tallafa wa mata

Ya kamata gwamnati ta dinga sa mata wakilci domin samun hanyar tallafa wa mata

Hajiya Zainab Sani Giwa mace ce ‘yar gwagwarmaya kuma mai son cigaban mata ‘yan’uwan ta ta fuskar wayewa da zamantakewa da kuma samun abin dogaro da kai. Ta yi fice sosai musamman a Ƙaramar Hukumar Giwa da ke Jihar Kaduna saboda kasancewar ta shugabar mata a yankin. A tattaunawar ta da jaridar Manhaja, masu karatu za su ji irin faxi-tashin da ta ke yi wajen faranta ran mata da marasa galihu. Daga AISHA ASAS a Abuja Masu karatu za su so jin cikakken suna da tarihin ki a taƙaice.Assalamu alaikum. To alhamdu lillahi, suna na Zainab Sani Giwa. Ni haifaffiyar…
Read More
An daina kishi na faɗan baki, sai na ƙwandala – Khadija Mahuta

An daina kishi na faɗan baki, sai na ƙwandala – Khadija Mahuta

Hajiya Khadija Abdulrasheed Mahuta mace ce wadda ya kamata mata su yi koyi da ita, kasancewar ta jaruma kuma tsayayya, sannan da ta san ciwon kan ta. Ta kasance cikin jerin mata da su ke tauna taura biyu a lokaci guda. Ma’ana, mace ce wadda ba ta zauna ba don jiran sai wani ya samo ya kawo mata, a’a, ta tashi tsaye ne haiƙan wajen rufa wa kan ta asiri. Wakiliyar Manhaja ta tattauna da ita inda ta bayyana wa masu karatu rayuwar ta wadda za ta iya zama makaranta ga mata. Daga AISHA ASAS Masu karatu za su so…
Read More