05
Jul
Hukumar ƙwallon da ƙwallon ƙafar Nahiyar Turai (UEFA) ta bai wa ‘yan kallo damar shiga filayen wasanni tare da robobin ruwa a hannu a yayin wasannin gasar kofin ƙasashen Turai ajin mata da ake farawa a ranar Laraba a ƙasar Switzerland, inda a yanzu haka yanayin zafin ke haura maki 30 a ma’aunin celsius. Cikin sanarwar da UEFA ta fitar a ranar Talata, hukumar ta ce maɗaukan ruwa ƙanana na robobi kaɗai aka bai wa ‘yan kallo damar shiga filayen wasa da su banda na kwalaben gilashi. Daga cikin ƙa'idodjin da aka rubuta a bayan tikitin shiga filayen wasa shine…
