11
Jun
Daga USMAN KAROFI A wani fafatawa na sada zumunta da aka buga a daren Talata a filin wasa na City Ground, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Senegal ta lallasa Ingila da ci 3-1, abin da ya sa ta kafa tarihi a matsayin ƙungiya ta farko daga nahiyar Afirka da ta doke Ingila. Harry Kane ne ya fara zura ƙwallo a ragar Senegal bayan ɗan wasan gaban Ingila, Anthony Gordon, ya gwada bugun da mai tsaron ragar ya mayar, amma Ismaila Sarr ya farke ƙwallon kafin ƙarshen rabin lokaci. A zagaye na biyu, Habib Diarra ya ƙara ci gaba da jefa ƙwallon…
