Fasahar marubuta waƙoƙin Hausa

Daga AISHA ASAS

Waƙa: HANKALI
Tare da Khalid lmam

Hankali gatan tunani,
Jagora ne gare shi,
Mai yin saiti wajen shi.

Shi doki ban da shakka,
Hawa nasa ko ga sarki,
Sai da linzami ku lura.

Shi tunani na fahimta,
Yafi mai saƙa a tufka,
Shi ka saƙa ko ya tufka.

Hankali in ka yi dace,
Shi kasa shi idan ya saƙa,
Sai ya tufke in da khairan.

In ba khairan a saƙar,
Sai ya kunce ba hiyana,
Saƙarsa ya ce ya sake.

Hankali tsanin tunani,
Shi hawa sama ko ga dogo,
In da tsani yafi tabbas.

Mai tunani mai basira,
Hankali na taimakonsa,
Rami ya gani ya kauce.

Hankali baiwa ga Bawa,
Shi kasa Bawa ya more,
Komai zai sai ya lura.

Ko da sarƙaƙiya cikinsa,
Babu shakka ko ga yaro,
Hankali riba akwai shi.

Ko basira ta yi teku,
Arziki na ruwa da kifi,
Hankali na taimakonta,

Roƙo na ya Ilahu,
Hankali Allah ka bani,
Kar na zam Sauna a dangi.

Mara lissafi da lura,
Shi ne soko da sauna,
Mai asara ko ladama.

Gaula ke ja ya dage,
Ilimi nasa ya ishe shi,
Hankali wai bai buƙata.

Aiki mai yi da lura,
Yafi mai duban agogo,
Samun nasara a aiki.

Rayuwa da awo ake yi,
Hankali ke auna nisa,
Zurfi na haƙa a rami.

Rijiya in za a yashe,
Hankali ke sa a gane,
An cimma idon ruwanta.

Hankali in ya yi rauni,
Shi ka sanya wuƙa ya yanke,
Shiri na mutum ya watse.

Hankali in ya yi nisa,
Zautuwa Bawa yake yi,
Yai ta sambatu a titi.

Nitsuwa nasa a gane,
Haka lissafi da lura,
Hankali na mutum a tace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *