Fusatattun jama’ar gari sun sheƙe ɗan leƙen asirin ’yan bindiga a Kaduna

Daga WAKILINMU

Wasu fusatattun mutane sun kashe wani mutum da matarsa da ɗansa a unguwar Zangon Aya da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna bisa zargin bada bayanai ga ’yan bindiga.

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Samuel Aruwan, kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna, ya bayyana a ranar Talata cewa, hukumomin tsaro sun kai rahoton kisan ga gwamnatin jihar.

Rahoton ya ce, an kashe Abdullahi Mohammed Gobirawa da matarsa Binta Abdullahi da ɗansa Hassan Abdullahi a lokacin da wasu ’yan daba suka kai farmaki gidansu da yammacin ranar Litinin.

“Ayyukan da ’yan ƙungiyar su ka aikata ya kasance martani ne ga zargin haɗin baki da mutanen uku da ‘yan bindiga, musamman dangane da sace-sacen da aka yi kwanan nan a yankin. Bayan kashe mutanen uku, ’yan iskan sun yi awon gaba da su tare da ƙona musu gida.”

A yayin da yake karɓar rahotannin, Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana baƙin cikinsa da tsananin damuwarsa kan ta’asar da ‘yan ƙasar ke aikatawa, ya kuma yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi ba bisa ƙa’ida ba. Ya kuma jaddada cewa kamata ya yi a yi amfani da hankali wajen wajen tinkarar zarge-zargen aikata laifuka, saboda ɓarnar da ake yi ɗaukar doka a hannu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *