Hadi Siriki da ƙaninsa sun ƙi amsa laifin karkatar da dukiyar ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa, EFCC, ta gurfanar da Hadi Sirika, tsohon ministan sufurin jiragen sama a gaban kotu bisa zargin almundahanar kwangila.

EFCC ta gurfanar da Sirika ne tare da ɗan uwansa, Ahmad Abubakar Sirika kamfanin da Enginos Nigeria Limited, wani kamfani mallakin Abubakar, a gaban mai shari’a Suleman Belgore na babban kotun babban birnin tarayya Abuja da ke zaune a Garki, Abuja.

An gurfanar da su a gaban kotu kan tuhume-tuhume 10 da aka gyara ranar 13 ga Mayu kuma aka shigar da su ranar 14 ga Mayu, 2024.
Ana zargin Sirika da cin zarafin ofishinsa ta hanyar bayar da kwangiloli na Naira biliyan 19.4 ga Enginos Nigeria Limited.

Duk waɗanda ake tuhumar sun ƙi amsa laifukan da ake zargin su da aikatawa.