JAMB za ta biya diyya ga ɗaliban da aka sauya wa gurin jarrabawar da ba su ne suka zaɓa ba

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Haɗaka ta Bada Gurbin Karatu (JAMB), ta ce za ta biya diyya ga dukkan wanda ya bada gamsassun hujjoji game da ɗaliban da aka tura su rubuta jarrabawa a wuraren da ba nan suka zaɓa ba.

A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun jami’in hulɗa da jama’arta, Fabian Benjamin, hukumar ta ce wasu ɗalibai suna yaudarar iyayensu game da gurin da aka tura su, yayin da kuma jagororin makarantu suke zargin JAMB da tura ɗalibai guraren ba nan ne garuruwan da suka zaɓa ba a lokacin rajista.

Babban jami’in ya ce, kowane ɗalibin JAMB ya na da damar zaɓar garin da ya ke son rubuta jarrabawar, yayin da ita kuma hukumar ta ke zaɓa masa inda zai rubuta a garin da ya zaɓa.

Ya kuma ce, ana yin haka ne tun a lokacin da ɗalibi zai yi rajista, inda a nan ne ake ba su zaɓin ɗaya daga cikin cibiyoyin rubuta jarrabawar dake yankin da suka zaɓa.

Ya kuma bayyana cewa, hukumar tana yin hakan ne da nufin sauƙaƙa al’amura ga ɗaliban, lamarin da ya sa ake ba su zaɓi a yayin rajista.

Har’ilayau, ya ce ana kira ga al’umma ga dukkan wanda ya samu labarin wanda aka tura wajen da ba nan ne zaɓinsa ba da ya tuntuɓi Hukumar bada kariya ga Kwastomomi ta Ƙasa, wato FCCPC ta Wattsapp acikin kwanaki huɗu ta lamba kamar haka: 08056003030 don tabbatar da bada diyyar ga wanda abin ya shafa.