Ƙalubalantar canja fasalin Naira ya sa na sha kaye a zaɓe – Matawalle

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya alaƙanta dalilin faɗuwarsa zaɓe da ƙarar da suka shigar da Gwamnatin Tarayya akan sauya fasalin kuɗi da Babban Bankin Nijeriya ya yi.

Gwamnan ya zargi cewar, wasu ƙushoshi a cikin Gwamnatin Tarayya da yin yaƙi da shi tuƙuru domin ganin bai sake komawa gwamnan jihar ta Zamfara ba.

Idan za a iya tunawa, Matawalle ya yi takara ne a jam’iyyar APC mai mulki, inda Dauda Lawal na jam’iyyar PDP ya buga shi da ƙasa.

Bugu da ƙari, gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje sun kai ƙarar Gwamnatin Tarayya zuwa Kotun Ƙoli.

A bisa yunƙurin canja fasalin kuɗi tare da taƙaita anfani da su wanda CBN ke aiwatar wa.

Matawalle ya ce, “An ce tunda mun je kotu akan canja fasalin kuɗi na Naira. To dani, da Ganduje da El-Rufai duk sai an hukunta mu.”

To amma a ɗaya ɓangaren, za a iya tunawa Sanata Uba Sani na jam’iyyar APC da El-Rufai ya ke marawa baya ya sha da ƙyar a Jihar Kaduna.

Yayin da ɗan takarar da Ganduje ke marawa baya, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya sha kayi a hannun ɗan takarar jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *