Ƙasashen Sin da Togo sun samu sakamako mai kyau a fannin haɗin gwiwa

Daga CMG HAUSA

A ranar 19 ga wata ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Togo Faure Essozimna Gnassingbé, suka aikewa juna sakon taya murna, game da bikin cika shekaru 50 da kulla hulɗar diplomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

Game da hakan, jakadan ƙasar Sin a jamhuriyar Togo, Chao Weidong, ya bayyana a wata hira da ya yi da ‘yan jaridar kafar CMG a jiya Jumma’a cewa, tun bayan ƙulla hulɗar diplomasiyya tsakanin Sin da Togo, ƙasashen biyu sun nuna goyon baya ga juna, kuma sun samu manyan nasarori a fannin haɗin gwiwa.

A fannin samar da ababen more rayuwa, bisa ƙwarya-ƙwaryar ƙididdiga, ƙasar Sin ta gina, ko gyara hanyoyin mota 17, da gadoji 12 a ƙasar Togo, waɗanda ke sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a, da jigilar kayayyaki.

Kana wasu ayyuka, kamar babban filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Lomé, da hanyar Lomé da ta kewaye birnin, wadda ɓangaren Sin ya aiwatar, sun zama abun alfahari ga ƙasar Togo.

Baya ga haka, Chao Weidong ya ce, “Tun daga ranar 1 ga Satumbar nan, ƙasar Sin ta aiwatar da dage harajin sifiri, har kashi 98%, na kayayyakin dake fitowa daga Togo zuwa ƙasar Sin”.

Mai fassara: Bilkisu Xin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *