Ƙidayar 2023: Hukumar NPC ta saki albashi da kuma alawus-alawus na ma’aikatantan wucin-gadi

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar Ƙidayar Al’ummar (NPC) ta fitar da tsarin albashi da alawus-alawus na ma’aikatanta na wucin-gadi waɗanda za su yi aikin qidayar al’umma da gidaje na shekarar bana ta 2023.

Idan ba a manta ba a kwanan nan ne dai hukumar ta kammala aikinta na ɗaukar ma’aikatan wucin gadin da za su yi aikin ƙidayar, kuma sannan ta bayyana cewa, atisayen zai faru ne a tsakanin 29 ga Maris da kuma 2 ga watan Afirilu.

A cewar hukumar NPC, kuɗin da za a biya ma’aikatan na wucin-gadi kala biyu ne – wato alawus da kuma albashi.

A cewar Daraktar sashen ƙidaya, Malama Evelyn Arinola Olanipekun, ma’aikatan wucin-gadin za su amshi alawus guda 3 ne kamar haka; akwai alawus ɗin abinci dubu biyu kowacce rana na tsahon kwanaki 13, sai alawus ɗin amsa da bayar da horaswa, da kuma alawus ɗin kuɗin mota.

Sannan kuma za a biya albashi bayan kammala aikin. Kuma albashin ma’aikatan wucin-gadin ya kama daga dubu 50 zuwa dubu 250 ya danganta da muƙamin da ma’aikacin yake.