Ƙungiya ta ɗauki nauyin horar da mata 100 girki a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Ƙungiyar Northern Chef Kamal Foundation ta shirya tsaf don koyar da mata 100 girke-girke saboda ƙaratowar azumi.

Taron ba da horon zai zai gudana ranar Laraba, 8 ga Maris, a Unguwar Hotoro, Kano.

A tattaunawar da ya yi da Blueprint Manhaja, shugaban ƙungiyar, Kamal Ahmad, ya ce ranar ta zo daidai da babbar rana ga mata, wato Ranar Mata ta Duniya,

Ya ce babban maƙasudin koyar da mata a wannan karon shi ne samar da ingantaccen abinci mai gina jiki musamman a watan azumin Ramadan da ke ƙaratowa, da kuma ƙara kulla kyakkyawar alaƙa a tsakanin ma’aurata da kuma bai wa yara abinci mai inganci.

Baya ga koyar da girke-girke, ƙungiyar Northern Cheef tana ciyarwa da raba dafaffen abinci ga mabuƙata da kuma ciyarwa a lokacin azumi.

Ya kuma ce a cikin shekaru 3 da kafa ƙungiyar sun horar da mata fiye da 500 yadda ake girki.

Ya yi kira ga al’umma da kuma gwamnati wajen tallafa wa irin wannan ƙungiya don ƙarfafa musu wajen ci gaba da faranta zukatan al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *