Ƙungiyar ma’abota kafafen yaɗa labarai ta tallafa wa ’yan gudun hijrar Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sokoto

Ƙungiyar ma’abota kafafen yaɗa labarai da cigaban ƙasa ta jihar Sakkwato ta gabatar da kayan agaji ga hukumar zakka da makafi ta jihar, domin raba wa mutanen da rikicin ’yan bindiga ya shafa a jihar.

Da yake jawabi, shugaban ƙungiyar na jiha Abdul’Aziz Muhammad Assada, ya ce, sun bayar da tallafin ne domin ƙarawa ƙoƙarin gwamnati a matakai daban-daban na rage raɗaɗi ga waɗanda harin ‘yan bindiga ya shafa.

Da yake mayar da martani a lokacin da yake karɓar kayayyakin, Shugaban hukumar, Malam Muhammad Lawal Maidoki ya yaba da irin hangen nesa da ƙungiyar ta yi wajen ƙara ƙaimi ga ƙoƙarin gwamnati a wannan fanni.

Shugaban zartarwa ya kuma buƙaci al’umma da ƙungiyoyi da su yi koyi da wannan ƙungiyar.

Haka zalika ya yi alƙawarin cewa, hukumarsa za ta ƙara da abin da aka bayar da kuma rabawa ga masu tsananin buƙatar kayayyakin agaji.

Kayayyakin da aka bayar sun haɗa da saiti ɗari ɗari na kayan sawan maza 50 da mata 50 da kuma buhun garin kwaki guda biyu.

Sauran waɗanda suka yi jawabi a wajen taron sun haɗa da uban ƙungiyar kuma uban ƙasar Katami Alh Usman Garba, da shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar, Babandiga Dan Masani da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *