Ƙungiyar marubutan Arewa ta yi taro don inganta tafiyarta

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Ƙungiyar marubutan Arewa mai suna Authors Forum m, ta yi zaman tattaunawa dangane da yadda za a shirya taron gani da ido karo na farko tare dukkanin mambobinta da ke faɗin ƙasar Nijeriya.

Wannan ƙungiya mai farin jini ta marubutan Arewa, ta shirya zama na musamman domin Tattauna muhimman batutuwa a ciki har da ƙirƙiro taron gani da ido don sada zumunci tsakanin marubuta da kuma ƙara wa juna sani a karo na farko.

Shi dai wannan zama an yi shi ne a kano inda uwar ƙungiyar ta fito wacce take da rassa a jahohi sama da goma shabiyu dake Arewacin Nijeriya. Taron ya gudana ne a ɗakin taro na Makarantar Koyar da Na’ura. Ai ƙwaƙwalawa ‘Troubleshooting Information Technology (TIT)’ da ke Unguwar Hotoro Danmarke.

Malam Khalid Khalid daga Jahar Kano shi ne wanda ya buɗe taro da Addu’a, inda daga bisani Mai magana da yawun ƙungiya na ƙasa (PRO) Injinya Bashir Isyaku Hotoro, ya zaiyano nasarorin da ƙungiyar ta ke samu tun a karon farko kafin ma tafiya ta yi nisa.

Ya ce yanzu haka babbar nasarar da ƙungiyar ta marubutan Arewa ta samu ita ce shigar sunanta lungu da saƙo a Arewacin Nijeriya musamman ga malaman jami’o’i da ɗalibai masu nazarin rubutu da kuma bibiyar Adabi kamar yadda ya dace.

Haka zalika, ya baiyana cewa yanzu haka ƙungiyar ta shiga hannun wasu jiga jigai kuma masana da ke Jahar kano, wanda da yawan su sun yaba da aiyuka da kuma manufofi na ƙungiyar, inda suka bada shawarwari dangane da yadda za’a ciyar da tafiyar gaba, da kuma bada gudummuwa da tallafawa Marubuta ta fuskar Rubutu wanda suiaka daɗe suna yi da kuma masu tasowa.

Ƙungiyar ta samu yabo da jinjina bisa yadda take gudanar da harkokinta, lamarin da wasu ke kallon ya bambanta da na sauran ƙungiyoyin marubuta da aka saba gani a Arewacin Nijeriya.

An saurari fashin baƙi dangane da jawaban da suka gabata daga bakin Malam Adamu Yusif Indabo wanda shine Magatakarda na ƙasa a wannan ƙungiya ta marubutan arewa. Marubucin Laitattafai da Finafinai wanda ya tsunduma cikin harkar ɗaukar nauyin shiri (Producer) Malam Zubairu M. Balannaji. Ya bada shawarwari danga ne da yadda za’a shirya taron da za’a gabatar nan bada jimawa ba idan Allah ya yarda.

Marubuciya Ummi Fulani na daga cikin waɗanda suka yi jawabi a wajen taron, ta kwararo bayanai masu kamun hankali da ƙara ƙaimi a cikin harkar rubutu.

A ƙarshe Malam Aliyu Usman Al’usku ya rufe taro da addu’a sannan aka tashi. Taron ya samu mahalarta daga sassa faban-daban.