‘Yan bindiga sun sace tsohon Ministan Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja, Sanata Solomon Ewuga, a jihar Filato.

Sace shi na zuwa ne bayan kisan gillar da aka yi wa Dakta Chike Akunyili, mijin tsohon Ministar Yaɗa Labarai kuma Babbar Daraktar NAFDAG, Farfesa Dora Akunyili.