Yadda bikin bajekolin finafinan Afirka na Kano ya gudana

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Babban Kamfanin shirya Finafinai da horarwa na Moving Image Nigeria Limited, kamar kowace shekara wannan ma ya shirya Bikin Bajekolin Finafinan Harsunan Afirka na Kano, wato ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ (KILAF), wanda shi ne karo na 5.

An dai shafe tsawon kwana biyar ana gudanar da tarurruka da shagulgula, wanda aka fara ranar Talata 22 ga Nuwanba aka kuma ƙarƙare a ranar Asabar, 26 ga Nuwamba, 2022.

Daga cikin abubuwan da aka gudanar, an yi horaswa kan dabarun ayyukan da su ka shafi harkar fim kamar ba da umarni, 4 labari, ɗaukar hoton fim, tacewa da kuma tace murya, inda aka ɗauki tsawon kwana uku ana yi a Digital Bridge Institute da ke Titin Filin Jirgin Sama.

Kazalika an gudanar da taron sanin makamar aiki na kwana biyu a otal ɗin Tahir, wanda aka kira da ‘Master Classes’, inda a nan ma ƙwararru a kan harkar fim na duniya su ka bayar da ilimi a game da sana’ar.

An gudanar da babban taro a Sashen Koyar da Aikin Jarida na Jami’ar BUK inda masana su ka gabatar da maƙaloli da laccoci.

Sannan an shirya bajekolin abincin gargajiya na Afrika, wato ‘African Kitchen’, inda aka baje abinci kala-kala domin mahalarta tare kuma da wasu zane-zane da kayayyakin gargajiya na nahiyar.

Da ya ke ƙarin haske, shugaban shirya taron, Malam Abdulkareem Muhammad, ya bayyana cewa maƙasudin shirya KIlAF shi ne a asssa yin finafinai a harshen Afirka, saboda kowane harshe na Afirka yana da muhimmaci don ya na da masu yinsa.

Ya ƙara da cewa “mun lura cewa idan muka shantake muka biye wa Turai duk finafinansu za a rinƙa yin su ne a harsunansu ne, to mu kuma mai ya hana mu rinƙa yi a harsunan na mu ba, domin idan kana yin fim da wani harshe to kana raya shi ne duk kuma yaren da ba a raya shi sai ka ga cewa ya fuskanci barazana na shuɗewa a doron ƙasa to ba mu san haka ta faru a harsunan Afirka wannan ne ya sa muka bijiro da wannan dandamali, don idan an yi finafinan mu auna mu tantance sai mu fidda waɗansu mu ba su kyautuka.”

Ya cigaba da cewa “Tawaga daga ƙasar Nijar mutum 11ne daga ƙasar Kenya mutum 2 daga ƙasar Afirka ta Kudu mutum 2 ne suka shigo daga ƙasar Togo mutum 1 ya hatta, a jihohin Nijeriya kuwa an samu mutane daga jahohi 34 jahohi 2 ne kawai ba su zo ba kenan.

“Sannan mun samu cigaba da aka samu Gidauniyar MacArthur ta ce mu tattara mata ‘yan fim guda 70 a yi masu bita suna san isar da saƙo a garesu a kan harkokin da suke a Nijeriya ka ga wannan ma cigaba ne.”

Ya kuma nuna farin cikin sa da kuma godiyar sa ga Allah da ya bayar da damar da aka gudanar da taron har karo na 5 ba tare da tsayawa ba.

A tsawon kwanakin da aka yi ana gudanar da wannan taro, an ware lokaci na kallon finafinan da su ka shiga wannan gasar inda a ke zuwa Film House da ke Shoprite daga misalin ƙarfe 7 na yamma a kowace rana domin kallon da kuma yin tambayoyi ga masu fim ɗin a kan abin da mutane su ka gani a fim ɗin.

Sannan an shirya yawon buɗe ido ga mahalarta taron, inda aka zagaya da su domin su ga yadda garin Kano ya ke ta fuskar addini, al’adu da kasuwanci.

A daren Asabar 26 ga Nuwanba ne aka yi taron kammala bikin an gabatar da waƙoƙin al’adun Ibo, Yarabawa da Hausawa.

Malam Abdulkareem Muhammad

An raba kyaututtuka ga masu finafinan da su ka yi nasara da kuma mutanen da su ka samar da cigaban masana’antar finafinai ta Afirka.

Shi ma a nasa jawabin, Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, wanda Turakin Bichi Alhaji Ado Bayero ya wakilta, ya yi kira ga jama’a da su koyi ɗabi’ar riƙo da al’adun su da kuma yaren su.

A cewar sa, “A yanzu an kai wani lokaci da yara su na tashi da Turanci; sai ka ga yaro ɗan sakandare, amma ya kasa faɗar wani abu da Hausa.

“Don haka dole sai mun dawo yin amfani da yaren mu ta hanyar koyar da matasa a cikin littattafai da finafinan mu. Don haka ina kira ga wannan taro da ya samar da wani tsari na koyar da matasa yin amfani da al’adu da kuma yaren Hausa.”

An kammala taron lafiya yayin da mahalarta ke fatan wanda za a shirya a shekara mai zuwa ya fi wanda aka yi a bana.