Akwai alaƙa mai kyau tsakanina da gwamnonin da na yi aiki ƙarƙashinsu – Gawuna

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana cewar akwai kyakkyawar dangantaka tsakaninsa da dukkanin gwamnonin da ya yi aiki ƙarƙashinsu a jihar.

Gawuna ya bayyana hakan ne a gidan Talabijin na TVC a cikin shirin “Countdown Nigeria Decides 2023” da aka yi tare da shi.

A cewarsa, “Ina da kyakkyawar alaƙa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da sauran tsofaffin gwamnonin da na yi aiki da su a gwamnatocin baya a matsayin shugaban ƙaramar hukuma, kwamishina da kuma a yanzu a matsayina na Mataimakin Gwamna.”

Ya ƙara da cewa, dangantakar ya kamata a ci gaba da tattalinta duk da bambancin jam’iyyun siyasa.

Kazalika, ya yi nuni da cewa bai yarda a samu gaba ko hatsaniya tsakanin masu ruwa da tsaki a siyasance ba, sai dai a fifita jihar Kano a gaba a kan duk wata maslaha.

Dan takarar gwamnanya buƙaci al’ummar Kano da su yi la’akari da ƙwarewa da nagartar ‘yan takara a matsayin ma’auni a lokacin zaɓe.

“Ina da ƙwarewar da ake buƙata a harkokin mulki wanda ya sanya ni a sama da sauran masu neman takarar gwamna,” in ji shi.

Daga nan Gawuna ya nanata ƙudurinsa na bayar da ‘yancin cin gashin kai ga ƙananan hukumomin jihar idan aka zaɓe shi a matsayin Gwamna.